ME YA FARU A KARBALA 17(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Husaini Ya Kama Hanyar Kufa
Safiyar 8 ga watan dhul hajji a
shekara ta 61H ita ce ranar
Tarwiya; ranar da alhazai suka
kama hanyar zuwa Minna don fara
aikin hajji. Ita ce kuma ranar da
kaddarar Allah ta fitar da sayyidina
Husaini daga garin tare da
iyalansa zuwa ga darajar da
madaukakin sarki ya ajiye masu ta
samun shahada a Karbala. Al-
Bidayah Wan Nihaya na Ibnu
Kathir (8/171).
Abdullahi dan Umar (R.A) wanda a
da suka dauki matsayi iri daya da
Husaini (R.A) kafin nadin Yazid a
yanzu sai da ya bi abokinsa
Husaini har tsawon tafiyar kwana
biyu yana kokarin shawo kansa,
yana ce ma sa “ka tuna rashin
kirkin mutanen Iraqi da rashin cika
alkawarinsu. Wace irin wahala ce
mahaifinka bai sha a hannunsu
ba? Kuma wace irin tozartawar ce
ba su yi ma yayanka Al-Hasan
ba?”. Daga karshe Husaini ya
dauko tulin takardunsu ya nuna ma
sa. Da Ibnu Umar ya hakikance ba
zai iya shawo kansa ba sai ya
rungume shi yana bankwana da
shi kuma ya fadi wata kalma mai
ban tausayi wadda ke nuna ya
hakikance Husaini ba zai kai labari
ba. Yana mai zubar da hawaye ya
ce ma sa:
ﺃﺳﺘﻮﺩﻋﻚ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﻗﺘﻴﻞ!
“Ina ba da ajiyarka ga Allah ya kai
wanda wanda za a kashe!”.
Martanin da sayyadi Husaini yake
maida ma duk masu bashi
shawara shi ne “Allah ya saka
maka da alheri. Na fahimci duk
abinda kake nufi na shawara da
nasiha. Ina gode maka a kan haka.
Abinda Allah ya nufa kuwa shi zai
faru ko na yi aiki da shawararka ko
ban yi ba”.
Idan mutum ya kwatanta matsayin
Husaini da na dan uwansa Al-
Hasan dole ne ya sha mamaki.
Al-Hasan dai nadadden sarki ne da
yan Shi’ar mahaifinsa suka taru
suka nada shi bayan cikawar
mahaifin nasa. Akalla yana tare da
runduna mai yawan sojoji sun kai
100,000. In da ya so sai ayi
shekaru ana yaki da Muawiya da
jama’arsa. Amma sai ya fifita
zaman lafiya a kan zubar da
jinainan musulmi. Don haka ya
nemi Muawiya da kansa suka
sasanta, ya dauki ragamar
al’umma ya rataya ma sa, ya kuma
sa duk jama’arsa suka yi ma sa
mubaya’a. Da haka sai al’umma ta
samu kwanciyar hankali akalla na
tsawon shekaru 20 da Muawiya ya
yi a kan karagar sarauta. Amma shi
Husaini saboda hukuncin Allah bai
kalli irin abinda wansa ya kalla ba
da aka zo wannan lokaci. Domin
ya fito zuwa Kufa ba shi tare da
kowa sai iyalansa. Wadanda kuma
ya dogara ga gudunmawarsu ba
masu fidda kitse wuta ne ba.
Mutane ne da aka san su da
munafurci da yaudara. Ga su kuma
da tsoro da kwadayin abin duniya.
A cikin hudubobin sayyadi Ali (R.A)
da ke cikin Nahjul Balaga ya sha
fitowa fili ya zarge su da haka.
Haka ma a littafan Shi’a da dama
an zargi mutandn Kufa da haka.
Duba alal misali Mausuat Ashura
na Jawad al-Muhaddithi da kuma
Fi Rihabi Ashura na Husain al-
Kourani.
A wurin Ahlus Sunna Hasan da
Husain (shugabannin matasan
aljanna) sun yi ijtihadi ne. Kuma la
budda dayansu ya yi daidai, daya
kuma ya yi kuskure. Amma yan
Shi’a sun ce dukan su ma’asumai
ne da ba su tuntube.
To, ko me zasu ce a kan wannan?

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “ME YA FARU A KARBALA 17(Dr. Mansur Sokoto)”
  1. jamilu Avatar
    jamilu

    Waresr r
    Sent from my BlackBerry wireless device from MTN

Leave a Reply

Categories
Latest updates