Kisan sayyidina Husaini ya yi kama
da kisan sayyidina Zubair bin Al
Awwam dan gwaggon Manzon
Allah Safiyyah bint Abdil Muttalib
(R.A) wanda ya kasance tare da su
Nana Aisha a cikin yakin basasar
rakumi. Yakin da makasan
sayyidina Usman; wadanda suka yi
masa juyin mulki suka hasa
wutarsa tsakanin sarkin musulmi
Ali da talakawansa da suka fito don
daukar fansar jinin Usman. Yaki ya
koma ba-ji-ba-gani a tsakanin ‘yan
uwa – Su Zubairu, Dalha da Aisha
a daya bangare, da kuma Ali,
Ammar bin Yasir da sauransu a
bangare daya. Da Ibnu Jarmuz ya
kashe Zubair sai ya zo yana murna
da bushara ga sayyidina Ali. Sai Ali
Radiyallahu Anhu ya nuna
damuwa kuma ya ce masa:
Tabbas na ji Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam yana cewa: “Ka yi
bushara ga wanda zai kashe dan
Safiyyah da shiga wuta”. Duba
BIHARUL ANWAR (32/336).
Babu shakka tambaya ta farko da
mutum zai yi bayan jin tarihin
abinda ya faru a Karbala shi ne
don me Yazid bai yi wa Ubaidullahi
hukunci ba?. Alal akalla ai ya
kamata ya cire shi daga gwamna.
Haka ne kam. Amma dai wannan
mas’ala ce ta siyasa. Ai ka ga ko
sayyidina Ali ba wani hukuncin da
ya yi wa Ibnu Jarmuz wanda ya
kashe Zubair duk kuwa da karanta
ma sa wannan hadisi da ya yi. Ibnu
Jarmuz ya ci gaba da zama cikin
rundunar sayyidina Ali sannan
daga bisani ya shiga cikin
wadanda suka yi ma sa tawaye har
suka yi yunkurin kashe shi, kai ma
suka kashe shi din (ina nufin
Khawarij). Dalilin kasancewar
lamarin na siyasa shi ne, duban
yanayin Kufa ita kanta da yake
babu salihin mutum da ke iya zama
gwamna a cikin ta. Duk wanda aka
tura ma su a matsayin gwamna
nan take za su kawo karar sa suna
neman a dauke ma su shi.
Sahabbai da dama suka yi wa
tuhumce-tuhumce iri iri har da
wanda suka ce wai bai iya sallah
ba, alhalin kuwa Manzon Allah
(SAWW) da kansa ya taba nada
shi a matsayin gwamna! Don haka,
a zamanin daular Bani Umayyah
zaka ga duk wani fasiki maras
imani – irin su Hajjaj da shi
Ubaidullahi bn Ziyad – gwamnatin
na bukatar su don irin su kadai ne
ke iyawa da Kufa. Na tattauna
wannan matsala a mukalar da aka
buga a fitowa ta 3 ta mujallar
Degel, June 2000 (FAIS, Usmanu
Danfodiyo University, Sokoto) mai
taken “The Umayyad Dynasty
Between Facts and Fiction: A
Study of the Genesis of the
Dynasty and Critical Analysis of it’s
Historical Sources”.
Manzon Allah (S) dai ya yi gaskiya
da ya ce, “Za ayi fitinu, wanda ya
zauna ya fi wanda ya tashi tsaye a
cikin su. Wanda ya tsaya ya fi
wanda ya yi tafiya a cikin su.
Wanda ya yi tafiya ya fi wanda ya
yi gudu a cikin su”. Sahih al-
Bukhari, kitab al-Fitan
Wa ya san iyakar tashin hankalin
da aka yi a kan neman sai sarkin
musulmi Ali (R.A) ya hukunta
makasan sarki Usmanu dan
Affana? Amma shi kuma a
matsayinsa na mai mulki ya san
abinda ya sani, ya kuma ga abinda
ya gani wanda talaka bai gani ba
kuma bai sani ba. Ba wai don ya
amince ko ya yarda da kisan gila
da aka yi wa sarkin da ya gabace
shi ba. Don haka irin wadannan
fitinu ake kamewa daga yin
hukunci a cikin su. Alkiyama na
nan tafe ba fashi. Kuma Allah ba
azzalumi ne ga bayi ba.
Leave a Reply