ME YA FARU A KARBALA 26(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Husaini (Radhiyallahu Anhu) ba
shi kadai Allah ya azurta da
shahada ba a Karbala. Akwai da
dama daga cikin ‘yan uwansa da
ya fito da su wadanda suka hada
da kannensa Ja’afar da Abbas da
Muhammad da Abubakar da Umar
da Usman dukkansu ‘ya’yan
sayyidina Ali. Akwai kuma ‘ya’yan
wansa Al-Hasan: Abdullahi da
Qasim da Abubakar. Sai ‘ya’yansa
shi kansa Husaini: Ali babba da
Abdullahi. Karamin dansa kam Ali
Zainul Abidin – Wanda ake ma
lakabi da Abubakar – bai samu
wannan daraja da danginsa suka
samu ba, saboda ba shi da lafiya a
wannan rana, don haka bai yi yaki
ba, su kuma arnan ba su taba shi
ba. Mun bada cikakken tarihinsa a
cikin littafin MAI RABON GANIN
BADI: ALI ZAINUL ABIDIN, wanda
aka buga a shekarar 2004 a kasar
Saudiyyah.
Daga cikin wadanda Allah ya
karrama da shahada a tare da
Husaini har wayau akwai ‘ya’yan
baffansa Akilu. Su ne, Ja’far da
Abdullahi da Abdurrahman. Sai
kuma Muhammad bin Muslim
wanda aka kashe mahaifinsa tun
kafin isowar Husaini. Daga cikin
‘ya’yan Abdullahi bin Ja’far kuwa
akwai Aunu da Abdullahi. In ka
hada da Husaini mutane 18 kenan
dukansu ‘yan gidan Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam. Wannan kuma shi ya sa
musibar ta kara tsananta a kan
musulmi.
Kafin mu yi maganar abinda ya
biyo bayan wannan fitina da kuma
sharhi a kan matsayinmu game da
Yazidu da hukuncin la’antarsa zan
so in yi tambaya a nan: Ko me ya
sa su ‘yan Shi’ah suke maganar
Husaini, suna makokinsa shi kadai,
ba sa ko nuni zuwa ga sunayen
sauran abokan shahadarsa? Ko ba
sa son mu san akwai masu
sunayen Abubakar da Umar da
Usman ne a cikin ‘ya’yan sayyidina
Ali da yan uwansa?!

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates