Har yanzu dai a kan Yazid
Mun riga mun fadi cewa, akwai
rikici mai yawa a tsakanin
mawallafa game da sha’anin
Yazidu har mun soma bada wasu
‘yan misalai a kan haka.
Daga cikin abin da ke nuna haka
zamu ga zancen wasiyyar da
Mu’awiyah ya yi masa, malam
Dinawari da Ibnu Abdi Rabbihi duk
sun ruwaito ta. Amma Dinawari
cewa ya yi Mu’awiyah ya yi masa
wannan wasici ne baka da baka,
amma shi Ibnu Abdi Rabbihi sai ya
ce Mu’awiyah ya rubuta ta ne a
yayin da Yazidu yake can yana
farauta da wasanni kuma bai dawo
ba sai bayan mutuwar uban nasa.
Duba Al Iqdul Farid na Ibnu Abdi
Rabbihi (4/372) da kuma Al
Akhbarut Tiwal na Dinawari, shafi
na 225.
To, wace ruwaya ce ta gaskiya a
cikin wadannan?
Game da zancen kashe HUSAINI
ma riwayoyin mutanen Kufa (Iraq)
sun karkata ga zargin Yazidu, kai
sun ma hakikance da cewa shi ya
bada umurnin a yi wannan danyen
aiki. Wasu riwayoyin kuma cewa
suke ya barrantar da kansa har da
rantsuwa cewa bai ce a kashe shi
ba, ya dai ce a dakatar da shi ne
daga yunkurinsa na juyin mulki.
Haka ma game da iyalan Husaini
bayan an kashe shi, an ce ya
wulakanta su, an kuma ce ya
girmama su. Akwai ma riwayoyin
Abu mikhnaf da ire-irensa masu
cewa ya dauki karen gamba ya
rinka sokawa a cikin hancin
Husaini lokacin da aka zo masa da
kansa. Yana wulakanta shi yana
Jin dadi. Alhali akwai riwayoyi da
suka ce kuka ya rinka yi har da
la’antar gwamnan Kufa, yana cewa
bai mutunta Manzon Allah ba ga
iyalansa. Zancen an zo da kansa
birnin Sham wurin Yazidu shi ma
masana da dama sun yi suka a
kan sa. Kuma duk wadannan
akwai su a littafan tarihi irin na su
Tabari da Ibnu Sa’ad da
makamantansu. Zamu dawo ga
wannan maganar idan mun zo
zancen Karbala.
Leave a Reply