Mai Rubutu: Hamza Diso
Imamu Ahmad da Muslim da Tirmizi da ibn Majah da wasunsu sun ruwaito hadisi da isnadan su zuwa Abu hurairah zuwa Annabi Salatin Allah da Amincin sa Su tabbata gare shi yace:
Duniya kurkukun mumini ce Aljannar kafiri”
Wannan hadisi yana da Shahidi a Hadisin Abdullahi bn Amr a musnad na imamu Ahmad da musannaf na ibn Abi shaibah da wasunsu, haka kuma yana da Shahidi a Hadisin Salman a wajen dabarani cikin Alkabeer da wanin sa.
Wannan hadisi kwata-kwata baya nuni kan cewar Arna sune zasu sami duniya banda muminai, kamar yadda wasu suke zaton hadisin! Shi wannan hadisi yana nuni ne akan abu biyu
Na farko: mumini da yake rayuwa bisa bin doran Shari’a dole ne sai ya hakura da wasu abubuwan da ransa yake so don Kawai yayiwa Shari’a biyayya, ta haka ne sai ya zamo kamar Dan kurkukun dayake kulle, idan ka koma ruwayar hadisin Abdullah bn Amr zaka ga karshen hadisin yace: idan mutum ya mutu sai a sake shi yayi yadda yake so” wannan fassarar daga sahabin take kamar yadda ibnu Abi hatim ya ruwaito daga babansa acikin littafin ilal cewa wannan riwaya maganar sahabin ce.
Abu na biyu: komai dadin da mumini zaiji a duniya idan aka kwatanta da abun zai samu a lahira to kamar a kurkukun yake, kamar yadda komai wahalar da Arne zai Sha a duniya idan aka kwatanta da abinda yake jiransa to kamar a Aljanna yake.
A takaice wannan hadisi baya nuni kan cewar duniya fa ta arnace
Leave a Reply