Danna nan domin shiga karatu Online
‘Yan’uwa Musulmi! Barkanmu da war haka, bayan haka, babban malamin Musulunci Alhafiz Ibnu Rajab wanda ya mutu a shekarar hijira ta 795 watau yau shekaru 640 ke nan da suka wuce, ya yi wa malamai wata maga da ya kamata a rubuta ta da ruwan zinari, ya ce cikin littafinsa mai suna Alhikamul Jadiiratu Bil…
·
KO HALACCIN SHIRYA MUSABAKA A KAN HADDAR ALQUR’ANI, KO HADDAR HADITHI, KO HADDAR WANI ILMI NA MUSULUNCI, ZAI WAJABTA HALACCIN RIKON RANAR HAIHUWAR ANNABI MAI TSIRA DA AMINCIN ALLAH A MATSAYIN WANI IDI??? LARABA 7/3/1435 H 8/1/2014 M Yana daga cikin misalan da za mu bayar na son zuciyar wadanda suka zaba wa kansu sabanin…
·
Wani dan’uwa ya tambaye mu cewa: Ko mene ne aqiidar marigayi Sheik Abdulaziz Bin Baz shugaban majalisar malamai ta Saudiyya game da Ruqyah da kuma yiwuwar a yi magana da aljani ta harshen mutum? Mutumin ya ce ya yi wannan tambayar ce saboda ya ji wasu malaman na cewa hakan kfirci ne kuma bokanci ne!…
·
Musulmi Sun Ci Gaba Da Fuskantar Wulakanci Jarrabawa sunnar Allah ce da take tare da ma’abuta gaskiya a duk inda suka kasance. Da ita ne Allah yake rarrabe masu addini da gaskiya da munafukai masu yin sa kawai don holewa da jin dadi. Haka kuma babbar makaranta ce da take horar da mazaje a kan…
·
Ci Gaban Yaduwar Musulunci 3. Musuluntar Dhimad Al-Azdi Dhimad dan kasar Yemen ne, daga fitacciyar kabilar nan ta Azd-Shanu’a masu dogon tarihi. Mutum ne da Allah ya yi ma sa baiwa ta yin rukiyya ga masu fama da kamun iskoka. A lokacin da ya ji wawayen Makka suna tadin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam suna…
·
Musulunci Ya Ci Gaba Da Yaduwa 2.Musuluntar Amru bn Abasata. Wannan shi kuma wani bawan Allah ne da ya kasance yana kyamar ayyukan jahiliyyah. Don haka da ya ji ana zagin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa ya bar tafarkin da aka sani sai ya niko gari ya nufato Makka. Ko da ya zo ana…
·
Musulunci Ya Ci Gaba Da Yaduwa A Sauran Sassa Kafin mu koma kan irin azabar da musulmi suka dandana a hannun mushrikai, za mu yi tsokaci game da yaduwar musulunci a wannan zamani da muke magana a kan sa zuwa sauran sassan yankunan larabawa. Duk da irin muzgunawar da manzon rahama Sallallahu Alaihi Wasallam yake…
·
Wasu Daga Cikin Yan Kungiyar Masu “Izgili” A can baya mun ga irin matakan da arna suka dauka don dakile addinin musulunci amma ba su ci nasara ba. Don haka sai suka koma ga cin zarafi da amfani da karfin tuwo. Mun ga kuma matsayin da Abu Lahabi ya dauka na bayyananniyar adawa shi da…
·
Matakan Fada Da Musulunci A lokacin da Quraishawa suka lura da ci gaban musulunci da yaduwarsa sun bi dukkan hanyoyin da suke iyawa don ganin sun dakushe shi. Daga cikin matakan da suka dauka har da: 1. Kokarin rage ma sa karfin tsaro. Babu wani mutum da Allah ya taimaki manzonsa da shi a wannan…
·
An Fara Kai Ruwa Rana Tsakanin Musulunci Da Kafirci Fara bayyana da’awar musulunci ke da wuya sai duk inda hankalin shugabannin Quraishawa yake ya tashi, suka kalli musulunci a matsayin wani gungu na ‘yan tawaye da ya zo ya tarwatsa tarayyar kasarsu, ya wautar da hankalinsu da na iyayensu, a yayin da zukata masu tsarki…
·
Da’awar Musulunci Ta Fara Fitowa Fili Shekaru uku kenan cif aka yi ana sirranta da’awar musulunci tare da kiran daidaiku wadanda ake ganin dacewar su da shiga musulunci a irin wannan lokaci mai tsanani. Kuma sama da mutane 40 ne suka samu horarwa ta musamman daga manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam wadanda suka hada da…
·
Ayari Na Biyu A hankali ayarin farko suka ci gaba da janyo mutane asirce suna kawo su wurin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana yi masu sharhin da’awarsa suna ba da gaskiya da shi. Babu kamar Abubakar a wannan fage, kasancewar sa babban mutum mai matsayi wanda jama’a ke taruwa a gidansa kuma wanda ya…
·
Wahayi Ya Tsinke, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Shiga Damuwa Tun daga wancan lokacin da muka fada a baya Jibrilu (AS) sai ya daga kafa bai sake ziyartar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ba. Har sai da manzo ya shiga cikin shaukin dawowar wannan bakon arziki. Sai bayan da watan Ramadhan ya shude ne…
·
Da sunan Allah za mu shiga: FASALI NA UKU Tarihin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Daga Annabta Zuwa Hijira Gari ya waye Kafin cikar shekarun manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam arba’in halin da duniya take ciki ya kara rikicewa. Jahilci ya yi kanta a cikin mutane domin sun dimauta daga bin mahaliccinsu. Amma shi kam…
·
ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 39 Daga Cikin Fifikonsa 5. Daukakar Al’ummarsa (kashi na biyu) Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yakan nuna damuwa a kan abubuwan da Allah ya kaddara faruwarsu na fitinu da za a jarabci al’ummarsa da…
·
ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 37 Daga Cikin Fifikonsa 4. Darajar Sahabbansa (kashi na uku) Wasu Darajoji da Allah ya Kebanci Wasu Daga Cikin Daidaikunsu Da Su: 1. Akwai wanda mala’ika Jibril (AS) yake saukowa a cikin siffarsa. Shi…
·
Ina Kadiradawa? Ga sako na musamman zuwa gare ku: قال سيدي أبو صالح عبد القادر بن موسى بن عبد الله بن يحيى الزاهد بن محمد بن داود بن موسى الجون بن عبد الله المحضى بن الحسن المثنى بن الحسن بن علي بن أبي طالب رضي الله تعالى عنهم أجمعين في كتابه “الغنية لطالبي طريق الحق”:…
·
A yau jum’ah 24/2/1435H na’ibi na 2 Sheikh Idris Garba ne ya jagoranci sallah a wannan masallaci bayan yayi huduba wadda ya mayar da karfi a cikinta wajen bayanin himmar sahabban manzon Allah (S) wajen kula da alkurani ta fuskar karatunsa da koyar da shi da zakulo asirrai da ilmummukan da ke cikin sa. Manzon…
·
Da yawan Mutane na zaton cewa; Kira zuwa ga Musulunci da Nusar da Musulmai kan Turbar Annabi, aiki ne da ya takaita ko ya rataya kan Manyan Malamai da Kuma Ustazai da wadanda ke da Ruwa da Tsaki cikin harkar Addini. Aikin fadada Musulunci da Gyarawa Mutane zama a cikinsa, Nauyi ne da ya rataya…
·
~CHOLESTEROL ~ Wani sinadari ne na ciwo da ake samun sa a cikin Jini idan yayi yawa , yana sabbaba cututtuka kamar haka:- 1- Cututtukan Zuciya 2- Hawan Jini 3- Ciwon suga 4- Paralyse ,( Mutuwar Bangaren jiki). 5- Obesity , (Nauyi ya mai wuce Kaida) . @ Me yake kawo Yawan Cholesterol ? @-…
·