Qa’idah: Asali acikin Ibada shine kamewa har sai ansamu dalili da yace ayi

Danna nan domin shiga karatu Online

Dalilin turo Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da sauran Annabawa shine: su kira mutane zuwa ga bautar Allah, su koya musu yadda zasu bauta wa Allah maɗaukakin sarki. Shiyasa dole akan duk wanda yake son tsira yabi abinda wa’innan manzannin sukazo dashi, domin wahayi ne daga Allah madaukakin sarki.

Shiyasa idan Mutum zai shiga Musulunci sai ya furta kalmar Shahada “Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, Annabi Muhammad Manzon Allah ne

Wanda baiyi Imani da wannan kalma ko baiyi aiki da ita ba baya zama cikakken Musulmi.

Abinda wannan kalma take nuni a taƙaice shine Mutum bazai bauta wa kowa ba sai Allah shi kaɗai, Haka nan Bazai bauta wa Allah da koyarwar kowa ba sai koyarwar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, domin Shine Allah ya turo shi zuwa garemu domin ya koyar damu addini.

Ashe kenan duk wani bauta da bai samo asali daga Annabi ba ya zamto shirme, kuma Wanda ya aikata ya aikata laifi.

Anan ne aka samo wannan Ka’ida “Asali acikin Bauta shine kamewa“.

ma’ana baya halatta ga mutum ya faro wani abu na ibadah a karan kanshi har sai ya samo asali daga Annabi. Tsaɓanin lamura na duniya wanda ya halatta ga Mutum ya ƙirƙiro duk abinda yaga dama wacce zata amfane shi ko ta amfani mutane matuƙar babu wani nassi a shari’ah da ya hana hakan. Kamar yacce aka ƙirƙiro wayar salula, komputa, jirgin sama da makamantansu. Duka wa’innan ba’a buƙatar ayah ko hadisi kafin ayi su, domin ba ibada bane. Lamuran mu ne na duniya. Kuma mu muakfi sani game da lamuran Duniyarmu kamar yadda Annabi ya faɗa.

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

Duk wanda ya ƙirƙiro wani abu acikin wannan lamari namu wanda baya cikinsa to an mayar masa

Bukhari: 2697. Muslim: 1718

Wannan Hadisi Ƙarara yake nunawa cewa Allah baya karɓan wani aiki na bauta wanda babu umarnin sa akai

Wasu mutane sukan ce Ai abinda Annabi ya hana shine laifi amma abinda bai hana ba babu laifi a aikata, kaga wannan batu nasu yaci karo da nassin wannan hadisin.

idan suka aikata wani aiki wanda basu da dalili akai, ka tambayesu meye dalilinku na aikata wannan aiki sai suce maka a ina ne aka Hana a aikata?

kaga Anan in ka fahimci wannan Qa’ida zaka yi musu bayani cewa ai asalin Ibada ba’a yinsa sai ansamo hujja.

sukan ce: toh Annabi ya hau mota? Ya riƙe wayan hanu? Da sauransu. Ai shima wannan Bid’ah ne.

To sai kace musu ai wannan lamuran duniya ne ba abinda ya shafi addini bane, sabida haka ya halatta muyi koda Annabi baiyi ba.

A abinda ya shafi lamuran duniya ne za’a ce ina ne Annabi ya hana. Amma abinda ya shafi harkar Addini za’a ce a ina ne annabi yayi umarni?

Idan har aka buɗe ƙofar kowa ya ƙirƙiri abinda yaga dama to haƙiƙa wannan addini zai gurɓace kuma hakan zai kawo rarrabuwan kan al’ummah. Domin kowani sarkin gari zai iya ƙirƙiran nashi irin ibadar idan Aka tambaye shi dalili sai yace inane Annabi ya hana. Hakanan kowani mutum ma zai iya yi a karan kansa.

Da fatan Angane. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates