Ramadaniyyat: 1444 [1] – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga karatu Online

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibn Taimiyya, Malami Na Allah (1)

  1. A wani lokaci a cikin shekarar hijira ta 668, duk wani matafiyi daga garin Harran zuwa Dimashƙa na ƙasar Suriya (Syria), zai iya cin karo da wani magidanci tare da iyalansa tafe a kan wannan hanyar, domin tsira da rayuwarsu daga wani mummunan hari da ‘yan ta’addar Tatar suka kai wa garinsu Harran, inda kuma yi ta’adi mai yawa na dukiya da rayukan jama’a. Wannan magidanci tare da iyalansa, sun kama hanyarsu ta zuwa garin Dimashƙa suna jayen da amalanke mai dauke da wasu ‘yan kayayyakinsu da ba su taka kara sun karya ba. Tare da su kuma akwai wani ɗan karamin yaro da bai wuce shekara bakwai a duniya ba, amma kuma mai matuƙar kwazo da basira da hankali irin na manyan mutane. Wannan yaro ya buɗe ido ya ga irin ta’addanci ‘yan Tatar suka tabka, sai wannan ya ƙara masa laƙantar gwagwarmaya da fadi-tashin rayuwa, domin a gaban idonsa ya ga yadda suka tarwatsa komai a garinsu, suka tilasta wa iyayensa fita gudun hijra da barin gidajen zamansu karfi da yaji. Wannan yaro shi ne: Abu Al-Abbas Taƙiyyuddin Ahmad ɗan Abdul-Halim ɗan Abdus-Salam ɗan Abdullahi ɗan Khudhairu ɗan Muhammad, wanda aka fi sanin ‘yan danginsa da suna: Iyalan ɗan Taimiyya.
  2. An haifi Ibn Taimiyya ranar goma ga watan rabi’ul Auwal, a shekarar 661 bayan hijira. Wasu masana ma suna cewa, an haife shi ne ranar 12 ga Rabi’ul Auwal.
  3. An yi saɓanin wajen tantance cewa shi Balarabe ne ko Bakurde ne, wato dan ƙabilar Kurdawa, to amma wannan ba wani abu ne mai muhimmanci babba ba, domin abin alfahari a wajen Ibn Taimiyya shi ne kyawawan ayyukansa da gwagwarmayar raya sunnar Manzon Allah (SAW) wanda ya kai shi ga mutuwa a cikin gidan kaso.
  4. Tarihi bai ba mu wani labari game da mahaifin Ibn Taimiyya ba, domin kuwa ya rasu a shekara ta 682 lokacin da Ibn Taimiyya yana matashi sosai bai wuce shekara ashirin da ɗaya ba. Amma mahaifiyarsa ta rayu har ta ga lokacin da ɗanta ya zama wani jan-gwarzo mai yaƙin ba wa sunnar Annabi (SAW) kariya da faɗa da bid’o’i da miyagun al’adu. Mahaifiyarsa ta ba shi gudunmawa da ƙarfin gwiwa a fafutukarsa da jihadinsa. Yayin da yake tsakiyar gwagwarmaya a fagen daga a ƙasar Masar, bayan kuma an kulle shi a gidan kaso, ya riƙa aika mata da wasiƙu masu cike da kalmomin nuna biyayya da girmamawa da kyautatawa, ya kuma riƙa ɓoye mata matsalolinsa da halin da ya tsinci kansa a ciki, domin kada ya jefa mata raɗaɗin rabuwa da shi.
    Za mu ci gaba insha Allah…….
Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates