Ramadaniyyat: 1444 (16) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (16)

Ci gaba…..

Ibnu Taimiyya Ya Sake Dawowa Al-Ƙahira:

  1. Ibnu Taimiyya ya sake dawo wa Al-Ƙahira cikin mutunci da karramawa, bayan Sarki Nasir ya koma kan karagar mulkinsa. Sarki shi ne ya nemi Ibnu Taimiyya da ya sake dawo wa ƙasar Masar. Ya iso Al-Ƙahira a ranar takwas ga watan Shawwul na shekarar 709. Ya koma kan karantarwarsa gadan-gadan. Waɗanda kuma suka yi sa’ayin cutar da shi suka zo suna neman yafiyarsa, a nan ne ya faɗi cewa: “Duk wani wanda ya cutar da ni a baya, to ni ta ɓangarena na yafe masa”.
  2. A nan kuma ya dace mu ambaci wani hali na dattako da Ibnu Taimiyya ya nuna bayan da Sarki Nasir ya dawo kan kujerar mulkinsa, ya so ya yi ramuwar gayya a kan malamai da alƙalai waɗanda suka ci amanarsa, suka koma goyon bayan abokin hamayyarsa, watau Al-Jashankhir, suka nuna masa wala’I da ƙauna. Kuma su dai waɗannan malaman su ne waɗanda suka riƙa yanke wa Ibnu Taimiyya hukunci ɗauri a jararrabawarsa ta farko, a inda ya yi zaman kurukuku na tsawon wata goma sha takwas a sanadiyyarsu. Don haka sai Sarki Nasir ya yi fatawa a wajen Ibnu Taimiyya cewa, wane hukunci ya kamata ya yi musu game da cin amanarsa da suka yi? Sai Ibnu Taimiyya ya buɗi baki ya ce masa: “Jininsu ya haramta a kanka. Haramun ne ka cutar da su”. Sai Sarki ya ce: “Mutanen nan fa sun cutar da kai, sun yi ƙoƙarin kashe ka a lokuta da dama”. Sai Ibnu Taimiyya ya amsa masa da cewa: “Duk wanda ya cuce ni, to ni na yafe masa. Wanda kuwa ya cutar da Allah da Manzonsa, to Allah ne zai ɗau fansa a kansa, ni ba zan ɗau fansa domin kaina ba”. Ibnu Taimiyya bai tsaya iya nan ba, sai da ya nema musu afuwa a wajen Sarki Nasir, ya riƙa lallashin sa yana ce masa: “Idan ka kashe waɗannan (malamai), to fa ba za ka ƙara samun malamai kamarsu ba.” Haka ya yi ta famar lallashin Sarki har ya shawo kansa ya yafe musu. Allahu Akbar ka ji zuciyar manya, masu tsoron Allah da neman yardarsa.
  3. Ibnu Taimiyya ya yi irin wannan karamci da halin dattako ga waɗannan malamai abokan hamayyarsa, daga cikinsu har da Ibnu Makhlufa, alƙalin da ya fi kowa tsangwamar Ibnu Taimiyya; shi ne wanda ƙememe ya hana shi kare kansa lokacin da ake masa tuhumce-tuhumcen ƙarya, daga ƙarshe ya jefa shi cikin kurkuku ba tare da an yi masa shari’a ba. Wannan matsaya ta Ibnu Taimiyya ta sa dole Ibnu Makhluf ya fito bainar jama’a ya yaba wa Ibnu Taimiyya, har yana cewa: “Ba mu taɓa ganin mutum irin Ibnu Taimiyya ba, mun yi ta zuga a kansa amma ba mu samu ikon galaba a kansa ba, sai ga shi ya samu iko a kanmu amma ya yafe mana, ya kuma riƙa ba mu kariya da hujja”.

Za mu ci gaba insha Allah….

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates