Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (20)
Ci gaba…..
- Ibnu Taimiyya ya ajiye ta’assubancin Mazhaba gefe guda, ya rungumi bincike da nazari mai zurfi a cikin littafin Allah, Alƙur’ani, da sunnar Manzon Allah (SAW), da kuma maganganun magabata na ƙwarai. Shehun Malamin ya kai matakin ‘Mujtahid Muɗlaƙ’, watau cikakken mujtahidi wanda ya tsayu da ƙafafunsa, ba ya buƙatar dole sai ya jingina da wata mazhaba idan zai yi fatawa. Wannan matsayin da ya kai a ilimi shi ne ya ba shi dama har ya saɓa wa ra’ayoyin limaman Mazhabobin nan huɗu a wasu mas’aloli masu girma sosai:
a) Mas’alar Rantsuwar Saki: Ibnu Taimiyya ya lura da cewa, Kalmar ‘saki’ ta zama kalmar da wasu suke rantsuwa da ita, watau sai ka ji mutum ya ce, ‘idan bai yi abu kaza ba, to matarsa ta saku’. Sai dai kamar yadda aka sani, idan mutum ya yi rantsuwa da Allah, sannan ya karya rantsuwarsa, to zai yi kaffara ne: ko ya ‘yanta bawa, ko ya ciyar da miskinai goma ko ya tufatar da su; ko kuma idan ya gagara aikata ɗaya daga cikin abubuwa uku na, to sai ya yi azumin kwana uku. Amma idan rantsuwar saki ya yi, sannan ya karya rantsuwarsa, to ba ya da hanyar kuɓuta sai dole ya rabu da matarsa, gidansa ya rushe, alaƙar aurensu kuma ta lalace. Sai Ibnu Taimiyya ya ga wannan al’amari ya yi tsauri sosai kuma ya munana. Sai ya shiga binciken tushen mas’alar daga Litttafin Allah da sunnar Manzon Allah (SAW) da maganganun magabata, da ya ga bai sami wata magana da take tabbatar da aukuwar saki ba, sai ya gane babu wani ƙaƙƙarfan dalili da yake nuna aukuwar saki ta hanyar irin wannan rantsuwar. Musamman idan an yi la’akari cewa shi mai wannan rantsuwa tun farko ba niyyarsa ba ce aukar da saki. Don haka sai Ibnu Taimiyya ya yi fatawar saki bai auku ba. Ya kuma ƙarfafi ra’ayinsa da maganganun wasu magabata na ƙwarai. Wannan fatawar ita ce ta zama sanadiyyar dakatar da shi daga yin fatawa a shekara ta 718.
b) Yana daga cikin mas’alolin da ya saɓa wa mazhabobi huɗu a cikinsu: Saki uku da kalma ɗaya, watau kamar mutum ya ce wa matarsa: ‘Na sake ki saki uku’. Ko saki uku a zama ɗaya, kamar ya ce: ‘Na sake ki, na sake ki, na sake ki’. To duka mazhababin nan huɗu sun yarda da cewa wannan saki ya tabbata uku gaba ɗaya. Amma Ibnu Taimiyya ya ja a kan haka, domin yana ganin hakan ya saɓa wa nassin Alƙur’ani da ya ce: “Saki sau biyu ne (ɗaya bayan ɗaya)” [Al-Baƙara, aya ta: 229]. Kuma ya kawo hadisai da aikin sahabbai a zamanin Sayyidina Abubukar da shekaru biyu na zamani Sayyidina Umar, kafin shi Sayyidina Umar ya mai da shi a matsayin uku, don ya zama horo a kan masu azarɓaɓi a sha’anin saki.
c) Daga cikin ra’ayoyinsa da ya saɓa wa mazhabobi huɗu: Saki ba ya aukuwa a cikin haila, ya kafa hujja da cewa, Annabi (SAW) ya umarci Abdullahi ɗan Umar da ya dawo da matarsa bayan ya sake ta tana haila. Ya kuma yi hujja da wasu daga cikin maganganun magabata.
- Ibnu Taimiyya ya yi irin waɗannan fatawoyi da wasunsu waɗanda suka saɓa wa ra’ayoyin limaman mazhabobi huɗu, sai wasu daga cikin malamai suka yi masa nasiha suka ja hankalinsa a kan ya yi shiru ya daina yin fatawa. Sai ya karɓi shawararsu ya daina fatawa. Amma daga bisani sai ya dawo ya ci gaba da ba da fatawa. Daga baya kuma sai umarni ya zo daga fadar Sarki cewa an hana shi sake bayar da fatawoyin irin waɗannan, sai dai kuma shi Ibnu Taimiyya ya bijire wa wannan hani, domin ya ɗauki hakan a matsayin ƙasƙanci, shi kuwa ba zai iya jure wa wulaƙanci game da addininsa ba, musamman yana ganin yana tabbaci a kan abubuwan da yake faɗa, ba molonka yake yi ba.
Za mu ci gaba insha Allah….
Leave a Reply