Ramadaniyyat: 1444 (19) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (19)

Ci gaba…..

  1. Abin da za mu yi la’akari da shi a nan, Ibnu Taimiyya a zangon farko na rayuwarsa a ƙasar Sham da Masar ya fi ba da ƙarfi wajen bayani a kan aƙida kamar yadda ta zo a Alƙur’ani da sunna. A ɓangaren ra’ayoyinsa na Fiƙhu kuwa yana dogaro da abin da ya zo a Mazhabar Imamu Ahmad ne, bai cika kauce mata ba sai a cikin wasu ‘yan mas’aloli kaɗan.
  2. Amma a wannan zango na biyu na rayuwarsa a Sham, to ya ba da kulawa ƙwarai a kan batutuwan da suke da alaƙa da Aƙida da kuma mas’aloli na Furu’a. Ya himmatu sosai a kan bincike cikin mas’alolin Fiƙhu da tunani na ɗan salafiyya, a wasu lokuta yakan cimma wata matsaya da ta saɓa wa mazhabobin nan huɗu; ko ta yi daidai mashahurin zance ko wanda ba mashahuri ba a cikinsu. Amma dai a sani cewa, duk abin da ya zaɓa a matsayin ra’ayinsa, to yana gina zaɓinsa ne a kan hujja da dalili daga Alƙur’ani da sunna, waɗanda ya riga yi yi musu cikakken sani. Babu sanda zai lalubi nassi na Alƙur’ani ko hadisi ya rasa, ko ya rasa wani miƙaƙƙen ƙiyasi na Fiƙhu wanda zai ƙara ƙarfafar nassi da shi; ko ya yi hujja da shi idan bai samu nassi ƙarara ba.
  3. Wannan bayani ba yana nuna bai damu da Fiƙhu sai a zangon rayuwarsa na biyu ba ne. A’a Ibnu Taimiyya ya damu da batun Fiƙhu a duk tsayon rayuwarsa, sai dai a nan muna bayanin gwargwadon yawan damuwarsa ne da sha’anin furu’a a wannan zango na biyu na rayuwarsa. A cikinsa ne ya ƙara ci gaba da bincike cikin mas’alolin Furu’a inda ya ƙetare da’irar Mazhabar Hanbaliyya, ya kutsa da nisa cikin dukkan mazhabobi na Musulunci, ya karance su karatu ba na wasa ba.
  4. Duk wannan zuzzurfan bincike da Ibnu Taimiyya yake yi a cikin mazhabobin Musulunci bai nisanta kansa daga Mazhabarsa ta Hanbaliyya ba, yana ɗaukar kansa har yanzu a matsayin ɗaya daga cikin ‘ya’yan wannan Mazhaba, tare kuwa da cewa yana da ra’ayoyinsa da dama waɗanda suka saɓa wa ra’ayin Mazhabarsa. Wannan kuwa ya faru ne saboda shi ya raja’a a kan tsamo hukunce-hukunce daga Alƙur’ni da sunna kai-tsaye ba tare da sai wani ya masa iso ba. Amma duk da wannan, ya ci gaba da girmama Fiƙhun Imamu Ahmad ba tare da ra’ayin riƙau game da shi ba. Yana faɗa game da Mazhabar Imamu Ahmad cewa:
  5. “Imamu Ahmad ya fi wasu da dama sanin Alƙur’ani da sunna da maganganun sahabbai da tabi’ai na ƙwarai. Wannan ne dalilin da ya sa da wuya a sami wata maganarsa da ta saɓa wa nassi kamar yadda ake iya samu a maganganun wasu. Da wuya kuma a samu wata maganarsa mai rauni face a cikin mazhabar tasa an kuma samun wata maganar tasa da ta dace da maganar da ta fi ƙarfi. Yawancin maganganun da ya keɓanta da su tsakanin sauran mazhabobin, maganarsa ta fi rinjaye, kamar alalmisali, yadda yake da ra’ayin cewa, za a iya karɓar shaidar kafiran amana a kan Musulmi idan akwai buƙatar hakan, kamar a halin tafiya da sauransu”. [Al-Majmu’, juz. 20 sh. 229].
  6. Za mu lura a nan, Ibnu Taimiyya yana rinjayar da Fiƙhun Ahmad Ibnu Hanbal ba wai don kawai yana Ibnu Hanbal ba, sai don ƙaƙƙarfar alaƙar da ke tsakanin Fiƙhun Ibnu Hanbal da Alƙur’ani da sunna. A hakan kuma ba yana mai ra’ayin riƙau game da shi ba ne, a’a sau da yawa ma yakan ɗau maganganun wasu malamai ya bar ta Imamu Ahmad. Domin yana kallon ‘Ta’assubanci’ watau ra’ayin riƙau, wani nau’i ne na bin son zuciya ba tare da wata hujja ko dalili ba. Yana cewa:
  7. “Duk wanda yake yi wa wani malami makauniyar biyayya (Ta’assubanci), to ya kwaikwayi halayen ‘yan bid’a. Yana yin haka ne ga Maliku ko Abu Hanifa ko Ahmad. Sannan maƙurar mai ta’assubanci ga ɗaya daga cikin waɗannan, shi ne ya zamanto ya jahilci gwargwadon ilimisa da addinisa, ya kuma jahilci matsayin sauran malamai, to don haka ya tabbata jahili mai zaluntar kansa. Allah kuwa yana umarni ne da ilimi da adalci, yana kuma hani game da jahilci da zalunci. Allah yana cewa: “sai kuwa mutum ya ɗauke ta (amana); lalle shi (mutum) ya kasance mai zaluntar kansa ne, mai jahilci”.
  8. Ka ga Abu Yusuf da Muhammad sun fi kowa koyi da Abu Hanifa da sanin manganunsa, to amma duk da haka sun saɓa masa a wasu mas’aloli da ba za su lissafu ba, yayin da sunna da hujja suka bayyana gare su har suka ga dole ne su saɓa masa, amma tare hakan suna girmama shi”. [Al-Majmu’ juz. 22, sh. 252-253].
  9. Za mu ci gaba insha Allah…..
Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories