Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (26)
Ci gaba…..
Mene ne Ya Canja Sarki Nasir?
- Mai tambaya zai iya tambaya cewa: An san Ibnu Taimiyya a farkon al’amari mutum ne mai faɗa-a-ji a wurin Sarki Nasir, wanda Sarki yake girmama wa matuƙa. To mene ne ya faru, har Sarki ya juya wa Ibnu Taimiyya baya, ya fara da tsare shi na ‘yan kwanaki kaɗan, sannan ya sake tsaurara matakan tsare shi daga ƙarshe?
- Amsar wannan tambayar za mu iya samun ta daga wani labari da Al-Maƙrizi ya bayar, inda ya rubuta cewa: “Sarki Nasir, wata rana, ya fita farauta kamar yadda ya saba. Yana tsaka da tafiya sai ya fara jin wata rashin lafiya mai tsanani kamar ba zai yi rai ba. Sai ya sauko daga kan dokinsa, amma kuma sai ciwon nasa ya ƙara tsananta. Sai nan take ya yi alwashi idan Allah ya ba shi lafiya, zai gina wurin bauta a wannan wurin. Da ya dawo Fadarsa ta kan dutse, bayan ‘yan kwanaki sai ya ji ya sami lafiya. Sai ya hau abin hawansa, shi da kansa ya koma wurin da ya fara rashin lafiya tare da ma’aikata, suka zana wata zawiya da ake kira ‘Khanƙah Saryaƙaus’ a shekara ta 723, ya samar da wurin khalwa na sufi ɗari. A daura da wannan zawiya kuma ya gina wani masallacin juma’a, ya kuma gina wurin wanka da wurin girki a shekara ta 725. [Al-Mawa’iz wal-I’itibar, juz. 4, sh. 294].
- Idan muka fahimci cewa farkon jarrrabawa da Ibnu Taimiyya ya haɗu da ita ta faru ne a shekara ta 726, to za mu fahimci su wane ne suka yi wa Sarki tasiri. Tun daga lokacin da Sarki Nasir ya gina wa sufaye zawiya, sai ya zama abokinsu na jiki, su kuma kowa ya san gabar da ke tsakaninsu da Ibnu Taimiyya. Babban Malaminsu Ibnu Aɗallah As-Sakandari ya daɗe yana tsananta inkari ga Ibnu Taimiyya da kai sukan sa wurin mahukunta.
- Tun da kuwa har Sarki Nasir ya buɗe wa sufiye zuciyarsa, to lalla zai rufe wa Ibnu Taimiyya ƙofa, zai riƙa sauraron sukan Ibnu Taimiyya daga abokan hamayyarsa Sufaye. Ta wannan hanya ce aka fara samun ɓaraka tsakanin mai martaba Sarki da Ibnu Taimiyya, sannan Ibnu Taimiyya ya fara gamuwa da jarrabawa bayan jarrabawa, har aka kai lokcin da aka ƙuntata masa sosai, har zuwa rasuwarsa. Allah ya yarda da shi. Amin.
Za mu ci gaba in sha Allah…
Leave a Reply