Ramadaniyyat: 1444 (5) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga karatu Online

Ramadaniyyat: 1444 (5)

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (5)

Ci gaba…..

Ibnu Taimiyya Ya Gaji Kujerar Babansa:

  1. Karatun Ibnu Taimiyya ya yi nisa sosai a cikin kowane fanni na ilimi; kama daga Alƙur’ani, Hadisi, Aƙida, Fuƙihu, Tafsiri, har zuwa Sira, Tarihi, Arabiyya da sanin ra’ayoyin malaman Falfasa da makamantansu. Bayan rasuwar mahaifinsa shekara ta 682, a lokacin Ibnu Taimiyya yana ɗan shekara ashirin da ɗaya, sai ya gaji kujerar mahaifinsa. Ya fara karantarwa da fatawa a babban masallacin juma’a na birnin Dimashƙa inda mutane suka riƙa tururuwa don zuwa sauraron karatunsa. Suka riƙa mamakin iliminsa da fasahar harhensa wajen sarrafa Larabci. Wasu daga nan suka lizimce shi, suka zama manyan ɗalibansa masu zumuɗin sauraron sa koyaushe. Suka so shi soyayya ta gaskiya daga ƙoƙon zukatansu. Majalisinsa ya kasance majalisi ne da yake tattaro mutane iri-iri masu mabanbanta fahimta da ra’ayoyi daban daban, da mabiya mazahabobi mabanbanta. Kowannensu kuma yana samun gamsasshen bayanin da ya shafi mazahabarsa da ƙungiyarsa.
  2. Idan Ibnu Taimiyya yana karatu ilimi ne kawai yake kwarara daga bakinsa. Wannan ne ya sanya Shehun Malami Ibnu Daƙiƙil Id yake cewa a kansa: “Lokacin da na haɗu da Ibnu Taimiyya na ga wani da aka baje masa ilimi a gaban idanunsa, ya kwashi na kwasa ya bar na bari”.
  3. Bayan ilimi da Allah ya yi wa Ibn Taimiyya baiwa da shi, har ila yau shi mutum ne mai kwarjinin gaske da haiba mai cika ido. Zahabi, almajirinsa ya siffanta shi da cewa: “Shi mutum ne fari mai baƙin gashin kai da na gemu, ba shi da furfura sai ‘yar kaɗan. Idanunsa biyu kuwa kai ka ce harshe biyu ne masu furuci. Tsakatsaki ne ba mai tsawo sosai ba. Yana da faɗin ƙirji, yana da babbar murya, sannan fasihi ne, mai saurin karatu, yakan yi saurin fushi, to amma yana danne fushinsa da yafiya da haƙuri. Mutum ne jarumin gaske, ga shi da yawan kyauta, sannan da kaifin ƙwaƙwalwa. Idan yana addu’a da neman agaji wajen Allah, ni ban taba ga mutum irinsa ba…”.
  4. Karatun wannan matashin malami karatu ne mai cike da hujja da dalilai masu gamsarwa. Duk sa’adda ya koro bayani, to yakan yi linƙaya ne a cikin kogin ayoyin Alƙur’ani da hadisan Annabi (SAW) da kuma maganganun magabata na ƙwarai; wato sahabbai da almajiransu tabi’ai da sauran limaman shiriya. Ba ya ƙyale wata kafar shubuha ko wani ruɗani face ya toshe shi da gamsasshen bayani mai ratsa zuciya, mai kama hankali.

Za mu ci gaba…..

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates