Mafi yawan maluman Shafi’iyyah
suna ganin cewa harabar
masallaci tana cikin masallaci.
Imamun Nawawii ya ce cikin littafin
Raudha’tuttaalib 1/465:-
(( ﻭﺍﻣﺎ ﺭﺣﺒﺔ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻓﻌﺪﻫﺎ ﺍﻻﻛﺜﺮﻭﻥ ﻣﻨﻪ)).
Amma Hanaabilah sun ce abin da
ya fi inganci cikin mazhabarsu shi
ne: Harabar masallaci ba ta daga
cikin masallaci.
Babban Malami Mardaawii ya ce
cikin littafin Al-Insaaf 3/364:-
((ﺭﺣﺒﺔ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻟﻴﺴﺖ ﻣﻨﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ ﻣﻦ
ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ ﻭﺍﻟﺮﻭﺍﻳﺘﻴﻦ)).
To amma ya zo kamar haka cikin
littafin Fataawal Lajnatid
Daa’imah31/234:-
(( ﺱ: ﻫﻞ ﻣﻜﺘﺒﺔ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﺗﻌﺘﺒﺮ ﻣﺴﺠﺪﺍ؟ ﻋﻠﻤﺎ ﺍﻧﻬﺎ
ﻓﺮﻉ ﻣﻨﻪ، ﻭﻫﻞ ﺳﺎﺣﺔ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﺗﻌﺘﺒﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ،
ﺍﻱ ﻳﺘﺮﺗﺐ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺍﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻣﻦ ﺻﻼﺓ
ﻟﺮﻛﻌﺘﻴﻦ ﻭﻋﺪﻡ ﺍﻟﺒﻴﻊ ﻓﻴﻪ ﻭﻧﺤﻮﻩ؟ ﺝ: ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﺩﺍﺧﻞ
ﺳﻮﺭ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻓﻬﻮ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻭﻟﻪ ﺣﻜﻢ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ
ﻓﺮﺣﺒﺔ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ، ﻭﻣﻜﺘﺒﺔ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻣﻦ
ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﺍﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻛﻞ ﻣﻨﻬﻤﺎ ﺩﺍﺧﻞ ﺳﻮﺭ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﺍﻻ
ﺍﻧﻪ ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﻻﺣﺪ ﺍﻥ ﻳﺼﻠﻲ ﻓﻴﻬﻤﺎ ﻭﻳﺘﺮﻙ ﺍﻟﺼﻼﺓ
ﻣﻊ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﺑﻞ ﻳﺠﺐ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻥ ﻳﺼﻠﻲ ﻣﻊ
ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﺿﻤﻦ ﺍﻟﺼﻔﻮﻑ ﺍﻟﺘﻲ ﺧﻠﻒ ﺍﻻﻣﺎﻡ)).
Ma’ana: ((Tambaya: Ko za a dauki
maktabar masallaci tamkar
masallaci? Duk kuwa da cewa ita
(maktabar) reshe ce na shi
(masallacin), kuma ko za a dauki
harabar masallaci a matsayin
masallaci, watau a ba shi dukkan
hukunce-hukuncen masallacin,
kamar yin salla raka’a biyu, ko
hana yin ciniki a cikin shi, da
makamancin hakan? Amsa: Abin
da duk yake cikin katangar
masallaci to shi ma masallacin ne,
yana kuma da hukuncin masallaci,
saboda haka harabar masallaci
masallaci ne, maktabar masallaci
masallaci ne, idan dai ko wani
daya daga cikin nasu yana cikin
katangar masallacin, sai dai kuma
ba ya halatta ga kowa ya yi salla a
cikinsu ya bar yin salla tare da
liman cikin jam’i, a’a wajibi ne a
kansa ya yi salla cikin jam’i cikin
safun da ke bayan liman)). Intaha.
Mu ma a nan muna kan abin da
mafi yawan Shafi’iyyah, da kuma
Al-Lajnatud Daa’imah suka fada.
Leave a Reply