Wannan kenan, sannan a cikin
kokarin cewa Sayyidina Aliyyu shi
ne ya fara salatil fatihi akwai
karyata abin da shi wanda ya zo da
salatil fatihin ya fada na cewa an yi
masa wahayinta ne a takardar
haske, kamar yadda bayanin haka
ya zo a cikin littafin (Jawahirul
Ma’ani 1/58) shehu Tijjani ya ce,
“Ita salatil Fatihi ba Bakari ba ne ya
wallafata ba, a’a yadda abin yake,
shi Bakari ya fuskanci Allah ne
tsawon lokaci mai yawa a kan
Allah ya bashi wani salati ga
Annabi (S.A.W), wanda a cikinsa
akwai ladan dukkan salatai, da
sirrin dukkan salatai. Ya dade yana
neman wannan abu (a wajen
Allah), sannan sai Allah ya amsa
masa addu’arsa, sai Mala’ika ya zo
masa da wannan salati, a rubuce a
cikin takardar haske”.
Wannan shi ne asalin samun
wannan salati, kuma shi ne abin da
Mal Madu ya kamata ya kawo.
Wanda idan muka dubi wannan
magana da kyau zamu ga akwai
matsala mai girma wajen gasgata
wannan batu, saboda dai babu
wani mutum koma bayan Manzon
Allah (S.A.W) da zai ce Mala’ika ya
kawo masa wani abu, kuma a
karba a rika bautawa Allah da
wannan abu, bayan Manzon Allah
(S.A.W) har ya bar duniya bai
koyawa Al’ummarsa wannan abu
ba, yarda da wannan, tuhumar
Annabi ne (S.A.W) cikin isar da
sako, kuma yarda da ne da wani
Annabi ne bayan Manzon Allah
(S.A.W), wannan kuma shi ne sirrin
da ya sa wadanda basa yin ta, ba
sa bauta wa Allah da wannan
salati, ba kamar yadda Mal Madu
yake so ya nuna ba na cewa, ai
tunda lafuzzanta na da kyau ba laifi
a bautawa Allah da ita.
Wani Abin da Mal Madu ya kawar
da kansa daga gare shi, shi ne irin
dimbin ladaddakin da wanda ya yi
wannan salati zai samu a wurin
Allah, wanda shi ma wannan ba
daga Allah ba ne, ba daga Manzon
Allah (S.A.W) ba ne.
Mai karatu ga kadan daga cikin
ladan wanda ya yi salatil Fatiha
daga inda aka samo ta wato littafin
(Jawahirul Ma’ani 1/58 – 59)
Shehu Tijjani ya ce, “Salatil Fatihi
wani lamari ne na Allah, babu
mashigar hankula a cikinsa, da za
a kaddara cewa, a samu wata
al’umma dubu dari, a kowacce
al’umma akwai kabila dubu dari, a
kowacce kabila da mutum dubu
dari, kuma kowanne daga cikinsu
ya rayu shekara dubu dari, yana
yin salati dubu ga Annabi (S.A.W),
ba tare da ya yi salatil fatihi ba,
sannan a tara ladan wannan
al’umma gaba dayanta, a tsawon
wadannan shekaru gaba daya, da
ba za su kai ladan wanda ya yi
salatil fatihi sai daya ba” Tiskashi!!.
A wani wurin shehu Tijjani ya ce,
“Salatil fatihi sau daya ta yi daidai
da duk wani zikiri da tasbihi da duk
wani istigafari da duk wata addu’a
da aka yi a duniya, karama ce ko
babba sai dubu shida”.
A Wani wurin shehu ya nakalto
daga wanda aka saukar masa da
ita, wato Albakariy ya ce, “Wanda
ya yi salatil fatihi sau daya, kuma
bai shiga Aljannah ba, to ya kama
wanda ya zo da ita a wurin Allah ya
rike shi!”
Wannan kadan kenan fa, kuma
mafi saukin abin da aka fada ne,
na ladan wannan salatin, ban da
cewa tana daidai da Alkur’ani sai
dubu shida. To yanzu dan uwa mai
karatu, zai yiwu wanda ya san
wadannan abubuwa ya yarda da
wannan salati, har ya ce zai
bautawa Allah da shi, don kuwa,
duk wanda ya san wannan, ya
kuma ci gaba da bautawa Allah da
wannan salati, to ya yi imani kenan
wani mutum zai zo da wata ibada
bayan Annabi (S.A.W) da aka yi
masa wahayinta, kuma ta shafe
abin da Manzon Allah (S.A.W) ya
zo da shi wajen lada, kai har ta kai
mutum zuwa Aljannah!!. Tabbas
na san Mal Madu ya san hukuncin
yarda da cewa akwai wanda ake
masa wahayi bayan Annabi
(S.A.W). Allah ya kare mu.
A karshe ina so dan uwa Mal Madu
da ire-iren masu fahimtarsa, su
sani cewa, rashin yin salatil fatihi,
ko yarda da ita, baya nufin kafirta
duk wanda yake yinta ba ne
Saboda masu yin ta sun kasu gida
biyu ne :
1 – Kaso na farko : Wadanda basu
san hakikaninta ba, ba su san
yadda ta zo ba, ba su san abin da
aka dabaibayeta da su ba na lada,
da nuna fifikonta akan salatin da
Annabi (S.A.W) ya zo da shi, su dai
kurum an ce musu salati ne ga
Annabi (S.A.W), don haka suke
yinta. Wadannan babu abin da
suke bukata illa karantarwa da
nuna musu salatin Annabi (S.A.W)
na gaskiya, wanda ya zo da shi,
wannan kuma shi ne halin da yawa
daga cikin mutanen kasarmu.
2 – Kaso na biyu : Wadanda sun
san wadannan abubuwa, kuma
sun kudurce su, sun yarda da su,
don haka suka rungume ta suna yi,
to wannan hukuncinsu yana ga
Allah, amma dai alal hakika suna
kan hadarin barin musulunci,
saboda yarda da wahayin ibada ne
bayan Annabi (S.A.W).
Amma maganar wani ya ce yana
yin ta ne don salati ne, kuma bai
yarda da abin da aka fada na
falalarta ba, to wannan shi ma
dayan biyu ne :
1 – ko dai wanda yake yaudarar
kansa, ya san ba haka abin yake a
ransa ba, kurum dai ya fada ne,
don kada a ritsa shi da wadannan
abubuwa, ya kasa bada amsa.
2 – ko wanda bai san abin da aka
fada a kanta din ba, don haka yana
bukatar ya je ya kara binceke.
Allah Madaukakin Sarki ya datar
da mu, ya nuna gaskiya, ya bamu
ikon binta, ya nuna karya, ya bamu
ikon guje mata
Leave a Reply