Salatil Fatihi A Ma’aunin Musulunci (2)(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Wannan kenan, sannan a cikin
kokarin cewa Sayyidina Aliyyu shi
ne ya fara salatil fatihi akwai
karyata abin da shi wanda ya zo da
salatil fatihin ya fada na cewa an yi
masa wahayinta ne a takardar
haske, kamar yadda bayanin haka
ya zo a cikin littafin (Jawahirul
Ma’ani 1/58) shehu Tijjani ya ce,
“Ita salatil Fatihi ba Bakari ba ne ya
wallafata ba, a’a yadda abin yake,
shi Bakari ya fuskanci Allah ne
tsawon lokaci mai yawa a kan
Allah ya bashi wani salati ga
Annabi (S.A.W), wanda a cikinsa
akwai ladan dukkan salatai, da
sirrin dukkan salatai. Ya dade yana
neman wannan abu (a wajen
Allah), sannan sai Allah ya amsa
masa addu’arsa, sai Mala’ika ya zo
masa da wannan salati, a rubuce a
cikin takardar haske”.
Wannan shi ne asalin samun
wannan salati, kuma shi ne abin da
Mal Madu ya kamata ya kawo.
Wanda idan muka dubi wannan
magana da kyau zamu ga akwai
matsala mai girma wajen gasgata
wannan batu, saboda dai babu
wani mutum koma bayan Manzon
Allah (S.A.W) da zai ce Mala’ika ya
kawo masa wani abu, kuma a
karba a rika bautawa Allah da
wannan abu, bayan Manzon Allah
(S.A.W) har ya bar duniya bai
koyawa Al’ummarsa wannan abu
ba, yarda da wannan, tuhumar
Annabi ne (S.A.W) cikin isar da
sako, kuma yarda da ne da wani
Annabi ne bayan Manzon Allah
(S.A.W), wannan kuma shi ne sirrin
da ya sa wadanda basa yin ta, ba
sa bauta wa Allah da wannan
salati, ba kamar yadda Mal Madu
yake so ya nuna ba na cewa, ai
tunda lafuzzanta na da kyau ba laifi
a bautawa Allah da ita.
Wani Abin da Mal Madu ya kawar
da kansa daga gare shi, shi ne irin
dimbin ladaddakin da wanda ya yi
wannan salati zai samu a wurin
Allah, wanda shi ma wannan ba
daga Allah ba ne, ba daga Manzon
Allah (S.A.W) ba ne.
Mai karatu ga kadan daga cikin
ladan wanda ya yi salatil Fatiha
daga inda aka samo ta wato littafin
(Jawahirul Ma’ani 1/58 – 59)
Shehu Tijjani ya ce, “Salatil Fatihi
wani lamari ne na Allah, babu
mashigar hankula a cikinsa, da za
a kaddara cewa, a samu wata
al’umma dubu dari, a kowacce
al’umma akwai kabila dubu dari, a
kowacce kabila da mutum dubu
dari, kuma kowanne daga cikinsu
ya rayu shekara dubu dari, yana
yin salati dubu ga Annabi (S.A.W),
ba tare da ya yi salatil fatihi ba,
sannan a tara ladan wannan
al’umma gaba dayanta, a tsawon
wadannan shekaru gaba daya, da
ba za su kai ladan wanda ya yi
salatil fatihi sai daya ba” Tiskashi!!.
A wani wurin shehu Tijjani ya ce,
“Salatil fatihi sau daya ta yi daidai
da duk wani zikiri da tasbihi da duk
wani istigafari da duk wata addu’a
da aka yi a duniya, karama ce ko
babba sai dubu shida”.
A Wani wurin shehu ya nakalto
daga wanda aka saukar masa da
ita, wato Albakariy ya ce, “Wanda
ya yi salatil fatihi sau daya, kuma
bai shiga Aljannah ba, to ya kama
wanda ya zo da ita a wurin Allah ya
rike shi!”
Wannan kadan kenan fa, kuma
mafi saukin abin da aka fada ne,
na ladan wannan salatin, ban da
cewa tana daidai da Alkur’ani sai
dubu shida. To yanzu dan uwa mai
karatu, zai yiwu wanda ya san
wadannan abubuwa ya yarda da
wannan salati, har ya ce zai
bautawa Allah da shi, don kuwa,
duk wanda ya san wannan, ya
kuma ci gaba da bautawa Allah da
wannan salati, to ya yi imani kenan
wani mutum zai zo da wata ibada
bayan Annabi (S.A.W) da aka yi
masa wahayinta, kuma ta shafe
abin da Manzon Allah (S.A.W) ya
zo da shi wajen lada, kai har ta kai
mutum zuwa Aljannah!!. Tabbas
na san Mal Madu ya san hukuncin
yarda da cewa akwai wanda ake
masa wahayi bayan Annabi
(S.A.W). Allah ya kare mu.
A karshe ina so dan uwa Mal Madu
da ire-iren masu fahimtarsa, su
sani cewa, rashin yin salatil fatihi,
ko yarda da ita, baya nufin kafirta
duk wanda yake yinta ba ne
Saboda masu yin ta sun kasu gida
biyu ne :
1 – Kaso na farko : Wadanda basu
san hakikaninta ba, ba su san
yadda ta zo ba, ba su san abin da
aka dabaibayeta da su ba na lada,
da nuna fifikonta akan salatin da
Annabi (S.A.W) ya zo da shi, su dai
kurum an ce musu salati ne ga
Annabi (S.A.W), don haka suke
yinta. Wadannan babu abin da
suke bukata illa karantarwa da
nuna musu salatin Annabi (S.A.W)
na gaskiya, wanda ya zo da shi,
wannan kuma shi ne halin da yawa
daga cikin mutanen kasarmu.
2 – Kaso na biyu : Wadanda sun
san wadannan abubuwa, kuma
sun kudurce su, sun yarda da su,
don haka suka rungume ta suna yi,
to wannan hukuncinsu yana ga
Allah, amma dai alal hakika suna
kan hadarin barin musulunci,
saboda yarda da wahayin ibada ne
bayan Annabi (S.A.W).
Amma maganar wani ya ce yana
yin ta ne don salati ne, kuma bai
yarda da abin da aka fada na
falalarta ba, to wannan shi ma
dayan biyu ne :
1 – ko dai wanda yake yaudarar
kansa, ya san ba haka abin yake a
ransa ba, kurum dai ya fada ne,
don kada a ritsa shi da wadannan
abubuwa, ya kasa bada amsa.
2 – ko wanda bai san abin da aka
fada a kanta din ba, don haka yana
bukatar ya je ya kara binceke.
Allah Madaukakin Sarki ya datar
da mu, ya nuna gaskiya, ya bamu
ikon binta, ya nuna karya, ya bamu
ikon guje mata

55 responses to “Salatil Fatihi A Ma’aunin Musulunci (2)(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)”
  1. ibrahim g.muhammad Avatar
    ibrahim g.muhammad

    ALLAH KA KARA GANAR DAMU SUNNAH.

    1. Muhammad Abubakar Avatar
      Muhammad Abubakar

      Allah ya ganar damu gaskiya

  2. ILIYASU IBN ALIYU Avatar
    ILIYASU IBN ALIYU

    Allahumma salli Ala sayyidina Muhammad Alfatihi lima ugliqa walkhatimi lima sabaqa nasirul haqqi bilhaqqi walhadi ila siradikal mustaqimi wa’ala ahlihi haqqa qadrhi wamiqidarihil azim.
    Muhammad Rabiu Rijiyan lemu babu shakka kana da ilimi ka kauda jahilci akanka amma sauran abu guda ne ka rasa,abunnan kuwa shine tsoma baki akan abunda bai shafeka ba yakamata ka kiyaye harshenka da abubuwa kamar haka dan iliminka ya amfane ka
    1.minal fahasha’i 2.walmunkar 3.wal kalamul kabihi 4.wa,aimanud dalaqi 5.wa,intiharul musulumi 6.wa,ihanatihi 7.wasabbihi 8.wattakawifihi .
    Amma ba,ad.
    Tambayana anan wai shin wasu lafuza ne abun ki ciki salatil fati? Ko kuna ganin akwai lafuxan da girmansu sun ma Annabi yawane cikin salatin?. AMMA kASAN SHEHU TIJJANI KUWA?IDAN BAKA SANSHI BA MENENÉ NAKA NASHIGA CIKIN LAMARINSA WANDA SHI BAI SHIGA CIKIN NAKABA? Kuma daka fada wasu daka cikin falalar salatil fati shin kaka ga wayanda sukai imani da ita basu karanta Alqur.anin ne? Koko basuyin sallarne?ko haddar Alqur.an?duk da ance karanta salatin sau daya yafi karanta Alqur,ani sau dubu shida?? Ko kana ganin cewa itace kadai salatin da sukeyi?. Sabila shehu ya sanardasu cewa idan akace ya ummurcesu dawani aiki toh su auwana ta da ma,aunin shari,a ta dace da maunin ko ta sabada ma,aunin, idan tayi daidai suyi inko ta saba to suyi watsi da ita maganar ba daga gareshi bane. sai yasa makaranta salatin haddan Alqur.ani suke tayi.
    MUSULUNCI YAZO MANA DA ADALCI SAI YASA AKA UMMARCEMU MUYI ADALCI. Rashin Adalci shi ya kawo mana rashin xaman lafiya akasarmu da duniya baki daya. Duk duniya babu abunda yakai Addini mahimmanci da xa,a baiyawa malamai masana addinin da mun xauna lafiya. Kaga idan da xaka lura likita bakowa ya iya ba tukin mota ko jirgi,mashin bakowa ya iyaba sai direbobinsu hakama gyaransu sai kanikancinsu haka alqalanci sai alqalai komai da komai da komai idan aka dorashi a hannun wa,yanda suka iya sai ka ga komai ya tafi daidai amma sai gashi abunda yafi komai mahimmanci kowa yace ya iya, mutum da ya haddace wani littafi wai shima ya xama shehu yana ba da fatawa ko tako ina harda inda bai karanta ba yana bada fatawansa .alhali ko karatun boko ne kowa da fanninsa kuma kowa xaifi xurfi ne akan fanninsa,idan ka tambayeshi akan wani fanni xaice maka bai saniba kuma dan yafada hakan baiyi abun kunya dan ba abunda yakaranta bane Kuma baka isa ka kirashi jahili ba. Malam inaso kasani Malamai masana addini sunce mana Antaba tambayan Sayyadina Abubakar ma’anar wata Aya cikin alqur’ani yace bai saniba alokacin kuma yana kalifanci sahabbai sukace ya kana kalifan manzon Allah(S.A.W) Atambayaka kace baka saniba sai yace masu to karya suke so yayi.toh kaga anan ashe ba gaxawa bane Atambayeka kace bakasani ba kuje ku tambaye masu yin abun Kamar yadda Allah Yace ‘Fas alu ahalazzikiri in kuntum laa ta’alamun”.
    TOH jama’a yakamata mui ma kanmu adalci kuma sai ai hattara kowa ya tsaya a inda Allah Ya ajeshi Dan azauna lafiya.

    1. Ismail Avatar
      Ismail

      Soki burutso kenan@iliyasu ibn aliyu , kai amma ka iya bankaura. To wallahi bamu ba salatin karyan nan daku jinginashi da manzo. Allah sarki!!! Gaskia kasha gubar aqidar nan dawa. Amma allah yasa kagane cewa ba wani abu acikin aqidarku sai cuwa-cuwa, da kula kula, da kage kage da karerayi da sunan son manzo.

    2. Ismail idris Avatar
      Ismail idris

      Soki burutso kenan@iliyasu ibn aliyu , kai amma ka iya bankaura. To wallahi bamu ba salatin karyan nan daku jinginashi da manzo. Allah sarki!!! Gaskia kasha gubar aqidar nan dawa. Amma allah yasa kagane cewa ba wani abu acikin aqidarku sai cuwa-cuwa, da kula kula, da kage kage da karerayi da sunan son manzo.

      1. Buhari haruna musa Avatar
        Buhari haruna musa

        Kai dai kurum kayi abinda ya dameka,Malam zaka nuna MANA ka waye,to sai anyi salatil phatihi sai dai ka fadi ka mutu saboda bakin ciki,Ni dai fatana kayi abinda ya dameka …

  3. asheer gimi Avatar

    allah ka yi mana albarka

  4. AMINU FADA AKURBA LAFIA Avatar
    AMINU FADA AKURBA LAFIA

    Idan zakayi magana kafadi wanda kasani ta iya fa himtarka karkashika hanyarda banaka ba

  5. Mustapha kaura Avatar
    Mustapha kaura

    Don Allah malan inason afasara man maanarta

  6. Nasrullah Avatar

    Wawa, jahili, dakiki, dangin yahudu……banda jahilci da karancin ilimi, ai Sayyadi Ali (as) shine ya fara yin salatil fatih kuma yace yajine daga Annabi Muhammadu (saw)…kana nufin Annabi ne yayi karya ko sayyadi Ali, ko kuwa tsaban dakikanci ne da kiyayya da kuke yiwa Annabi wanda kungiyar Izala to koyar daku??? To wallahi kayi hattara in ba haka ba sai ka mutu da haushin kare kamar yadda sama’ila idris yayi ko kuma ka mutu babu kai a gangar jikinka kamar mahmoud gumi na kaduna

    1. Nibras Avatar

      Wannan shine dalilin mara dalili, zagi da hayaaniya. In abinda aka fada karyane ka kawo dalili mana.

  7. nazifirabiua Avatar

    Gaskiya ne Allah ya tabbatar da mu akan sunnah

  8. Abdoulkarim Avatar

    masha Allaah

  9. Abdoulkarim Avatar

    annan shine dalilin mara dalili, zagi da hayaaniya. In abinda aka fada karyane ka kawo dalili mana.???????????????????????????

  10. anas usman Avatar
    anas usman

    idan salatil fati ba gaskiya a cikinta, to ya ya za a yi a hana yin bautan Allah da shi

  11. Mohammad Gambarawa Avatar
    Mohammad Gambarawa

    Hakika maalaminku yayi bayani,Amman abin mamaki Kuma abin da yamanta shine;a duniyar muslunci Allahu S.W.T. da manzonsa Annabi Muhammad kuma shugaban halitta S.A.W. ne kadai zasu ce ABU kaza ya halitta ko kuma bai halitta ba. Amman abin haushi. kuma abin takaici yace maku salatul fatihi babu kyau Baku tambayarsa cewa shin Allah ne yace ba kyau ko manzon Allah koko a wane littafi yaga anfada bata da kyau .Inaba malaninku shawara cewa ya rage girman kai da tunanin cewa shi mai ilimi ne yatafi fadar malamai yasha namaki Yakuma Ji abunda malamai suka FADA akan salatul Fatihi.Kukuma yan kallo a koma makaranta wajen malamai na gaskiya acigagaba da karatu insha Allah zaa gane.

  12. Mubarak Avatar
    Mubarak

    Annabi ya ce; yana daga cikin kawun musuluncin mutum ya bar abinda bazai amfaneshiba. kuma ya ce ku tambayi ahalin abu idan kun kasance baku da ilimi game da abin

  13. Nasiru musa Avatar
    Nasiru musa

    Ni da inayin salatil fati amma tunda Nagano salatil fati jabun salatine na saki na tuba nakama original wato salatin Annabi da ya koyar da bakinsa mai tsaki

  14. ALLAH UBANGIJI KASA MUCIKA DA IMANI BIJAYI ANNABI Mohamad (s.a.w)

  15. yan izala baku fahimtar addini saboda aqidarku irin ta yahudawa cewa duk abinda kwakwalwa ta kasa ganowa ba gaskiya bane. ku sani ilmi irin na maarifa ba wai littafi zaka dauka ka ganoshi ba. ilmi ne wanda allah ke basuwa sakamakon tsalkakan zuciyya har ta sami wusuli saboda taqwa(wattaqullah wa yullimukumullah). masu wannan ilmi suke samun ainahin sirrin alqurani.misali inda ayar qurani take cewa”innallaha wa malaikatuhu yusalluna alannabiyyi ya ayyuhalladhina amanu sallu alaihi” sai allah ya sanarda shehu tijjani ta hanyar ilhama da ruuya ba wahayi sabo ba cewa salatil fatihi ta shigo cikin umumil aya da tayi umurni “sallu alaihi(kuyi salati ga annabi)”.salatul ibrahimiyya misali ne na wada ake yima annabi salati ba rufe kofar yin salati ga annabi aka yi ba don babu annabi yace kada ayi wani salati in ba wannan ba. wannan kashfi ya zo ma shehu tijjani haqiqatan. ko wahhabiyawa na son suce idan abu ya faru ga mutum shice abin bai faru ba? kuma cewa baannabe kawai malaika ke baiyana ma wata fahimta to da malaika ya baiyana ga maryam fa ?ita annabi ce .salatil fatihi ba sabo wahayi ba ne , fahimta ce ta maanar umarnin da ke ciki aya kamar wada mukayi bayani a sama.mutane irin su shehu usmanu danfodiyo sun sha baiyana wasu sirrori na quran ba tare da sun koya daga littafi ba. sai suce ilminda allah ya jefa zuciyarsu ba haka bane. abinda yassa wahabiyawa basu samun irin wannan ilmi zauqi(by experience)sabo da basu yawan ibada da zata tsalkaka zukatansu har ta sami annuri da zai sada ta da allah ta sami ilhama ko kashfi. suna kwantawa suna ta barci suna ta tusa bayan gama hawan mata.yaya zasu gano abinda wadanda”tataja junubihim anil madajii” zasu iya ganowa. ina fatar yan izala suna fahimtan abinda nake fada su daina hawan karan tsaye akan abinda basu san wada aka ganoshi ba. su sani taba mutuncin waliyyai irin su shehu tijjani nada hadari.shehu usmanu bin fodiyo ya fada cikin ihyaussunnatil muhammadiyya wa ihmadu bidiatu shaitaniyya a babin ihsan cewa inkarin karamomin waliyyai na kawo suul khatima(mugunyar mutuwa ba kalmar shahada) kuma an sha ganin yan izala na kuwwa lokacin daukan rai ba kalmar shahada sabanin yan dariqa. ku tambayi likitoci da mutane ke mutuwa gabansu

  16. mami abdullahi Avatar

    SLM malam dan Allah addu ar biyan bukata nake so Wanda zanyi kaifi wuka

  17. umar Avatar
    umar

    Gaskia akwoi matsala, haba malam iliyasu yaza’a kawo sabon abu a musulinci kace bai shafe shi baccin kuma yana musulmi, ai inaga duk abunda ke cikin addinina ya shafeni saidai indama ita salatil fatin ba addininin bace, kuma da ka kawo misali da saiyaddina abubakar, ai bakace aiyar bata shafeshi ba,
    Kaikuma nasiru maganar ilimi akeyi ba zagi ba in kana dana ka sai ka kawo hujjah sai, a saurareka kaji
    Kaikuma gambarawa, ai ka mance Allah yace muyi ma Annabi SAW salati, sannan Annabi yace ga yadda zamuyi, watau kun kasa fahimtar yan izalah, ne,
    Dan izalah bai yadda cewa ba akwoi wani waliyyi wanda yakai Annabi SAW, shiyasa komi akace gashi yana da falala in ba Annabi SAW yafada bai yarda shiyasa akace kabar wanda shehu tijjani ya koyar ka dauki wanda bakin da baya karya ya kowar watau Annabi Muhammadu SAW

  18. Zainuddeen Avatar
    Zainuddeen

    Ni dai na dauki salatul fatih abisa salati wanda kowa ma zai iya hadawa matuqar kalmomin da aka hada basu kaucewa addini ba,Shi kuma salatin Ibrahimiyya na dauke shi abisa Salatin da in kai kana da lada biyu ladan sunnah da ladan salati sabanin sauran salatai wadanda su ladan salati ne kawai.

  19. Assalamu alaikum warah matullahi wabarka tuhu ina rokon allah yaba malam lafiya kuma ya karamasa ilimi mai yawa mai amfani. Amin wassalam

  20. muhammed nasir Avatar

    wannan gaskiya ne abinda kafada malam allah ka kara tabbatar damu akan sunnah.

  21. falalou Avatar
    falalou

    Malam, a koma makaranta da sawran karatu. Ga chawarata, ka samu daya daga cikin malaman tijjaniya ya baka karatu.

  22. muhammadmusa Avatar
    muhammadmusa

    Kai jahilci baiba….dama annabi yace wabda Allah ya nupeshi da alkairi sai ya fahimtar dashi addini. Menenne aibun salatil fatih??? Wahabiyawa bakwa karatu kuma baku fshimci addininba ….sabida kun wulaqanta manyan waliyai da sufaye wadanda sune suka tafiyar da sunnar annabi bayan wafatinsa da sahabbansa da tabiai…Allah ya ganar damu

  23. Saleembinusman77 Avatar
    Saleembinusman77

    Salatul fati tsumma ma yafishi

  24. MURTALA MAGAJI BABURA Avatar
    MURTALA MAGAJI BABURA

    ALLAH KA SA MU A HANYA MADAIDAICIYA AMIN.

  25. Saleembinusaman77@gmail.com Avatar

    Kafircin shii,a 1 taqiyya agurin shi,a duk wanda bayayinta toba musulmibane

  26. Saleembinusaman77@gmail.com Avatar

    Da salatil fatih gara tsumma

  27. ayaune mlm Alqaseem da mlm Abubakar baban gwale. xasu gabatarda lecture agarin wudil insha Allahu

    1. sadeeq kabeer bichi Avatar
      sadeeq kabeer bichi

      Haba saleem yazaka ce da salatil fatihi gwara tsumma wannan kuskure ne domin kuwa idan kaduba fassarar salatin zakaga cewa annabi aka dosa bawai son rai akayi ba

  28. sadeeq kabeer bichi Avatar
    sadeeq kabeer bichi

    Haba saleem yazaka ce da salatil fatihi gwara tsumma wannan kuskure ne domin kuwa idan kaduba fassarar salatin zakaga cewa annabi aka dosa bawai son rai akayi ba

  29. sijangebii Avatar

    SUBHANALLAH! Ku masu Kare Salatil Fatih, har yanzu banji wani yace ga hujjar yin saba. Ba Wanda ya kawo Aya ko Hadisi ko wani bayani mai gamsarwa daga Sahabbai ko Tabi’ai akan ingancinsa ba.

  30. […] Source: Salatil Fatihi A Ma’auninMusulunci (2)(Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo) […]

  31. Mahammad Dahiru Abubakar Avatar
    Mahammad Dahiru Abubakar

    Allah ka qara ganar damu sunnah da ikon binta da rungumarta

  32. uthman tijjani Avatar
    uthman tijjani

    yan xu ne na tabbata wasu malaman ba sa karatu domin salatin FATI NA annabi be kuma duk me yin ta xai Shiga aljanna da izinin Allah

  33. nasirsaniumardaura Avatar
    nasirsaniumardaura

    to Mlm Rabe rijiyar lemo mizakace game d salatin malaman imam shafi i .dasukace wann salatin yafi kowane salati.allahumma salli alah sayyiduna muhammadu kullama zakahuzzakirina w gafala anzirihizzakirina km basu kebe kowane salatiba

  34. khalid yunusa Avatar
    khalid yunusa

    Bilal Sambo
    ……..{{{{{{{ SALATUL FATIH }}}}}}}
    INGANCIN “SALATUL FATIH” DAGA KITABU WA
    SUNNAH
    **{salatin Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ }*
    A gaskiya ya kamata duk wanda yake dalibin Ilimi
    ne, to ya daina amfani da jite jiten mutani domin
    gudun faadawa cikin halaka.
    Domin so dayawa yan Izala domin basa son dariqa
    sai su dinga karya suna mana sharri da kazafi.
    Kuma sai suce a cikin “Jawahirul ma’aani” aka
    rubuto.
    “bi’isa lizzamina badala”
    Haka wani dan izala ya tura min message ta inbox,
    ya bani haushi, amma kuma gaskiya ya bani dariya
    sossai.
    GA ABINDA YACE MANI:
    Bilal kake wa? Ya kamata ku dinga tsoron Allah ku
    daina karya, acikin jawahirul ma’aani shafi na 164″
    shehu Ibrahim yace an yi masa wahayin salatul
    fatih. Waiyazubillah.
    Me zaka ce akan wannan? Kuma kada kayi karya
    domin ga Jawahirul Ma’ani din a hannuna. sai
    najika…
    **Haba!! Wani kariya ne haka?
    Ba shehu Ibrahim ba, ko Shehu Tijjani { ﺭﺿﻲﺍ ﻟﻠﻪﻋﻨﻪ}
    yazo duniya ya tarar da Salatul Fatih balle shehu
    Ibrahim{ ﺭﺿﻲﺍ ﻟﻠﻪﻋﻨﻪ}.
    Salatu Fatih::
    kamin mu shiga bayani ya kamata musan shin:
    >> Me nene SALAT??
    >> Me nene FATIH???
    DOMIN KALMOMI NE GUDA BIYU AKA HADASU
    {salatul fatih}.
    Allah yana cewa:
    “wa salli alaihim inna salaataka sakanan lahum…
    {Q9:103}
    A wannan ayar Allah yayi wa Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
    ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ umurni da yayi wa bayinsa{na kwarai}
    addu’a domin hankalinsu ya kwanta.
    Acikin wata ayar kuma yace:
    “walaa tusalli alaa ahadin minhum mata abada…..
    {Q9:56}
    Anan kuma Allah ya hana Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ
    kada yayi wa kowani daya daga cikin su addu’a
    {matattun munafuqai kenan}.
    To wannan misalai sun ishe mu gane ma’anar
    SALAT anan shine “ADDUA”
    Na biyu kuma:
    Salat na daukar ma’anar “IBADA” ko ADDU’A.
    Kamar yanda Ibn kathir ya nuna. Saboda fadin
    manzo s.a.w cewa:
    ” Izaa da’a ahadakum ilaa ta’aamin fa’in kaana
    sa’iman fal yusalli….
    **idan ankira{gayyace} dayanku wurin cin abinci, to
    idan ya kasance yana Azumi ne to yayi Sallah…
    {a nan salaat Ibaada ne kenan}.
    AL~FATIH: shine “budewa” kamar ayar farko a
    qur’ani suratul “Fatiha” da surar aka bude qur’ani.
    Shi yasa ma’anar “Salatul Fatih” “Addu’ar
    budewa”{budewar Rahma marar iyaka}.
    Kuma daya ne daga cikin sunayen Allah, kuma data
    ne daga cikin sunayen Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ
    Shi yasa ku masu shegantaka kuna cewa SALATIN
    FATI ko kuma SALATIN PARTY domin ayi dariya, to
    wallahi kuna cikin Hatsari babba!!!
    Domin mayarda ayoyin Allah da Annabi{s} abin
    wasa ko ayi dariya KAFURCI ne, koda kullum
    Azumu da karatun qur’ani kakeyi Allah zai rusa
    ayyukan mutum gabadaya saboda wannan
    wallahi…
    Allah yace mamaki da yana mamaki:
    ﻗﻞ ُُﺃﺑﺎِﻟّﻠﻪَﻭَﺁﻳﺎَﺗﻪِﻭﺭ ﺳَﻮﻟﻪِﻛﻨُﺘﻢُ ﺗﺴﺘْﻬَﺰْﺅِﻭُﻥ ??? ﻻﺗﻌَﺘْﺬَﺭﻭﺍﻗﺪَﻛ
    ﻔَﺮَﺗﻢُ ;;;
    shi yasa a kula….
    ** wanda Allah ya bada Salatul fatih ta hannun sa,
    akan Tartibin da muke amfani dashi, shine
    “Muhammadu Al~bakari{RA} ta hanyar {KASHFU}
    Amma inda rigimar take shine yawancin yan Izala
    suna cewa ta yaya Allah zai bada wani abu addinin
    musulici bayan Allah yace:
    “Al yauma akmaltu lakum dinukum wa atmamtu
    alaikum ni’imati waraditu lakumul islama dinan.?
    Domin acikin ayar Allah yake cewa a yau na cika
    maku addininku, daga nan aka kulle wahayi….
    Abakar Gumi” yayi maganganu akan haka sossai
    cewa ta yaya Allah zai ce wa Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
    ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ “A YAU NA KAMALLA MAKU ADDININKU”
    amma wani yazo waishi anyi masa wahayi{yayi
    surutai dayawa “zomo}.
    Shine “KABIRU GOMBE” shima yana cewa, to a
    tambayi Muhammad Bakari” shin wahayin Salatul
    fatih, kamin “Alyauma akmaltu lakum dinikum” ne
    akayi ko kuma bayan saukar ayar “Al’yaumal
    akmaltu”
    Domin ba’a saukar da wata aya ba, a bayan
    Al~yauma akmaltum.
    DAYAKE SU YAN IZALA DASU DA MALUMAN SU
    DUK BASA KARATU……
    {suratul ma’ida:3}
    “Al yauma akmaltu lakum dinukum wa atmamtu
    alaikum ni’imati wa radeetu lakumul islam dinan.
    ** Duk wanda yace bayan wannan ayar babu
    wahayi to Jahili ne, dakiki ne wawa ne kuma
    mahaukaci….
    A ranar da aka saukar da wannan ayar: {Q5:3}
    ranar Juma’a ne, a Arfa” manzon Allah{ ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
    ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ } yana zaune akan Rakumin shi.
    > Bayan saukar ayar “Alyauma Akmaltu” Allah ya
    saukar ayar karshe na suratul Nisa’i. 176:
    “yastaftunaka qulillahu yuftikum fil kala………… Ilaa
    akhiriha.
    > Bayan wannan da kwana Hamsin{50days} Allah
    ya saukar da aya ta dari da ashirin da takwas
    {128:suratu Taubah}
    “lakad jaa akum Rasulun min anfusikum azizun
    alaihi maa anintum harisun Alaikum bil mu’mineena
    ra’ufun raheem wa’in tawallau fakul hasbiyallah
    laa’ilaaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa rabbul
    arshil azeem..
    Bayan wannan da kwana talatin da biyar{35days}
    sa’annan Allah ya saukar da aya ta dari biyu da
    tamanin da daya{281:Baqara}
    “wattaqu yauman tur’jauna fihi ilallah summa
    tuwaffa kullu nafsin maa kasabat wahum laa
    yuzlamun:
    Duk wa’annan bayan “Alyauma akmaltu” ne ko
    kuma su ba wahayi bane??
    Sa’annan kamin Annabi{ ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ } yayi
    wafati, bayan ayoyin qur’ani gabadaya sun gama
    sauka, Allah yayi masa wahayi na “Hadithil Qudsi”.
    Na kawo wannan ne domin yan izala dake yawan
    cewa bayan wannan aya aka rufe wahayi.{Jahilai}
    Intaha….
    Abubakar Gumi yayi suratai sossai akan salatul
    Fatih.Acikin littafin sa
    “AQIDATUL SAHIHA”{shafi na 22} yace:
    *hazaa walam yarwi an ahadin min a’immatil
    hadeeth lafzu SALTUL FATIH” walam yasnidhu
    ahadin ilan Nabiyy{s} fi hayatihi walaa ilaa ahadin
    min sahabatihi wa tabi’eena wa tabi’i tabeen.
    {GUMI}
    Ma’ana: babu mutum ko kwaya daya daga cikin
    malaman hadithi da ya kawo irin wannan lafazi na
    salatu fatih ko isnadi zuwa ga Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
    ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ . Haka ma sahabbai da tabi’ai da tabi’i
    tabi’eena…
    Wannan yana daga cikin abinda ya jawo mana
    fitina, domin wasu yan Izala basu maganar hankali
    sai hauka da tada hargitsi sakanin al’ummah
    Annabi{ ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ } kuma sun san gaskiya
    amma suke karyata wa, idan kaji maganar da Gumi
    yayi kamin mutuwar shi zaku tabbatar da sun
    gaskiya suke karyatawa.
    “SALATI” addu’a ce kake rokon Allah ya biya maka
    bukatunka.
    Bukatar kuwa shine yayi wa Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
    ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ salati domin mu bamu iya ba.
    DUK DUNIYA BABU MUTUMIN DA YA TABA YIN
    SALATI, SAI DAI KA ROKI ALLAH YAYI WA ANNABI
    SALATI DOMIN SHI KADAI IYA SALATIN.
    To addu’a kuma sai kuce dole sai mutum yayi
    amfani da lafazi daya kawai?
    Yaushe Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ yace haka?
    Allah bai ce mana dole sai munyi anfani da wasu
    kebantattun lafuza ba wallahi!
    Abinda yace: id’uni astajib lakum” ku kirani zan
    amsa maku, to abinda wahabiyawa basu gane ba
    shine:
    Yau idan na ga dama sai ince:
    YA ALLAH KA BANI KUDI IN SAYE MOTA”
    fadin haka haramun ne??
    Ba haramun bane kuma Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ
    bai yi irin wannan addu’ar ba, kowa da irin abinda
    yake bukata, na’am acikin qur’ani akwai addu’oi
    dayawa kamar irinsu:
    * Rabbana Atina
    * Rabbigfirli
    * Rabana zalamna anfusana
    * Rabbi shirahli sadri
    * Rabbi zidni iliman etc……..
    Amma Allah bai tilasta mana cewa dole muyi
    amfani da su kadai ba.
    Ina naga dama sai ince: ya Allah ka bani sa’a domin
    inci exams..
    Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ baiyi irin wannan addu’a
    kuma babu zai ce min KALA”
    To haka abin yake ga “Salati”. Lokacin da Allah
    yace wa Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ yayi ma wasu
    mutane addu’a yace masa:
    “wa salli alihim inna salataka sakanan lahum*
    Ma’ana: kayi masu addu’a….
    Shin da Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ zai yi masu
    addu’ar, SALATUL IBRAHIMIYYA ya karanta
    masu??? To ai Salati aka ce!!
    Inda Allah yana nufin kada mu karanta wani salati
    daban, dole sai wanda Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ ya
    koyar kawai da sai ya fada a cikin qur’ani, da sai
    Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ ya fada a Hadithi.
    “DUK AYYUKAN DA ALLAH YA WAJABTA MANA
    AKAN MUYI SU, KADA MU KARA KADA MU RAGE
    KADA MU CANZA WANI LAFAZI, ALLAH YA BAMU
    SUNE TARE DA SHARUDAN SU,BAMU
    TAMBAYESHI BA.
    Misali SALLAH:
    Sai da ya gaya mana sharudanta. Yace:
    > wa aqimussalata”
    > “Inna salata kanat alal mu’mineena kitaban
    mauquta:
    >Yace: walaa taqrabus salata wa antum sukara”
    >yace: hatta tagtasilu.
    > wa akimu wujuhakum inda kulli masjidin, wad uhu
    mukhliseena…
    >Annabi s.a.w yace: Sallu kama ra’aitumuni usalli”
    > Assalatu Imamu din.. etc…
    IDAN KAYI IRIN NAKA TO SALLARKA TA LALACE.
    AZUMI:
    >”kutiba alaikumussiyam”.
    >YAUSHE?”shahru ramadAN”
    > Walaa tubashiru hunna”
    > washrabu hatta yatabayyana lakumul hatul
    abyadu minal haitil aswadu minal fajr.
    > uhilla lakum lailata siyam rafasu ila nisa’ikum…
    > summa atimmussiyam ilallail….etc
    ASSIYAMU:TARUKU TAAM:
    Sharutan azumi ne ake gaya mana.
    HAJJI:
    “wa atimmul hajja wal umrata lillah fa’in uhsirtum
    famastaisara minal hdyi walaa tuhliku ru’usakum
    hatta yablugal hadyi mahillah faman kana minkum
    mareedan aw bihi azan min ra’asihi fafidiyatun min
    siyaam aw sadaqatun aw nusuk fa’izaa amintum
    faman tamatta’a bil Umrati ilal hajji famastaisara
    minal hadyi famanlam yajjid fa siyamu salasati
    ayyam fil hajj wa saba’atun izaa raja’atum Tilka
    asharatun kamila, zaalika liman lam yakun ahluhu
    haadiril masjidil haraam wattaqullah wa’alamu
    annallaha shadidun iqaab.
    DA AYOYIN DA KE BAYAN DUKKA HUKUNCE
    HUKUNCE HAJJI DA UMRA NE.
    To haka Allah ya keyi, amma da aka saukar da
    ayar “SALATI”
    “INNALLAH WA MALA’IKATAHU YUSALLUNA ALA
    NABIYYI..zuwa karshe
    Allah bai ce ga hukunci salati ba, kada ku karanta
    salatul fatih, bai ce haka ba saboda addu’a ce,
    addu’a kuma duk lafazin da ya dace kana iya
    amfani shi.
    To shi yasa Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ bai ce komi
    akai ba,kuma manyan Sahabbai din basu tambaya
    ba domin sun san addu’a ce, wasu daga cikin
    sahabbai basu san yanda zasu yi salati ba suka
    tambayi manzo ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ yanda zasuyi sai
    ya basu SALATUL IBRAHIMIYYA amma bai ce kada
    a karanta wani daban ba.
    Yan’uwa don Allah ku karanta wanna Hadithi da
    kyau kuyi tunani akai da basira zaku gane cewa ba
    iyankance salatin Annabi{s} ba, kuma salatul
    Ibrahimiyya Annabi {s} ya karanta masu shi ne
    saboda Tawadu’u.
    Abu sa’idul Badri{R} yace muna zauna tare da
    sa’ad bin Ubadah{R} sai Annabi s.a.w ya zo
    wurinmu, sai Basher bin Sa’id {R} ya tambayi
    Annabi s.a.w cewa: ya Rasulullah!!!
    Allah yayi umarni da mu dinga yi maka salati, to ya
    zamuyi mu karanta?
    SAI ANNABI{ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠ YAYI SHURU!!!
    Sauran Sahabbai suka ce:
    “HAR MUKAYI NADAMAR “INA MA DA{bashir bin
    sa’id}BAI YI MA ANNABI{ ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ } IRIN
    WANNAN TAMBAYA BA!.
    Sai Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ yace: kace Allahumma
    salli alaa muhammad……har karshe “innaka
    hamidun majid.
    SABODA TAWADU’U
    Amma sauran manyan Sahabbai sun san cewa
    ba’a hana mutum ya karanta wani salati daban ba,
    sai suna karanta irin nasu, wallahi su duka sun
    kirkiro salatai daban daban wanda baya cikin
    wanda Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ ya karanta.
    Domin dama tun kamin a gayamasu Salatul
    Ibrahimiyya sun kasance sun yin Salati ga
    Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ
    Imaman Ahlussunnah wal jama’ah hudun na
    gaskiya{Imam malik, Abu Hanifa, Shafi’i, Hambal
    {R.jamee’a} su dukka sun karanta salatai da irin
    nasu lafazi, babu shi acikin wanda Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
    ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ ya karanta.
    Kuma mu Alhamdulillahi…….
    YAN’UWA ALBAISHIRINKU!!!
    SAYYIDINA ALI {R.A} SHI YA FARA KARANTA
    SALATUL FATIH….
    Domin naji Abubakar Gumi{tsohon najadu} yana
    cewa:
    ::”walam yarwi an ahadin min a’immatil hadeeth
    lafzu SALTUL FATIH”{aqidatul sahiha GUMI}
    Ma’ana:: daga cikin Maluman Hadithi babu ko
    dayansu da YA RUWAITO LAFAZIN “SALATUL
    FATIH”
    To ku saka masa hannu a idonshi kuce masa
    makaryaci domin yayi karya….
    Sayyadina Ali karramallah wajhahu ya karanta
    SALATUL FATIH” ya koya wa Salamatul Kindiyy
    {R.anha} Itama ta koya wa wasu sahabbai.
    Bari in fara bada hujjah da maluman da suka kafa
    wahabiyanci, almajiran Ibn Taimiyya.
    IBN KATHIR BA DAN DARIQA BANE!!!
    Kowa ya sani Almajirin Taimiyya ne.
    Ka je ka duba tafsirin Ibn kathir: karkashin aya
    kamar haka:
    “innallaha wa malaikatahu yusalluna alannabiyy ya
    ayyuhallazina amanu sallu alaihi wa sallimu
    taslima”
    Bayan fassarar ayar sai ya kawo hadithin:
    ﺣﺪﻳﺚ ﺁﺧﺮﻣﻮﻗﻮﻑ: ﺭﻭﻳﻨﺎﻩﻣﻦﻃﺮﻳﻖﺳﻌﻴ
    ﺪﺑﻦﻣﻨﺼﻮﻮﺭﻭﺯﻳﺪﺑﻦﺍﻟﺤﺒﺎﺏﻭﻳﻳﺰﻳﺪ ﺑﻦﻫﺎﺭﻭﻥ،
    ﺛﻼﺛﺘﻬﻢﻋﻦﻧﻮﺡ ﺑﻦﻗﻴﺲ : ﺣﺪﺛﻨﺎ ” ﺳﻼﻣﺔﺍﻟﻜﻨﺪﻱ :
    Wa’nnan sune suka ruwaito hadithin daga
    Salamatul Kindiyy{sahabiya ce Allah ya kara yarda
    da ita.
    Tace: sayyidina Ali{RA} ya kasance yana koya
    mana{da wasu mutane} wannan addu’a:{ ﻛﺎﻥﻳﻌﻠﻢ
    ﺍﻟﻨﺎﺱﻫﺬﺍﻟﺪﻋﺎﺀ }:
    Amma salatin na da tsawo..
    ﺍﺟﻌﻞ ﺷﺮﺍ ﺋﻒﺻﻠﻮﺍﺗﻚ ، ﻭﻧﻮﺍﻣﻲﺑﺮﻛﺎﺗﻚ، ﻭﺭﺃﻓﺔ ﺗﺤﻨﻨﻚ ،
    ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺭﺳﻮﻟﻚ
    ”ﺍﻟﺨﺎﺗﻢﻟﻤﺎﺳﺒﻖ ، ﻭﺍﻔﺎﺗﺢﻟﻤﺎﺃﻏﻠﻖ ، ﻭﺍﻟﻤﻌﻠﻦ ﺍﻟﺤﻖﺑﺎﻟﺤﻖ، ,,,,,
    ,,,,,,,,
    Ij’al sharaifa salawatka wa nawaamee barakatika
    alaa Muhammadu Abdika wa rasulika
    Al khatimu lima Sabaka, wal Faatih limaa Ughlika,
    wal mlinal Haqq bil Haqq…… Ilaa akhiriha
    duba littafin:
    Imam Qaadiy Iyyadh {Ash-shifa} juzu’i na 2 shafi
    70\72.
    > Yusufun Nabhaaniy{R} a littafin:
    :”Afdhalul-salawaat alaa sayyidil saadaat”{ya kawo
    wani rawaya na salatul fatih}
    > Imam Ibn Jazuli {R}
    {Dalaa’ilul khairaat}
    >Imam Al-qisdalaaniy{R}
    “Al-mawaahibul ladunniyya
    > Al-Sayyid Muhammad bin Hadi bin Hassan bin
    Abdul-Rahman Al-Saqafy- Al-Hussainy{R} littafin:
    An-Nafahaatul Anbiyaa’u fees-Salaati alaa Khairil
    bariyyat”
    > Imam sakhawi {R} littafin:
    Al-qaulul badeeah fis salaati alal
    Habeebi shafee’u” shafi 44-45.
    aciki zaku ga Hadithin:
    Sayyada Salamatul Kindiyy{R} itace wadda
    sayyidina Ali {R} ya fara koyawa “salatul fatih”
    Muhammad bin Abdulrahman bin Muhammad
    bin Abubakar Al Sakhaawiy Al Shafi’iy{ an haife shi
    a Sakhaa, Misra. 831 A.H ya rasu a 902 A.H} yace
    isnadin wannan salatin ya inganta har zuwa kan
    Annabi s.a.w.
    {{Al-qaulul badeeah: 45} >>1963<<
    Babban misali da zaku gane yan Izala yan jayayya
    ne kuma yan Iska.
    JAFARU KANO SALATIN SHI DABAN.
    KAREN GOMBE SALATINSHI DABAN
    GUMI YANA KARANTA SALATU TUNJINA.
    akwai casset din karen gobe mai taken. "An fake
    da guzuma aka harbi karsana"
    Ya bude taron da salati kamar haka:
    Allahumma salli alaa habibi qulubina wa shafi'ina
    wa kurratu a'ayunina wa maulana muhammad.
    A INA YA SAMO WANNAN SALATI??
    INA KUKA BAR SALATI IBRAMIYYA??
    Ku an lamunce maku kuyi wanda kuka ga dama
    amma banda mu ko?
    TO GASHI DAI KUN GANI SLATUL FATIH NA DA
    ASALI DAGA ASALIN MASU ASALI SAYYIDI ALI
    R.T.A
    SALATUL FAITIH NADA ASALI DAGA:
    Sayyidi Ali R.A
    Sayyidi Muhammadul Bakari {R.A}
    Qur'anul Kareem
    Hadithu shareef
    Shehu Tijjani R.A
    Shehu Ibrahim R.A
    Alhamdulillahi…………

  35. Mustapha Abdullahi Aliyu Avatar
    Mustapha Abdullahi Aliyu

    Aslw,ya kamata izala ta daina batawa kanta lokaci domin kowa a kasarnan yayi nisanda ba zasu iya riskarsa/su ba.Kuma duk abinda ku kaga mutane sunayi to kyalesu zai fi muku amfani.Don haka ku ringa neman hujja,idan an baku to kuyi shiru ko da kuwa kanbata

  36. Mustapha Abdullahi Aliyu Avatar
    Mustapha Abdullahi Aliyu

    Allah ya shiryemu.Ameen

  37. Dukkan Yabo da Godiya sun tabbata ga Allah SWT.
    Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Annabi (s) Alayensa da Sahabbansa baki daya.
    Maida Martani !
    Toh da farko dai ina mai naiman tsarin Allah da yakareni daga yin fasiqanci, ma’ani insha Allahu bazan yi irin taka ba. Saboda Sunnah ta karantar dani cewa: Zagin Musulmi fasiqanci ne.
    Kayi maganganu da dama. To amma ba zanci amanar ilimi ba, duk inda kayi dai-dai zan fada.
    Kayi kokarin kawo ma’anar kalmomin “SALAT” da kuma “FATH”. Na’am kayi kokari, ma’anar ta fito. Amma a inda gizo yake sakar shine: Ganin yadda idonka ya rufe, yasa kake ta zuba; ba kakkautawa kana tafin son ranka. Harma da fadin inkaga dama kace: kaza-kaza, toh dama addini da ganin dama ake aiwatar dashi ?. Ka fadan ! In kai addu’ar Allah ya baka wani abu(kamar yadda kace: Allah ka bani sa’a inci exam…), da kai wannan addu’ar lada kimanin nama Allah zaisa a rubuta ma ?, amma in kai Salatiwa Annabi (s) fa ? [1=10, 10=100, 100=1000…].
    Yiwa Annabi (s) salati umarnin wane ?_ALLAH SWT. Allah ya umarce ka da aikata wani al’amari ka kuma aiwatar, kayi mai cenan ?_Bauta ! Toh tayaya za’a bautawa Allah ?_Tahanyar da Annabinsa(s) ya koyar ! Allah ya umarci da ayiwa Annabi(s) salati. Annabi(s) kuma ya koyar da hanyar da za’a zartar. Shin da kake fadin a Sahabbai kanana ne suka tambayi yaya za’a yiwa Annabi(s) salati, mai yake tabbatar da haka ?. Mu daukama haka ne, kenan a amsar da Annabi(s) ya bayar yakebancewa su masu tambayar ne ? Ko kuwa Allah SWT su masu tambayar kadai yaba wa umarni ? Cayai: “….yaku wadanda sukai imani, kuyi salati da taslimi a gare shi[Annabi(s)].” toh mu dauka ace Sahabbai basu tambaye shi, ta yaya kai(Khalid) zaka yiwa Annabi(s) salatin ?_da abinda yazo tunanin ka ?. Wannan kenan ! Toh duk da cewa ba’a sa wani limit ba wajen addu’a. Mu dauka kowane irin salati mutum yai da ko wane irin lafazan da basu sabawa shari’a, kayi dai-dai kuma zaka samu lada(kuma hakan abin yake). Toh amma maye matsalar Salatul Fathi, in dai haka ne ?
    WADANNAN SUNE NUNA KUSKUREN Salatul Fathi:
    *Wahayinta akai,
    *Mala’ikane yakawo,
    *Wani mutum aka kawowa ba annabi, ba manzo ba,
    *Annabi da Sahabbai basu santa ba, basu taba yin taba.
    *Wai tana dai-dai da karanta Qurani sau 6000,
    *Bata da makarfafa Qurani ko Sunnah, kamar yadda Salatul Ibrahimiyya take dashi,
    *Masu yinta, sunfi fifitata akan Salatul Ibrahimiyya.
    Toh a bash ma a cewa Muhammadul Bakari ya roki Allah ya bashi irin salatin da yace ya roka, kuma Allah ya bashi. Shin toh a sanda mala’ikan ya kawo cayai dashi ya umarci alumma ko yayi ta ? Ya roka an bashi, sai yayi abinshi shi kadai. Wallahi kaima shaida ne kasani, kan aji dan Darika yayi Salatul Ibrahimiyya yayi Salatul Fathi yafi a irga. Mai wannan yake nunawa ? Ansamu wani yazo da wani al’amari cikin addini kuma jama’a sunkarba hannu 2-2, harma suna daukaka nashi fiye da wanda Annabi(s) ya koyar. Akwai hadisin da kasan shi na san shi. Annabi(s) yace: “Wanda duk yazo da wani al’amari (cikin al’amuran addini) wanda kuma (ya kasance) ba daga gare mu yake ba; toh (hakika wannan) abin mayarwa ne wa(mai shi). A inda a ruwayar Muslim kuma (wanda yazo da wani (amal) aiki….). Sannan kuma ya akai daraja da Salatul Fathi take dashi haryafi na Annabi ?
    Sabo da yanayin lokaci a nan zan da kata, amma ba dan na kare ba. Akwai batutuwa da dama a baki na. Toh amma dare yayi 11:21. Amma zan dawo in dora insha Allah.
    Wassalam !

  38. Cigaba….
    Maida Martani wa Khalid Yunusa.
    Kana maganan cewa ai wai Sayyadina Aliyu (RA) ya fara Salatul Fathi, toh mu dauka ma haka ne. Shin lokacin da Sayyadina Aliyu (RA) yake yin wannan Salati Annabi na raye ? Sa’anan shi Aliyu (RA) ya koyar da cewa wannan shine mafificin salati ? Kash ! Dake idanka ya rufe, ruwayar ma bata inganta ba, amma baka fahimci hakan ba. Dalili, a sananun masu rawaito hadisi (isnad) ba’asan Samalatul Kindiy ! Kuma ma ko da akace tace ! Ai ba aji tace Annabi(s) ya kasance yana koyarda mu ba, a’a sai dai tace Sayyadina Aliyu (RA) yake koyar dasu. Toh koma dai yaya ne malaman hadisi sun tabbatar da rashin ingancin hadisi, kuma ma salatin (ko addu’ar) ai tasha babban da Salatul Fathi illa bada lafiza biyu ka dai.
    Bari in kara komawa baya.
    Kace: wanda Allah ya bada Salatul Fathi ta hannunsa akan Tartibin da muke bi shine Muhammad Al-bakari(…).
    Toh anan akwai abubuwan duba, da kuma abin yake nuna tifka da warwara a maganarka. Kace Sayyadina Aliyu (RA [better than] Karamallahu wajahahhu) shi ya fara wannan salati, kuma kazo kace ga ta inda tabiyo ta hannun M. Bakari. Toh shikenan ! Haka ne tabbas bayan saukar ayar “Al yaumu akamaltu lakum dinikum..” an saukar da wasu ayoyin. Amma ka fadi cewa Annabi(s) yace: “la nabiya ba’adii” (babu wani annabi [da zaizo a] baya na). [Sahihayni]. Haka kuma babban malamin nan na fassarar Al-Qurani wato Ibn Abba(RA), wanda Annabi(s.a.w) ya dafa kansa yace: “ya Allah kasanar dashi Al-Qurani da fassararsa”, ya bada fahimtarsa game da Surah Al-Masad cewa conclusion na aikin annabatar Annabi(s) yazo karshe Allah SWT yake alarmtawa. Sa’anan a hajjin bankwana ;-( Annabi(s) yake tambayar Sahabbai cewa: “shin na isar da sako ?” sukace: “Na’am ka isar” Annabi(s) yace: “Toh Allah ka shaida ! Allah ka shaida !! Allah ka shaida !!!” kafin nan Annabi(s) ya rufe da cewa: “Zan tafi zan bar muku abubuwa biyu. Wadanda idan kunyi ruko dasu baza ku hallaka ba [sune] Littafin Allah [wato Qurani] da Sunnah ta”. Toh amma duk da wannan sai ga Bakari yazo da wani salati mafifici yace daga gun Allah ne, ya aiko mala’ika ya kawo, bayan shudaiwar kusan karni 10. Amma ko da Sahabbai da Tabi’ai basu samu darajar basu wannan salati(Salatul Fathi) ba sai Bakari, (wa iyyazu billahi minal dalala). Toh shikenan mu dauka ma haka ne. Kenan za’a iya samu wani annabi ko manzo bayan Annabi(s) ? Karka manta Annabi(s) ne yace babu wani annabi da zaizo bayansa da wani sako. Toh bama haka ba. Shin addinin ne bai cika ba; yasa Bakari yazo da wani al’amari ? Laisa kazalik ! Addinin Allah cikakke ne “al yaumu AKMALTU lakum dinukum…”. Kana ikirarin ko nuna cewa kai dalibin ilimi ne, kenan bakasan da wadannan gabobi ba ko ince ayoyi da hadisan ba ? Shin baka auna su da kuma abin da Bakari yazo dashi bisa mizani na ilimi da hankali da tunani ba ? Kaji tsoron Allah yakai Khalid Yunusa. Kasani Allah mai jine kuma mai ganine. Yasan duk abinda muke fada da aikatawa. Kasani mafi kyawun zance shine zancen Allah SWT, haka kuma mafi kyawun shiriya da koyarwa suna na Annabi (s.a.w), kuma mafi muni acikin al’amura shine kirkirar wani al’amari cikin al’amuran addini, yin hakan kwa ! bata ne, bata kuwa na shiryarwani izuwa wuta[Annabi(s) ne ya fada ba ni ba]. Allah ka shiryar damu tafarkin ka madai-daici, ka kuma kare mu daga azabar ka, nan duniya da lahira.
    Wassalam alaikum
    Shaikh Abubakar Gumi 🙁 (rahimahullah).
    Shaikh Kabiru Haruna Gombe 🙂 (allahuma zidhu imanan wa afiya).
    Shaikh Ja’afar Mahmud Adam Kano ;-( shahiidi (rahimahullah).
    Shaikh Muhammad Auwal Albani Zaria ;-( shahiidi (rahimahullah).
    Shaikh Balalau Kano :-)(allahumma zidhu imanan wa taufiqan).
    O Allah protect your ulama’a as-salihuun.

  39. Adamu Maijama'a Katagum Avatar
    Adamu Maijama’a Katagum

    Malam Bilal Sambo Allah ya saka da alkairi, wallahi malaman izala kuna cutar mabiyanku domin bakwa fada musu gaskiyar lamarin addini. Duk abinda kuka nuna musu bakyau ko bidi’a ne bakwa kawo hujja inda annabi ya hana. Idan duk abinda annabi baiyi bane bidi’a ai ba salatil fatih bane kawai, ita kanta izala ai annabi baiyi ba haka sahabbai, tabi’ai da tabi’ittabieen. Me yasa duk abinda ‘yan izala bakwa yine kadai bidi’a? Shin gasar karatun Qur’ni, Lunching, Wa’azin kasa,jiha da local government, makarantar matan aure da sauransu duk annabi baiyi ba. Kuma duk ba wanda yace muku ‘yan bidi’a, sai maulud da salatil fatih ne kadai bidi’a? saboda sun danganci annabi ko? ya tabbata bakwa kaunar annabi.

    1. Musa Avatar

      Khaji Jahili Izala Kalmar Kawarwa Ne Idan Baka Sani Ba Bari Na Fassara Maka A Kawar Da Bidi,ah A Tsayar Da Sunnah Shine Ma,anan Wawa Tafki Kawai

  40. Basiru Abdullahi Avatar

    MARTANI GA YUNUS KHALID
    بسم الله الرحمن الر حىم
    اللهم صل على سيدنامحمدالفاتح لما أغلق و‎ ‎الخاتم لما‎ ‎سبق ناصرالحق بالحق والهادى الى صراطك المستقيم و على اله حق قدره و مقداره العظيم*
    الحمدلله*
    Alhamdulillah ! Alhamdulillah !! Alhamdulillah !!! Da Allah yasa muka buɗa ido muka ga kanmu masoyan Shehu Tijjani mabiya Shehi Tijjani Yan Ɗariqar Shehi Tijjani (ar) Allah badan aikinmu ba dan ibadarmu ba Allah dan albarkachin Shehi Ahmad Tijjani jikkan Annabi Muhammadu (s.a.w) kabamu sibati cikin ɗariqar Shehi Ahmad Tijjani (as) kakar ɓemu cikin Ɗariqar Shehi Ahmad Tijjani (ra) kata shemu cikin ɗariqar Shehu Ahmad Tijjani ya Allah Albarkachin Shehu Ahmad Tijjani Allah kaimana haka dan sirrin da ke tsakaninka da Shi * Alhamdulillah malam mai sukar Salatil Fatihi da wadansu suka to kasani cewa gaba ɗaya Salatil Fatiha wallahi ba inda sunan S, Tijjani ko ɗaya, sai dai sunan Manzon Allah (s.a.w) wanda akai salatin dan shi to in dai addur Salatil fathi ce SHEHI AHMAD TIJJANI dan yafadi wasu kaɗan daga asararan shine kuke yaɗama Duniya to wallahi summa wallahi tallahi duk abin Maulanmu Shehi Ahamad Tijjani yafaɗa to wallahi tallahi summa tallahi billalhillazi la iha illahu munyi imani kamar yanda Sayyidina Abubakar (ra) yagasga mushiriki yayinda ya kawo masa tsegumin Shugaba (s.a.w) sai Sayyidina Abubukar yagasga tashi to muma wallahi mun gasgata Shehinmu Ahma Tijjani duk abinda yafa walau a littafinn shi Shehunnan mune koko a jauwa’hirilma’ani to wallahi mun yarda ciki taslimi *

  41. Ina rokon ALLAH SWA yatsareni dafadawa cikin wannan aqida shirka dakuma yin gagganci izuwa wurin ALLAH SWA.kuma ina rokon ALLAH SWA yatsare muna Malaman mu na Sunnah Ameen

  42. Hakika salatul fathih salati ne na annabi saw domin gaba dayanta an tsintotane daga cikin alqur’ani mai tsarki.

  43. Gaskiyane yan Izala basu fahimci su jahilai bane kuma bazasu fahimci hakaba, har abada, kuma wannan maganar ina yintane,badon inkare wancan dan iskanba dayace yana bautawa shehu, A’A, nima ina tareda buk wanda yake masa kallon lafiri, to amma, ina fadin hakane domin, Allah yace:”WALA TAKFU MA LAISA LAKA BIHI ILMUN” &> “FAS’ALU AHLAZZIKRI IN KUNTUM LA TA’ALAMUNA”, don me yan izala bazasu rika zuwa wajen sufaye su dinga tambayar abinda basu saniba kuma yashige musu duhu a littafan darikaba? nabada misalin mutumin dazai siyo littafin fida=tiyata, na likitoci kuma yace tunda yazama dakta a turanci, bari yakaranta yagane sai yafara fede mutane, wannan=sai yafara kashe mutane kamar yadda ku yan izala kuke yanzu, MANZON ALLAH YACE: MIN HUNUL ISLAMIL MAR’I TARKUHU MALA YAANIHI, kaiba dan darikaba, bakuma ace dole kayiba, kuma kayi wa’azi wa mutane kace bakyau, to ai kai kafita a wajen Allah, saura yarage namu mu sufaye, tunda Annabin Allah ma ance dashi:”LAISA ALAIKA HUDAHUM” & “LASTA ALAIHIM BI MUSAIDIR”.P.T.O.

  44. So karatu Avatar
    So karatu

    Ilmin ka ya zama na na banza. Ka zama khawariji mai jayayya da hadisan da suka yi magana akan mubashshirat. Har kana cewa wai babu wahayi? To su mubashshirat din minene? Kai lalle ka yi asara. Duk wannan ilmin naka amma ya zama na banza?

  45. Saminu Avatar
    Saminu

    Cab yaro kakoma makaranta agane waye Allah waye Manzon Allah kajiko+

  46. Naseer Avatar

    Inaso kafada mana irin mutuwar DA Gomi yayi wawa

  47. Naseer Avatar

    Kafada mana irin mutuwar da sheik Gum yayi Allah. Sarki

Leave a Reply to AbdoulkarimCancel reply

Latest updates
Categories