Sharudan umarni da kyakkyawa da hani da mummuna

Danna nan domin shiga karatu Online

Umarni da kyakkyawa da hani da mummunan aiki yana daga cikin Ibada mai ɗinbin lada a Addinin Musulunci. Kuma Allah yana son masu umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Kamar yadda yake ƙin wa’inda Basu yin wannan aiki.

ƙin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna yasa Allah subhanahu wata’ala ya tsine wa Bani Isra’ila. Allah ya bada labari a Al’Qur’ani mai girma yace:

(لُعِنَ ٱلَّذِینَ كَفَرُوا۟ مِنۢ بَنِیۤ إِسۡرَ ٰ⁠ۤءِیلَ عَلَىٰ لِسَانِ دَاوُۥدَ وَعِیسَى ٱبۡنِ مَرۡیَمَۚ ذَ ٰ⁠لِكَ بِمَا عَصَوا۟ وَّكَانُوا۟ یَعۡتَدُونَ)
[Surat Al-Ma’idah 78]

(كَانُوا۟ لَا یَتَنَاهَوۡنَ عَن مُّنكَرࣲ فَعَلُوهُۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُوا۟ یَفۡعَلُونَ)
[Surat Al-Ma’idah 79]

An tsine wa kafirai daga banu Isra’ila a harcen Annabi dawood da Isa ɗan Maryam. Sabida tsaɓawa Allah da ta’addanci da sukeyi

Sun kasance basu hana junansu kan mummunan aiki da suke aikata wa. Tir da wannan mummunan aiki da sukeyi na ƙin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.

Wannan yake nuna maka munin wannan laifi. Dole musulmi in yaga abinda bashi da kyau yayi inkarinsa.

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

من رأى منكم منكرًا فليغيرْه بيدِه ، فإن لم يستطعْ فبلسانِه ، فإن لم يستطعْ فبقلبِه ، وليس وراءَ ذلك من الإيمانِ مثقالُ ذرةٍ

Muslim

Wanda yaga wani abin ƙi to ya canza shi da hanunsa( idan yana da hukunci a hanunsa) idan bazai iya ba toh ya canza shi da harcensa( wurin faɗakar wa da wa’azi da tsawatar wa) idan ba zai iya ba toh yaƙi wannan munkarin acikin zuciyarsa. Babu wani imani ko da kwatankwacin kwayan zarra ne bayan haka( Ma’ana wanda zaiga munkari amma ko azuciyarsa bazaiji baya ƙinta ba toh bashi da Imani

Meye sharuɗan Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna?

  1. Mai umarni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna dole ne yasan abinda yake umarni dashi ko kuma hani dashi. Dole ya zamto yana da ilimi kan abinda yake umarni ko hani akai, sabida kada yaje yayi hani kan abinda yake da kyau, ko kuma yaje yayi umarni da abinda yake bashi da kyau. Allah maɗaukakin sarki yace: “Kada ka tsoma bakin ka kan abinda baka da ilimi akai” Suratul-Isra: 36. Sabida haka ba’a umarni da kyakkyawa ko hani da mummuna bisa jahilci ko son zuciya. Ana maida lamarin ne zuwa ga Allah subhanahu wata’ala.
  2. Ya zamto yana da sani kan cewa wanda yakeso ya umarta ko yayi masa hani ɗin ya aikata abin hani ko kuma yaƙi aikata abinda yakeso ya umarceshi dashi. Kamar kaga mutum kawai kace masa ya tashi yaje yayi sallah bayan bakasan yayi ko baiyi ba, ko kuma kaga wani da wata acikin mota suna zaune sai kawai kaje ka fara masa wa’azi bayan baka san meye matsayin ta awurinsa ba. Ko matarsa ce ko wata muharramansa. Sabida haka dole ka lura da halin wanda kakeso kayi kira ko hani gareshi.
  3. Kada ya zamto hani da mummunan zai janyo afkawa zuwa ga wanda yafishi muni. Wannan yana da buƙatar lura sosai. Kaman mutum ne ka ganshi yana shan sigari, kuma kana da tabbacin inka hana shi shan wannan sigarin toh zai koma shan giya. Toh anan sai ka barshi kan wannan munkari da yake kai, sabida yafi sauƙi akan wanda zai koma idan aka hanashi wannan. Shiyasa Allah maɗaukakin sarki ya hana zagin Allolin Kafirai. Duk da cewa wannan Allolin basu da amfani kuma sun cancanci zagi. Amma Allah ya hana a zagesu sabida hakan zai jawo su zagi Allah. Toh kaga garin inkarin munkari an janyo wani munkari wanda ya fishi.

An rawaito Cewa: wata rana Sheikhul Islam ibn Taimiyyah yana tafiya shi da wani acikin Sham. Sai suka haɗu da wasu mutane daga cikin Tatar(tatar wasu mutane ne wa’inda suka yi ta kashe al’ummar Musulmi a lokacin sukayi ta ta’addanci a bayan ƙasa) sai Sheikhul islam suka ga wa’innan mutane suna shan giya sai Sheikhul Islam baice musu komai ba ya wuce abinsa, sai Wannan abokin tafiya nashi yace: meyasa baka hanasu wannan aiki da sukeyi ba? Sai Sheikhul Islam yace: idan muka hanasu shan wannan giya toh tafiya zasuyi zuwa ga matayen musulmi suna zina dasu. Suna kwashe dukiyar su. Wataƙila ma su kashe su. Shan giya shi yafi sauƙi. Ku dubi irin wannan fiqhu na Sheikhul Islam! Shiyasa dole sai ka lura sosai. Kada kaje garin yin hani da mummuna kaje ka janyo wanda yafi shi. Allah yasa mudace.

Wannan sune sharuɗan Amru bil ma’aruf da kuma nahyu anil munkar.

an rawaito daga Annabi yana cewa:

والذي نفسي بيدِه لتَأمرُنَّ بالمعروفِ ولتَنهوُنَّ عن المنكرِ أوليُوشِكَنَّ اللهُ أن يَبعثَ عليكمْ عقابًا منهُ فتدعونهُ فلا يَستجيبُ لكمْ

Attirmithi: 2169

Ina rantsuwa da wanda rai na ke hannunsa ko ku rinƙa umarni da kyakkyawa ku rinƙa hani ga mummuna ko kuma Allah ya kusa ya turo muku wata uƙuba daga gareshi ku yi ta addu’a yaƙi amsa wa

Wannan hadisi yana nuna mana haɗarin yin shiru game da ɓarna. Musulmi a duk lokacin da ya ga ɓarna dole ne yayi inkarinsa. Ko da hanu ko da baki ko da zuciya. Allah yasa mudace. Ya kuma sanya mu cikin masu umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates