Shin taɓa gaba yana warware alwala?

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Tambaya: Shin idan na miji ta taɓa Azzakarin sa ko mace ta taɓa farjin ta sai sun sake alwala? Misali kaman mutum ya kammala wankan janaba sai ya taɓa Azzakarin sa sai ya sake yin alwala kafin yayi Sallah?

Amsa: Tambaya ta farko game da na miji idan ya taɓa Azzakarin sa ba tare da shamaki ba akwai zance biyu wanda suka fi ƙarfi na Maluma.

Na farko: idan na miji ya taɓa Azzakarin sa ba tare da shamaki ba to alwalan sa ya karye sai ya sabunta alwala.

Wannan Shine Mazhabar Malikiyya da Shafi’iyya da Hanabila.

Dalilan su: sun kafa Hujja da Hadisin da aka rawaito daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Wanda ya shafi Azzakarin sa to yayi alwala

Abu dawud: 181. Tirmidhi: 83

Sannan sukace lokacin da mutum ya shafi azzakarin sa sha’awar sa zata iya motsawa wataƙila wani abu ya fito masa ba tare da ya sani ba.

Sharhul Mumti’ Na Ibn Uthaymeen: 1/280

Zance na biyu: idan mutum ya shafi Azzakarin sa ba tare da Shamaki ba to alwalarsa bata karye ba.

Wannan shine mazhabar Hanafiyya, da wasu daga cikin Ƴan Malikiyya Da wasu daga cikin Magabata. Hakanan wannan shine Ra’ayin Sheikhul Islami Ibnu Taimiyya da Sheikh Ibnu Uthaymeen

Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya yace:

Abinda yafi bayyana shine Shafan Azzakari baya warare alwala, sai dai mustahabbi ne wanda ya shafi azzakarin sa ya sabunta alwala, amma wanda yayi sallah bai sabunta alwala ba Sallarsa tayi amma idan ya sabunta to hakan shi yafi.

Majmu’u Fatawa: 21/222

Dalilan wa’inda sukace Shafan Azzakari baya warware alwala Shine Hadisin da aka rawaito daga ɗalk bin Ali Allah ya ƙara masa yarda yace:

Munje wurin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi mukayi masa mubaya’a, mukayi Sallah tare dashi. Lokacin da ya kammala sallah sai wani mutum yazo kaman mutumin ƙauye sai yace ya Manzon Allah me kake gani game da Mutumin da ya shafi Azzakarin sa a Sallah? Sai Annabi yace masa Shin Azzakarin ka mene ne in ba Wani ɓangare ne na jikin ka ba?

Abu dawud: 182. Annasa’i: 165

Wannan Hadisi yana nuna cewa idan Mutum ya shafi Azzakarin sa da hannunsa to alwalar sa bai karye ba, domin Azzakarin sa kaman sauran gaɓɓan jikinsa ne. Kamar yadda Annabi yayi bayani a wannan hadisi.

Wurin haɗa wannan hadisi da wanda ya gabace shi wasu Maluman sun ɗauki umarni da Annabi yayi kan sabunta Alwala idan mutum ya shafi azzakarin sa a matsayin Mustahabbi ne ba wajibi ba saboda wannan hadisi na ƙarshe. Wasu kuma sun banbance tsaƙanin shafan Azzakarin, idan mutum ya shafa da Sha’awa to zai sake alwala idan kuma bai shafa da sha’awa ba, ba sai ya sake alwala ba.

Wannan Hukunci da muka ambata ya shafi Ramin dubura. Duka Hukuncin su ɗaya.

A taƙaice abinda wannan Amsa ya ƙunsa shine: Wanda ya shafi Azzakarin sa Da sha’awa To ya sake alwala, wanda kuma ya shafa ba da sha’awa ba to yana da kyau ya sake alwala. Idan kuma mutum ya shafi Azzakarin sa kuma akwai shamaki kaman ya shafa akan saman wandon sa to babu komai a kansa.

Tambaya ta biyu: Hukuncin wadda ta shafi farjin ta, shin alwalar ta ya karye?

Shima duka Hukuncin sa kaman na Farko.

Allah shine mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories