Sunnanta Sunnah mai kyau da kuma mara kyau

Danna nan domin shiga karatu Online

An rawaito daga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace:

مَن سَنَّ في الإسْلَامِ سُنَّةً حَسَنَةً، فَعُمِلَ بهَا بَعْدَهُ، كُتِبَ له مِثْلُ أَجْرِ مَن عَمِلَ بهَا، وَلَا يَنْقُصُ مِن أُجُورِهِمْ شيءٌ، وَمَن سَنَّ في الإسْلَامِ سُنَّةً سَيِّئَةً، فَعُمِلَ بهَا بَعْدَهُ، كُتِبَ عليه مِثْلُ وِزْرِ مَن عَمِلَ بهَا، وَلَا يَنْقُصُ مِن أَوْزَارِهِمْ شيءٌ

Muslim 1017

Wannan hadisi annabi ya faɗeshi ne lokacin da wasu mutane sukazo wurinsa wanda da yawa daga cikinsu ko dukansu ƴan Ƙabilar Mudar ne. Sukazo a yanayi na talauci da wahala, Hankalin Manzon Allah ya tashi. Ya shiga gida ya fito ya umarci Bilal yayi kiran Sallah, sannan yayi Sallah sai ya tashi yayi huɗubah wa Sahabbansa kan taimako da bada sadaqa. Aka samu Sahabbai da yawa kowa ya kawo abinda zai iya har aka tara abinci da tufafi masu yawa. Manzon Allah yayi farin ciki da ganin wannan ƙoƙari na sahabbansa wurin taimakawa. Wanda zai taimaka wurin fitar da wa’innan mutane daga cikin halin da suke ciki. Shine sai Annabi yace:

Wanda ya sunnanta sunnah mai kyau acikin Addinin Musulunci toh yana da ladan wannan Sunnah, da kuma ladar wa’inda sukayi aiki dashi, ba tare da an rage lada daga cikin ladansu ba, haka nan wanda ya sunnanta wata sunnah mummuna a Addinin Musulunci toh yana da laifinta, da kuma laifin wa’inda sukayi aiki da ita ba za’a rage musu wani abu daga cikin laifinsu ba.

Abinda ake nufi da sunnah anan shine mutum ya fara aikata wani abu da Allah ko Annabi sukayi umarni dashi. Sai mutane su gani suyi koyi dashi

Ko kuma wata sunnah ce ta Annabi amma sai aka mance da ita akayi watsi da ita, sai wani yazo ya raya ta. Kamar yadda Umar Radiyallahu anhu ya raya sunnar yin sallar tahajjud a masallaci da liman. Dama sunnah ce ta Annabi, amma ya bar amfani da ita ne sabida gudun kada a wajabta ta kan Al’ummah. Bayansa kuma sai Umar ya dawo da ita. Toh wanda ya raya sunnar da aka bar amfani da ita shima ya sunnanta Sunnah mai kyau. Ba wai ana nufin cewa mutum ya ƙirƙire wani abinda baya addini ya kawoshi ya saka a addini ba. Domin shi kanshi dalilin faɗin annabi wannan magana yana daɗa nuni da fassarar da mukayi ta farko. Domin dama sadaqa ai abu ne wanda Al-Qur’ani yayi umarni dashi. Kuma Annabi yayi umarni dashi

Toh duk wanda ya sunnanta sunnah mai kyau, haka ladan zaiyi ta binsa har ranar tashin Qiyaama. Haka nan wanda ya sunnanta wata sunnah mummuna. Haka zunubi zaiyi ta binshi har zuwa ranar tashin Al-Qiyaama. Misali wanda zai ƙirƙiri wata Bid’ah ya sanya ta a Addini. Ko kuma wanda zai ƙirƙiri wani kalan laifi ya yaɗa Al’ummah su rinƙa amfani da ita.

Sabida haka ya dace mutum ya rinƙa lura da ayyukansa. Kada ya yadda ya kira mutane zuwa ga Abu mara kyau, domin zunubin ba zai tsaya anan ba. Duk zunubansu shima yana da commission aciki. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates