Menene Tahiyyatul Masjid? Kuma meye Hukuncin ta?
Tahiyyatul Masjid itace raka’oi biyu da Mutum zaiyi da zarar ya Shiga Masallaci kafin ya zauna.
Hukuncin ta: Sunnah ce
Dalili: an rawaito daga Abu Qatada Allah ya ƙara masa yarda yace:
Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: idan ɗaya daga cikin ku ya shiga Masallaci kada ya zauna har sai yayi Sallah raka’a biyu
Bukhari: 930. Muslim: 875
Haka nan an sake rawaito wa Jabir Allah ya ƙara masa yarda yace
Sulaik Algaɗfani ya shigo masallaci Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana huɗuba sai ya zauna sai Annabi yace masa ka tashi kayi raka’a biyu amma ka taƙaita.
Bukhari: 930. Muslim: 875
Wannan yake nuna a kowani lokaci mutum ya shiga Masallaci zaiyi wannan raka’a guda biyu koda ranar Juma’a ne Limami yana huɗuba.
Sannan Tahiyyatul Masjid tana faɗuwa idan mutum ya shigo masallaci ya samu ana sallah, ko ana gab da a fara sallah kuma lokaci bazai bashi dama yayi rakao’in biyu ba.
Tahiyyatul Masjid a Masallaci mai alfarma:
Idan mutum yaje Ka’aba da nufin yin ɗawafi to wannan ɗawafin ya maye gurbin Tahiyyatul Masjid, amma idan yaje domin sallah ne ko karatu ko wani abu to hukuncin sa ɗaya da sauran masallatai zaiyi wa’innan raka’oi guda biyu
Leave a Reply