TARBIYYAH TA MUSULUNCI

Danna nan domin shiga karatu Online

بسم الله الرحمان الرحيم.
DAYAWA DAGA CIKIN MATA SUN HALAKA!
DAYAWA DAGA CIKIN MATA SUN ZAMA ‘YAN WUTA.
DAYAWA DAGA CIKIN IYAYE SUN HALAKA!
DA YAWA DAGA CIKI MAZAJE SUN HALAKA!
Allah ka tsaremu.
Da Farko Ya tabbata cikin hadisin manzon Allah(s.a.w) yace:
سيكون في آخر الزمان نساء كاسيات عاريات، إلعنو هن فإنهم ملؤونات، والله لا يجدن ريح الجنة وإن ريححا لتوجد من مسيرت كذا وكذا.
Manzon Allah yace: ‘a karshen zamani za’a samu wasu mata wanda suke sanya tufafi amma suna tafiya tsirara. Ku tsinemusu domin su din tsinannu ne, wallahi ba zasuji ko kamshin aljannah ba, kuma ita kamshin Aljannah ana jintane daga tafiyar wuri kaza zuwa wuri kaza..muslim 2127. A wannan ruwayar kenan.
صحيح مسلم، ألباس والزينة، باب نساء كاسيات عاريات المائلات المميلات رقم(٢١٢٨ )
A karkashin wanna hadisi ibn abdul barri. Yace tufafin nasu bata rufe jikinsu ba.
‘yan’uwa musulmai wannan ta zama wajibi a garemu mu tashi muyi iya kokarinmu wajen kare iyalanmu zuwa fada wa raamin halaka. Shin ‘yar’uwa musulma meye abin burgewa a wurinki kin fita kina nuna wani sashi na jikinki a waje kin zama tsinanniya?
Duk wata mace da ta sanya kaya ya matse jikinta tana rangwadi akan hanya wannan ‘yar wuta ce, haka annabi ya fada.
Abin ban haushi sai kaga ‘yan mata suna hawa kan shafuka ta facebook ko wasu dabam suna sanya hotunansu wanda kuma acikin hotunan zaka ga suna nuna tsiraicinsu. Toh kusani wannan abinda kukeyi tsabawa Allah ne, kuma wallahi babu abinda zai jawo muku sai bakin jini da zubar mutunci agun duk wani mutumin kirki!
Yaaa ku ‘yan mata da matan aure masu sanya hotunansu a facebook, ko wasu shafuka na internet kuna dariya ko kuna nuna tsiraicinku, wallahi baku burge kowa sai ‘yan iska. Babu mai sauraronku sai ‘yan iska. Kuma annabi yace ku tsinannu ne ku tuba kada daga karshe kuzo kuna nadaama ….
Yau kashiga jami’o’inmu kasha mamaki. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Zakaga ‘yar musulma ka kasa ganeta. Tayi shiga irin ta arna. A haka annabi zaiyi alfahari damu?
Meye Amfanin makarantar da zai kaiki ga halaka? Boko hauka ne?
Sannan yau a arewacin kasannan kashiga kaga inda yara mata suke fita talle… Kaga inda ake zinace zinace dasu, kaga yarinya musulma amma tana dauke da cikin arne iyamuri. Shin iyaye nawa zaku samu a tallen? Shin kun zabi duniya akan lahira? Kuna nufin Allah bazai tambayeku ba?
Sanan ku duba inda zinaace zinaace yayi yawa tsakaanin al’ummah ayau.
Shin kanaso ka auri mazinaciya ko ke kinaso ki auri mazinaci?
Allah yace.
ﭐﻟﺰﺍﻧﻰ ﻟﺎ ﻳﻨﻜﺢ ﺇﻟﺎ ﺯﺍﻧﻴﺔ ﺃﻭ ﻣﺸﺮﻛﺔ ﻭﭐﻟﺰﺍﻧﻴﺔ ﻟﺎ
ﻳﻨﻜﺤﻬﺎ ﺇﻟﺎ ﺯﺍﻥ ﺃﻭ ﻣﺸﺮﻙ ﻭﺣﺮﻡ ﺫﻟﻚ ﻋﻠﻰ
ﭐﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ.
Mazinaci baya auren kowa sai mazinaciya, haka itama mazinaciya bata auren kowa sai mazinaci, Allah ya haramta haka ga musulmai….
Yaaa ku mazinata ku tuba.
Maganata ta karshe ‘yan mata ku sani ba kowa bane Allah ya baku daman ku nuna mishi adonku… Inkun tabbata ku muminai ne ku tuba ku ciccire hotunanku akan facebook. Ga iya mutanen da Allah ya baku daman ku nuna musu adonku… Allah yace..
ﻭﻗﻞ ﻟﻠﻤﺆﻣﻨﺖ ﻳﻐﻀﻀﻦ ﻣﻦ ﺃﺑﺼﺮﻫﻦ ﻭﻳﺤﻔﻈﻦ
ﻓﺮﻭﺟﻬﻦ ﻭﻟﺎ ﻳﺒﺪﻳﻦ ﺯﻳﻨﺘﻬﻦ ﺇﻟﺎ ﻣﺎ ﻇﻬﺮ ﻣﻨﻬﺎ
ﻭﻟﻴﻀﺮﺑﻦ ﺑﺨﻤﺮﻫﻦ ﻋﻠﻰ ﺟﻴﻮﺑﻬﻦ ﻭﻟﺎ ﻳﺒﺪﻳﻦ
ﺯﻳﻨﺘﻬﻦ ﺇﻟﺎ ﻟﺒﻌﻮﻟﺘﻬﻦ ﺃﻭ ﺀﺍﺑﺎﺋﻬﻦ ﺃﻭ ﺀﺍﺑﺎﺀ
ﺑﻌﻮﻟﺘﻬﻦ ﺃﻭ ﺃﺑﻨﺎﺋﻬﻦ ﺃﻭ ﺃﺑﻨﺎﺀ ﺑﻌﻮﻟﺘﻬﻦ ﺃﻭ ﺇﺧﻮﻧﻬﻦ
ﺃﻭ ﺑﻨﻰ ﺇﺧﻮﻧﻬﻦ ﺃﻭ ﺑﻨﻰ ﺃﺧﻮﺗﻬﻦ ﺃﻭ ﻧﺴﺎﺋﻬﻦ ﺃﻭ ﻣﺎ
ﻣﻠﻜﺖ ﺃﻳﻤﻨﻬﻦ ﺃﻭ ﭐﻟﺘﺒﻌﻴﻦ ﻏﻴﺮ ﺃﻭﻟﻰ ﭐﻟﺈﺭﺑﺔ ﻣﻦ
ﭐﻟﺮﺟﺎﻝ ﺃﻭ ﭐﻟﻄﻔﻞ ﭐﻟﺬﻳﻦ ﻟﻢ ﻳﻈﻬﺮﻭﺍ ﻋﻠﻰ ﻋﻮﺭﺕ
ﭐﻟﻨﺴﺎﺀ ﻭﻟﺎ ﻳﻀﺮﺑﻦ ﺑﺄﺭﺟﻠﻬﻦ ﻟﻴﻌﻠﻢ ﻣﺎ ﻳﺨﻔﻴﻦ ﻣﻦ
ﺯﻳﻨﺘﻬﻦ ﻭﺗﻮﺑﻮﺍ ﺇﻟﻰ ﭐﻟﻠﻪ ﺟﻤﻴﻌﺎ ﺃﻳﻪ ﭐﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥ
ﻟﻌﻠﻜﻢ ﺗﻔﻠﺤﻮﻥ.
Kuma ka ce wa mũminai mãta
su runtse daga gannansu,
kuma su tsare farjõjinsu kuma
kada su bayyana ƙawarsu fãce
abin da ya bayyana daga gare
ta, kuma su dõka da mayãfansu
a kan wuyan rigunansu, kuma
kada su nũna ƙawarsu fãce ga
mazansu ko ubanninsu ko
ubannin mazansu, ko ɗiyansu,
ko ɗiyan mazansu, ko ´yan
´uwansu, ko ɗiyan ´yan´uwansu
mãtã, kõ mãtan(2) ƙungiyarsu,
ko abin da hannãyensu na
dãma suka mallaka, ko mabiya
wasun mãsu bukãtar mãta daga
maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su
tsinkãya a kan al´aurar mãtã.
Kuma kada su yi dũka da
ƙafãfunsu dõmin a san abin da
suke ɓõyħwa daga
ƙawarsu.Kuma ku tũba zuwa ga
Allah gabã ɗaya, yã ku
mũminai! Tsammãninku, ku
sãmi babban rabo…
Toh wannan ka’idar zamubi mu zauna lafiya, duk mai halin hana barna ya hana. Duk wata mace mai kaunar Allah da manzonsa, da kuma son Shiga rahamar Allah, ta cire duk hotunansu da basu dace ba, sannan su fadakar da ‘yan’uwansu su daina. Haka masu yawo da sutura wadda bata rufe jiki su daina, Domin mu gudu tare mu tsira tare. Allah yasa mudace!!!

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

4 responses to “TARBIYYAH TA MUSULUNCI”
 1. Tasiu Haruna Avatar
  Tasiu Haruna

  Allah (S.W. A) ya saka da alkhairi ya kuma sa mu gyara halayan mu. Ameen

 2. Muhammad Avatar

  The peace upon you:-)agaskiya naji dadi wanan fadakarwa taka malam, allah yasa maka da alkairi.amin,yaaa ku yan uwana maza da mãtã, gyara kayanfah bai zama sauke mureba ba!!don haka muyi kokari mu gyara,don kuwa su malai suna matikar kokarinsu na ganin mun gane gaskiya,mun gujema tsari ko dabi’a irin ta turawa,wasalam allah yasa mu dace!!!

 3. Salman umar inuwa Avatar
  Salman umar inuwa

  Allah ka datar damu.

 4. Abubakar Auwal Kwalam Avatar
  Abubakar Auwal Kwalam

  jazakallahu khairan

Leave a Reply

Categories
Latest updates