Tarihin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Fitowa ta 7: Auren Manzon Allah da Khadijah da kuma tafiyar sa zuwa sham karo na biyu

Danna nan domin shiga karatu Online

Shekara kafin Hijira: 28

Shekarar Miladiyya: 595


An samu tsaɓani wurin tabbatar da shekarun Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kuma na Khadijah Radiyallahu Anha lokacin aurensu.

wasu sukace Manzon Allah ya aure ta lokacin yana da shekaru ashirin da biyar, wasu kuma suka ce ashirin da bakwai, wasu kuma suka ce talatin. Wasu sun faɗa wasu shekarun ba wannan ba.

Ita ma Khadijah wasu sunce a lokacin shekarun ta talatin da biyar wasu kuma suka ce Arba’in.

Khadijah Allah ya ƙara mata yarda ita ta nemi auren Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Haka ya faru ne lokacin da ta samu labarin Amanar sa da kuma halayensa kyawawa.

An rawaito cewa:

Ƴar’uwan Khadijah tayi jinga da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da abokin tafiyarsa, Lokacin da suka ƙare tafiyar. Sai ya zamto akwai wani daga cikin ladan aikinsu da ya rage a wurinta. Sai wannan abokin tafiyar na Manzon Allah yayi ta zuwa wurin Manzon Allah yana neman suje su karɓo wannan haƙƙi nasu. Sai Manzon Allah yace masa yaje shi yana jin kunya. Bayan da wannan abokin tafiyar na Manzon Allah yaje wurinta sai ta tambaye shi ina Muhammad? Meyasa bai zo tare dakai ba? Sai yace nace masa yazo mu tafi, sai yace yana jin kunya.

Bayan da wannan ƴar’uwa ta Khadijah ta dawo gida sai ta zanta wa Nana Khadijah labarin Manzon Allah da abinda ya faru. Tace: Ban taɓa ganin mutum mai kunya da kamewa ba irin Muhammadu.

Sai Khadijah taji tana sonshi. Sai ta tura a kirawo shi. Da yazo sai ta faɗa masa cewa tana so ya aure ta. Ta kuma ce masa yaje ya sami mahaifinta suyi magana.

Sai Manzon Allah yace: babanki mutum ne mai dukiya bazai amince ya aurar dake gareni ba. Sai tace: kaje ka masa magana sannan kabar komai a hanuna.

Haka akayi. Manzon Allah yaje. Kuma aka samu dacewa.

Manzon Allah ya aure ta tana Bazawara.


A wata riwaya wanda zamu kawo a ƙasa akwai ɗan banbanci da wacce ta gabata.

Tafiyar Manzon Allah zuwa ƙasar Sham karo na biyu

lokacin da Manzon Allah yakai shekara ashirin da biyar a Rayuwarsa. A lokacin ya shahara da suna da ake masa laƙabi dashi Al-Amin(Mai aminci). Sabida aminci da riƙon amanar sa. Sai baffansa Abu ɗalib ya nemeshi da yayi safara zuwa sham domin ya samo musu dukiya da zasu cigaba da gudanar da rayuwarsu na yau da kullum. Domin a lokacin Abu ɗalib ya kasance bashi da dukiya, sai ya nemi Annabi da yabi ayarin ƴan kasuwa da suke zuwa Ƙasar sham domin kasuwanci. Ya kuma nemeshi da yaje wurin Nana Khadijah ta bashi dukiyar da zaije yayi kasuwanci dashi. Dama ta kasance takan tura mutane zuwa Sham domin yi mata kasuwanci da dukiyarta sai su raba ribar. Abu ɗalib ya kasance baya son Manzon Allah ya tafi zuwa sham saboda yana masa tsoron kada yahudawa su cutar dashi. Amma da yake bashi da wata hanya, kuma bashi da wata mafita sai wannan sai ya umarci Manzon Allah da yayi wannan tafiyar.

Manzon Allah yaje wurin nana Khadijah. Ta haɗa shi da wani yaronta mai mata hidima sunansa Maisara domin suyi wannan tafiyar zuwa sham tare da ayarin ƴan kasuwan Quraishu.

Dama kafin yazo wurinta tana da labarin gaskiyar sa da riƙon Amanar sa.

lokacin da suka isa Kasuwar Busra sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yaje ƙarƙashin wani bishiya domin ya huta. Kusa dashi akwai wani wurin bautar wani malamin Kirista. Sai wannan Malamin kiristan ya fito yaga Maisara daman ya sanshi. Sai ya tambaye shi. Ya kai Maisara wanene wannan da ya sauƙa ƙarƙashin wannan bishiya?

Sai yace wani ne daga cikin Quraishawa, daga cikin Mutanen Harami. Sai wannan Fadan yace: Babu mai sauƙa a ƙarƙashin wannan bishiya sai Annabi.

Manzon Allah yaje ya siyar da kayan da yazo dashi. Kuma ya siyo abubuwan da yake buƙata na kasuwanci da zai koma dashi zuwa Makkah. Sannan sai suka dawo tare da wannan ayari na ƴan kasuwa.

Lokacin da ya dawo wa Khadijah da dukiyarta sai ta siyar da abinda ya dawo dashi kuma ta samu riba mai ɗinbin yawa. Maisara ya bata labarin abinda wannan malamin kirista ya faɗa. Da kuma yanayin Manzon Allah da ya gani. Sai ta ƙaddamar da kanta zuwa ga Manzon Allah tana neman aurensa.

Nana Khadijah Ta kasance mace mai dukiya da kuma Ɗaukaka. Lokacin da ta faɗawa Annabi cewa tana son shi da aure, sai yaje ya sanar da ƴan’uwan mahaifinsa Domin neman shawarinsu. Kuwa suka amince masa.

Sai baffansa Hamza ya tafi tare dashi zuwa ga mahaifin nana Khadijah domin neman aurenta.

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya aureta. Kuma itace matarsa ta farko. Kuma bai auri wata mace ba har sai da ta mutu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates