TARJAMAR NASSIN FATAWAR BABBAN MAJALISAR FIQHUN MUSULUNCI TA DUNIYA GAME ALLURAR RIGAKAFIN CUTAR POLIO(Ibrahim Jalo Jalingo)

·

·

Kafin mu kawo tarjamar muna
jinjinawa dukkan abokanmu na
da’awah zuwa ga yin riko da
sahihiyar Sunnah koda kuwa mun
yi sabani da wasunsu cikin wasu
bangarori na wannan mas’ala ta
allurar rigakafin cutar polio. Muna
fata Allah Ya taimake mu.
*******************************
Ita dai wannan fatawa ta Babbar
Majalisar Fiqhun Musulunci ta
Duniya an yi ta ne a ran 7/6/1434
H 17/4/2013 M.
*******************************
Ga nassin fatawar: ((Bayani na
biyu daga babbar majalisar fiqhun
Musulunci ta Duniya game da
sha’anin wajibcin yin allurar
rigakafin cutar polio:
Godiya ta tabbata ga Allah
Ubangijin talikai, tsira da aminci su
tabbata ga annabinmu Muhammad
da iyalansa da sahabbansa gaba
daya.
Bayan haka: Lalle majalisar fiqhun
Musulunci ta Duniya wacce ta
samo asali daga Kungiyar
taimakon juna ta Musulunci, lura
da ta yi na matsayinta cikin
Musulunci, saboda ganin cewa ita
marji’i ne na Fiqhu ga al’ummar
Musulmi, da kuma irin yadda ta
fahimci wajibcin da aka dora wa
Malamai masu nasiha, bayan ta
karbi rahotanni kan irin yadda aikin
yin allurar riga kafi ya yi nasara a
kasashen Musulmi game da
dakatar da yaduwar ciwon polio a
cikinsu, in banda sashin wasu
kasashen kamar su: Pakistan, da
Nigeria, da Afganistan, wanda
kuma hakan ya zo daidai da sabon
kamfen din da gwamnatocin
wadannan kasashe suke yi, toh ita
(wannan majalisa) tana sabunta
kiranta ga iyaye maza da mata, da
dukkan masu lura da yara kanana
cikin dukkan Duniya, tana kiransu
da su ba da hadin kai ga wannan
kamfe, su kuma gaggauta yi wa
‘yayansu maza da mata allurar riga
kafin cutar polio, saboda tabbatar
muhimmancin cewa wannan
allurar na raba su da sharrin
kamuwa -cikin falalar Allah da
ni’imarsa- da cutar polio wacce har
yanzun nan ba ta da magani in har
ta kama mutum, wacce kuma take
sabbaba nakasa ta dindin ga mara
lafiya.
(lalle yin wannan allurar) wajibi ne
na shari’ar Musulunci, kuma
amana ce a wuyayen shugabannin
yara, su ne kuma za su dauki
zunubin kin yi wa yaransu wannan
allurar.
Hakika ya tabbata daga bangarorin
da suke da hakki a kasashen
Musulmi cewa wannan allura babu
wani abu a cikinta da yake da
alaka da alade, sannan kamar
yadda wadanda aka amince da
ilminsu suka tabbatar babu wani
abu cikin allurar da yake hana
haifuwa ga mata cikin kwanukan
rayuwarsu masu zuwa.
Sannan dukkan kasashen Duniya
daga cikinsu har da kasashen
Musulmi sun yi ittifaki a kan yi wa
yara wannan allura ta rigakafin
cutar polio, da kuma cewa babu
wata cutarwa da ta tabbata a
cikinta.
Sannan wannan wajibci da yake
kan iyaye da shugabanni yana
farawa ne tun ranar da aka haifi
yaro kuma zai ci gaba har lokacin
da ya kai shekaru shida, tare da
bin tsarin jadawali na karban
allurar kamar yadda aka tsara,
saboda fa’idar riga kafi ta tabbata,
tare kuma da maida hankali zuwa
ga sauran allurai na riga kafi da
ake yi wa yaran kamar na:
Tuberculosis, da Diphtheria, da
Titanous, da Whooping-cough, da
Liver disease, da Measles, lalle
alluran rigakafi da wasunsa suna
da tasiri cikin wadannan cutuka –
bayan falalar Allah da minnarsa-
watau wajen kauda annoba, da
cutuka masu yaduwa wadanda a
da can yan adam suka yi ta fama
da su, kamar ciwon agana da
makamantansa.
Hakika Babbar majalisar Fiqhun
Musulunci ta Duniya ta halatta wa
masu mulki -ganin cewa su ne
wadanda umurninsu ke da alaka
da maslaha- ta halatta masu tilasta
wa mutane yin alluran rigakafi
saboda abin da yake cikin yinsa na
hana yaduwar cutuka.
Lalle ya zo cikin Sakin layi “b”
Article na uku na Matsayar Babbar
Majalisar Fiqhun Musulunci ta
Duniya, lamba: 67 (7/5) shekara ta
1412 H wanda ya yi daidai da 1992
M game da sha’anin jinya abin da
nassinsa ya ce: ((Yana halatta ga
masu mulki su tilasta wa mutane
yin jinya a wasu lokuta, kamar
jinyar cutuka masu yaduwa cikin
jama’a, da karban allurar rigakafi)).
Lalle Malaman Babban Majalisar
Fiqhun Musulunci ta Duniya da
dukkan masana Fiqhunta wadanda
ke wakiltan kasashensu, dukkansu
suna da burin su ga cewa matasan
al’ummar Musulmi masu zuwa nan
gaba sun kasance suna jin dadin
rayuwa da irin baiwar da Allah
Mabuwayi Ya ba su kamar yadda
ya kamata, kuma su kasance suna
cikin cikakken koshin lafiya,
lamuransu su kasance har karshe
lamura ne masu kyau, saboda duk
lokacin da aka ce yara mazansu da
matansu suna cikin koshin lafiya,
to kuwa lalle ana musu tsammanin
makoma kyakkyawa.
Babbar Majalisar Fiqhun
Musulunci ta Duniya tana yin
wasiyya ga dukkan kasashen
Duniya saboda kasancewar yaki
da polio lamari ne na nuna wa dan
adam jinkai, haka nan kuma tana
yi wa kasashen Musulmi da sauran
kungiyoyinsu kebabbiyar wasiyya,
saboda kasancewar mas’alar yaki
da cutar polio mas’ala ce da ta
shafi Al’umma, da cewa su yi
dukkan abin da za su yi saboda su
kauda dukkan abin za iya kawo wa
yin allurar rigakafi cikas, su yi
dukkan abin da za su iya yi domin
kawar da dukkan wasu wahalhalu
da za su iya hana yin allurar.
Sannan a wannan wuri,
Sakatariyar Babbar Majalisar
Fighun Musulunci ta Duniya tana
yin tir da fatawowin da suka fito
daga sashin wadanda sawaaba ta
nisance su, fatawowin da suke
haramta yin allurar riga kafi,
fatawowin da suka dogara a kan
wasu bayanai mara kan gado, da
kuma wasu tunani na kure,
fatawowin da aka fitar ba tare da
an yi tunanin irin barnar da za su
iya jawo ba na cusa yara cikin
wannan mugun ciwo ba tare da
sun yi wani laifi ba, illa dai kawai
iyayensu ne suka yi aiki da
fatawowin wadancan mutane.
Babbar Majalisar tana yin wasiyya
ga masu hudubar masallatai da
limamansu, da Malamai masu
wa’azi masu kira zuwa ga Allah
Mabuwayi, masu shiryarwa masu
karantarwa da su kira jama’a a
cikin hudubobinsu cewa su bada
hadin kai a nan gaba ga aikin
allurar rigakafi, sannan kuma su yi
aiki domin yakar wancan fatawa
wacce take shazzah (fatawar yan
tsiraru da ta saba wa fatawar masu
rinjaye) wacce take cewa yin
allurar rigakafin cutar polio
haramun ne, kuma take ta sanya
shakka da balbala cikin mutane ba
tare wata hujja ko dalili ba.
Sannan Babbar Majalisar Fiqhun
Musulunci ta Duniya tana yin tir da
babbar murya da abin da sashin
masu laifi suka aikata na kashe
wani adadi na ma’aikatan allurar
rigakafin cutar polio, da ma
wasunsu daga cikin ma’aikatan
kiwon lafiya, ba tare da sun yi wani
laifi ba, da kuma yin garkuwa da
wasunsu saboda neman fansa
domin neman biyan wasu bukatu
kebabbu ko gamammu, abin da
Shari’ar Musulunci da ma sauran
shari’u, da dokokin kasashen
Duniya suka haramta.
Haka nan Babbar Majalisa tana yin
tir da yin amfani da aikin polio da
wasu masu taimakawa aikin ke yi
domin biyan bukatun kansu, ko dai
a bayyane ko kuwa a boye ta
hanyar leken asiri, abin da ba yi da
wata alaka da harkar kiwon lafiya,
tana yin tir da haka saboda hakan
ya saba wa dokokin Duniya da
kuma ayyukan kwarai na jinya.
Hakika Babbar Majalisar Fiqhun
Musulunci ta Duniya ta fitar da
bayani filla-filla a shekarar 1430 H
wanda ya yi daidai da 2009 M
domin jan hankulan jama’a saboda
yin allurar rigakafin polio, bayanin
da ya kunshi hukunce-hukunce da
kuma dalilai na Shari’ah wadanda
suka bayyanar da wajibcin yin
allurar rigakafin cutar polio, sannan
a yanzu kuma tana kara karfafa
abin da ya zo cikin wancan
bayanin wanda ma’anarsa a
takaice shi ne:-
Wajibi ne a kan mutum ya kare
jikinsa da jikin iyalansa, ya kuma
tsare lafiyarsu, ya nisantar da su
dukkan wani abu da zai cutar da su
iya karfinsa, saboda fadar Allah
Madaukaki: ((Kada ku jefa
hannayenku zuwa ga halaka, ku
kyautata, lalle Allah Yana son
masu kyautatawa)). Suratul
Bakara: 195. Yin abin da zai kare
lafiyar jikkuna daga dukkan wani
abu da zai sa su cikin hatsari yana
daga cikin manyan wajibai cikin
Shari’ar Musulunci, sannan Ka’idar
hana cuta da cutarwa ita ma ta
hana hakan, ka’idar da take
asalinta shi ne adithin Annabi daga
Dan Abbas ya ce: Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah Ya ce:
((Babu cuta babu cutarwa)). Imam
Ahmad ne ya fidda shi cikin
Musnad dinsa, da Hakim cikin
Mustadrak, da wasunsu.
Musulunci ya dora wa iyaye maza
da mata dawainiya mai girma
game da sanya tsaro ga ‘yayansu
maza da mata, da kuma kyautata
kiwon dukkan sha’anoninsu, daga
cikin hakan akwai: Sha’aninsu na
lafiya musamman ma wadanda ba
su balaga ba daga cikinsu, akwai
hadithai da suka zo da hakan daga
cikinsu akwai fadarsa mai tsira da
aminci: ((Dukkanku masu kiwo ne
kuma wadanda ake tambayarsu
kiwon da aka ba su, Shugaba mai
kiwo ne kuma wanda ake
tambayarsa kiwon da aka ba shi
ne, Na miji mai kiwo ne cikin
iyalansa kuma wanda ake
tambayar abin da aka ba shi kiwo
ne, Mace mai kiwo ce cikin gidan
mijnta kuma wacce ake tambayar
abin da aka ba ta kiwonsa ne)).
Buhari da Muslim ne suka fitar da
shi. Da kuma fadarsa mai tsira da
amincin Allah: ((Ya isan ma mutum
a matsayin zunubi a ce ya yi watsi
da wanda yake iyali ne gare shi)).
Almustadrak.
Allah Mabuwayi ya yi wa mutum
ni’ima da ya halicce shi cikin mafi
kyauwun tsari, Mabuwayi ya ce:
((Hakika mun halicci mutum a bisa
mafi kyawun tsari)). Suratut Tiin: 4.
Mabuwayi Ya yabi annabinSa
Zakariyya a lokacin da ya roke shi
kyakkyawan zurriyya, neman
kyakkyawan zurriyya yana hadawa
da lafiyar jiki, Mabuwayi Ya ce: ((A
can ne fa Zakariyya ya roki
Ubangijinsa Ya ce: Ya Ubangiji Ka
ba ni wata zurriyya mai kyau daga
gare ka, lalle kai Mai jin addu’a ne)
). A’alu Imran: 38. Sannan
Musulunci ya kwadaitar da mutum
da ya nemi sabuban karfi da kuma
dukkan abin da zai taimake shi, an
karbo daga Abu Hurairah Allah Ya
kara masa yarda ya ce: Annabi mai
tsira da amincin Allah ya ce:
((Mumini mai karfi ya fi alheri kuma
ya fi soyuwa a wurin Allah a kan
mumini mai rauni, amma akwai
alheri a cikin ko wanne daga
cikinsu, ka nuna kwadayin samar
da abin da zai amfane ka..)).
Muslim ne ya ruwaito shi.
Akwai hadithai da suka zo game
da jan hankali domin neman jinya
da sabuban da suka dace wurin
jinyar, daga cikinsu akwai fadarsa
mai tsira da amincin Allah: ((Ku yi
magani lalle Allah Mabuwayi bai
sanya wata cuta ba face sai da ya
sanya mata magani, in banda cuta
guda’ watau tsufa)). Abu Dawud,
da Tirmizi, da Ahmad ne suka fidda
shi.
Ana daukan allurar rigakafin cutar
polio a matsayin jinya na kariya
daga cutar da ake tsoron
aukuwarta kafin ta auku, abin da
ake kira da harshen zamani
magani irin na kariya, hakika
Musulunci ya tabbatar da wannan
matsayi, saboda ya zo daga
Annabi mai tsira da amincin Allah
cewa: ((Wanda ya karya da dabino
bakwai daga cikin dabinon Madina,
to sihiri ko guba ba zai cutar da shi
ba)). Buhari ne ya ruwaito shi.
Kamar yadda ya tabbatar da shi
har yanzu a cikin ka’idodin da ake
bi domin a hana yaduwar cuta mai
yaduwa cikin jama’a, an karbo
daga Annabi mai tsira da amincin
Allah cewa ya ce: ((Idan kun ji
labarin aukuwar annoba a wata
kasa, to kada ku shige ta, idan
kuma annoba ta auku a kasar da
kuke cikinta to kada ku fita daga
cikinta)). Buhari ne ya ruwaito shi.
Musulunci yana kira zuwa ga
fa’idanta daga dukkan wani
bincike, ko wani ci gaba da aka
samu na ilmin kimiyya wanda zai
saukake rayuwar mutum a wannan
Duniya… Lalle shi ya zo ne domin
ya tabbatar da alherin mutane da
jin dadinsu Duniya da Lahira,
Madaukaki Ya ce: ((Ku tambayi
ma’abuta ambato in har ku ba ku
sani ba)). Annahl: 43. Mai tsarki Ya
ce: ((Ba mu aiko ka ba face a
matsayin rahama ga Duniya)). Al-
Ambiya: 107.
Lalle tunkude cutuka ta hanyar yin
allurar rigakafi ba ya karo da yin
tawakkali, kamar yadda tunkude
yunwa, da kishin ruwa, da zafi, da
sanyi, ta hanyar yin kishiyoyinsu ba
ya karo da shi tawakkalin, a
gaskiya ma hakikanin tawakkali ba
ya cika sai an yi riko da sabuba na
fili wadanda Allah Madaukaki Ya
kafa su domin su rika samar da
abin da suke sabbabawa ne bisa
kaddara da Shari’ah, saboda haka
yana yiwuwa barin yin allurar
rigakafi ya zama haram matukar
dai hakan zai cutar. Wannan shi ne
abin da aka rubuta a takaice.
Allah Ya yi dadin tsira da aminci ga
shugabanmu Muhammad da
iyalansa da sahabbansa da
wadanda suka bi shi da kyautayi
har zuwa ranar Kiyama.
Sakataren Babbar Majalisar
Fiqhun Musulunci ta Duniya
Professor Ahmad Khalid Babakr
Cikin garin Jidda
7/6/1434
17/4/2013)). Intaha.
*************************************
Yan’uwa Musulmi wannan ita ce
tarjamar fatawar Babbar Majalisar
Fiqhun Musulunci ta Duniya game
da allurar rigakafin cutar polio,
manufarmu da kawo wannan
fatawar shi ne fa’idantar ‘yan’uwa
Musulmi na wannan kasa tamu
Nigeria, saboda su san mene
matsayin majoratin Maluman
Musulunci na Duniya game da
wannan allura ta rigakafin cutar
polio.
Sannan ina jan hankalin ‘yan’uwa
da su rika yin taka tsantsan cikin
lamuransu, su daina gina lamura a
kan aatifah ko son wani kawai, ko
kuma kin wani kawai, waji bi ne a
rika hankalta game da yadda
lamura ke kasancewa har su cutar
da mutane, ko suke faruwa har su
amfanar da mutane.
Lalle zai zama abin mamaki
matuka mutane su ki karban
shaidar mafiya yawan likitocin
Duniya, sannan kuma kuma su
karbi shidar mainoratinsu wacce ta
saba wa shaidar mafiya yawan!!
Haka nan zai zama abin mamaki
matuka mutane su yi watsi da
fatawar Majoratin Maluman
Musulunci na Duniya, su koma
suna yi musu jumhiri suna cewa su
‘yan kanzagin Yahudawa ne, su
wadanda kafurai suka ba su kudi
ne domin su cutar da al’ummar
Musulmi, sannan kuma su suna yin
dukkan abin nan da suke yi ne
saboda dogara da wata fatawa da
wasu mainorati suka bayar.
Haka nan abin mamaki ne matuka,
mutane su karyata gwamnatocin
kasashe wadanda babban aikinsu
shi ne lura da maslahar jama’arsu
cikin fannoni daban daban cikinsu
kuwa har da fannin kiwon lafiya, su
karyata gwamnatocin su daura yin
yaki da su ko dai da baki ko kuwa
da alkalami, wasu ma har da
makami domin akwai masu kai wa
masu aikin allurar rigakafin cutar
polio hari da makami su kuma
kashe wadanda kwanansu suka
kare, saboda kawai dogara da
bayanan da wasu daidaiku cikin
al’umma suka fada!!!
Lalle irin wannan manhaji gairi
mahsuubil awaaqib shi ne yake
kawo hargitsi cikin Kasa da
Al’ummah, kuma su jahilai har
kullum irin wannan yanayi suke so,
inda nan da nan sai ku ga cewa
sun fara fiskantar mutane da
fasikantarwa, sai kuma kafirtawa,
daga nana sai kuma kawo musu
hari bisa hujjar cewa su makiya
al’ummar Musulmi ne, su mutane
ne da suka karbi kudin Yahudawa
domin su cutar da Al’ummah!!!
Lalle mu a wannan Kasa ya
kamata mu fi kowa taka tsantsan,
saboda har yanzu ba mu fita ba
tukun daga musibar wadanda suka
haramta karatun boko, saboda
kawai su a ganinsu karatun boko
yana karo da addinin Musulunci
yana kuma cutar da Musulmi cikin
addininsu, suna da irin shubuhohi
nasu da suke ambatawa, amma
dai majoratin maluman Musulunci
sun san da cewa su ‘yan hayaniya
ne kawai, kuma wannan lamari
nasu babu abin da yake yi face
cutar da Musulunci da Musulmi.
Muna rokon Allah Madaukakin
Sarki ya nuna mana gaskiya
gaskiya ce ya ba mu ikon aiki da
ita ya nuna mana karya karya ce
ya ba mu ikon guje mata.
Ya kuma raba mu mu wannan
Al’ummah Islamiyyah da sharrin
‘yan hayaniya da jahilai cikin rigar
malamai. Ameen.

6 responses to “TARJAMAR NASSIN FATAWAR BABBAN MAJALISAR FIQHUN MUSULUNCI TA DUNIYA GAME ALLURAR RIGAKAFIN CUTAR POLIO(Ibrahim Jalo Jalingo)”
 1. Kabir garba Avatar
  Kabir garba

  Mun gode allah yasaka da alkhairi,ya ganar da wanda yajahilchi wannan allura.

 2. Marwan B. Kabir Avatar

  Allah Ya Saka

 3. Salisu Avatar
  Salisu

  Allah yatemaka

 4. Abubakar Auwalu Avatar
  Abubakar Auwalu

  Allah yasa da alkhairi

 5. usman saleh Avatar
  usman saleh

  Mu dai yi hattara!!!???

 6. Muhd garba Avatar
  Muhd garba

  Mun gode allah ya biya

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: