Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh.
A-janu halittu ne na Allah kamar yadda mutane suke halittu, Cikinsu akwai Musulmai, akwai kafirai, Akwai masu mulki akwai masu kuɗi akwai talaka. Sannan kuma Kamar yadda Shari’a ta hau kanmu haka suma shari’a ta hau kansu.
Abune sananne a shari’a cewa Al-janu suna da banbanci da ƴan Adam, ta yadda suna iya ganin mu amma mu bamu iya ganinsu, Sannan kuma suna iya shiga jikin ɗan adam Kamar yadda Nassoshi na Shari’a suka tabbatar, sannan kuma yanayi na yau da kullum ya tabbatar da hakan.
To yaya Musulmi zai kare kansa daga shaiɗanun Al-janu?
- Lazimtar Zikirin safe da yamma: in kanaso ka samu kariya daga shaiɗanun Al-janu to ka lazimci zikirin safe da yamma wanda aka Rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, Domin wannan zikirin yana ƙunshe da addu’oi wa’inda zasu tsare mutum daga shaiɗanu da masu sihiri, Mutum zai iya amfani da littafin hisnul Muslim ya duba shafin zikirin safe da yamma
- Yin Bismillah yayin shiga gida: idan Mutum zai shiga gidansa to yayi Bismillah domin idan yayi Bismillah to shaiɗanu bazasu iya shiga gidan ba, Amma idan baiyi ba to zasu bishi su shiga kamar yadda aka rawaito daga Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Haka nan yana da kyau mutum ya koya wa yaransa da iyalansa duk wanda zai shiga gida ya rinƙa yin Bismillah kafin Sallama, ta yadda koda ya mance bai yi ba za’a samu wani daga cikinsu yayi.
- Yin Addu’a yayin fita daga gida: idan Mutum zai fita daga gida sai ya karanta Addu’ar da aka Rawaito daga Annabi, “Bismillah Tawakkaltu alallah Wala haula wala Quwwata illa billah” بسم الله توكلت على الله ولا حول ولا قوة إلا بالله idan Mutum ya karanta wannan Allah zai bashi kariya.
- Yin Bismillah yayin cin abinci: Idan mutum yazo cin Abinci ya ambaci sunan Allah, idan yayi haka toh zai kore shaiɗanu daga abincinsa, idan kuma baiyi ba to tare dashi zasu ci. Idan ya mance baiyi ba sai yayi a ƙarshe. Yace : “Bismillahi fi awwalihi wa aakhirih” بسم الله في أوله وآخره
- Yin Addu’a yayin shiga bayan gida: Idan Mutum shiga ban ɗaki yayi Addu’a wanda aka Rawaito. ” Allahumma inni Auzu bika Minal khubthi wal khaba’ith” اللهم إني أعوذ بك من الخبث والخبائث. Hakanan inya fito yayi Addu’a. “Gufranak” غفرانك
- Yin Addu’a yayin saduwa da iyali: Lokacin saduwarka da iyalinka ka ambaci sunar Allah sannan kayi Addu’a “Allahumma jannibnash-shaiɗana wa jannibish-shaiɗana ma razaqtana” اللهم جنبنا الشيطان وجنب الشيطان ما رزقتنا
- Yawaita karanta Al’qur’ani Musamman Suratul Baqara: Karanta Al’qur’ani a gida yana korin shaiɗanu musamman Suratul Baqara, domin Annabi yace shaiɗan yana gudu daga gidan da ake karanta suratul baqara.
- Kawar da duk wani kayan ɓarna daga gida: Dole Musumi ya kula da abinda yake shiga cikin gidansa, kada ya bari ana shigar masa da fina finan batsa, ko waƙoƙi Marasa kan gado da makamantansu, domin wannan yana janyo shaiɗanu cikin gidan
- Kawar da duk wani hoto: Haka nan hotuna da ake maƙala wa a bango ko ake ajiye su a bayyane suna hana Mala’ikan Rahama shiga gida wanda hakan ka iya janyo shaiɗanu cikin gidan.
Wannan kaɗan ne daga matakan kariya daga shaiɗanun Al-janu. Allah yasa mudace, ya kuma tsare mu daga sharrin su
Leave a Reply