Gulma shine ka ambaci wani abu na wani wanda baya so a sani. Kamar Mutum na aikata wani abu mara kyau sai kaje kana yaɗa shi a cikin mutane.
Gulma Haramun ne, Amma akwai wasu wurare da ya halatta ayi gulman mutum. Gasu kaman haka:
- Kai koke: Misalin mutum ya zalunce ka, ka kai koken sa wurin wanda zai bi maka haƙƙin ka, kaman Alƙali ko Waninsa, a lokacin ya halatta kayi bayanin halin wannan mutumi , Misali kace wane ya zalunce ni ya ci mini dukiya da makamantansa.
- Hani da mummuna: Misali mutum yana aikata mummunan aiki, ya halatta ka faɗa wa wa’inda zasu dakatar dashi su hukunta shi.
- Neman shawara: Misali wani ya nemi shawarar ka yana so yayi kasuwanci da wani mutum, kai kuma kasan halin mutumin nan bashi da kyau to dole ka faɗa masa gaskiyar halin wannan mutumin. Ko kuma ya nemi shawarar ka yanaso ya aurar da ɗiyar sa ga wani mutum kuma kasan mutumin bashi da hali mai kyau, anan ma dole ka faɗi gaskiyar halin mutumin nan da ka sani.
Leave a Reply