Baidace ace wani Qudubi ko wani Nujubi Ko wani Gausi Koma dai karamin shehi ko babba ya fito ya kafirta wa’innan mutane da suka zagi Annabi(sallallahu alaihi wasallam) a kano da sunan cewa su ‘yan hakika sannan kuma ya kasa kafirta inyass wanda awurinsa su wa’innan mutane suka samo aqeedunsu.Wannan rashin adalci ne. Duk da munsan cewa kafirtasu da akayi ta shafi dukansu har da babansu inyass da suka samo wannan aqeedah awurinsa, amma ya dace afito fili a kafirtashi shima domin kada nan gaba asami wani da zai sake zuwa ya dauko bayanansa na kafirci yana yadawa cikin al’ummah. Sannan cewa ayiwa ‘yan tijjaniyya adalci kada a dangantasu da wa’innan mutane wannan ba daidai bane. Wa’innan mutane bawai sabon abu sukazo dashi daga wurinsu ba, a’a abune wanda tuntuni yana rubuce tun shekarun baya masu yawa cikin littattafansu kuma malamansu suna koyar dashi sai dai ba kowa ake bari ya gane ba sai wanda yayi nisa cikin tafiyar. Wanda wannan abin da kafiran ‘yan hakikan kano suka fada kadanne daga cikin munanan abubuwa da suke kunshe cikin littattafansu. Abin da kawai zamuce ma ‘yan tijjaniyya su tausaya wa kansu su tuba subar wannan tafarki domin wannan tafarki ba ta annabi bace.
Leave a Reply