Zikiri shine ibada mafi sauƙi da mutum zai iya yi a ko wani irin hali a kwance ko a zaune, ko a tafiya….. Kayi ƙoƙari kayi amfani da lokacinka wurin yin zikiri, domin falalolinsa na da yawa.
Allah yace:
يا أيها الذين آمنوا اذكروا الله ذكراً كثيراً، وسبحوه بكرة وأصيلا
ya ku w’inda kuka yi imani ku ambaci Allah, ambato mai yawa.
Ku masa tasbihi safiya da maraice.
Sheikh Abdur Rahman Assi’idy yake cewa game da wannan ayah:
يأمر تعالى المؤمنين، بذكره ذكرا كثيرًا، من تهليل، وتحميد، وتسبيح، وتكبير وغير ذلك، من كل قول فيه قربة إلى اللّه، وأقل ذلك، أن يلازم الإنسان، أوراد الصباح، والمساء، وأدبار الصلوات الخمس، وعند العوارض والأسباب. وينبغي مداومة ذلك، في جميع الأوقات، على جميع الأحوال، فإن ذلك عبادة يسبق بها العامل، وهو مستريح، وداع إلى محبة اللّه ومعرفته، وعون على الخير، وكف اللسان عن الكلام القبيح
Allah maɗaukakin sarki yana umartan muminai da ambatonsa ambato mai yawa, abinda ya shafi la’ilaha illallah, da kuma hamdala, da tasbihi, da kabbara da ma wasunsu. Na wuridin safiya da yammaci, da kuma bayan salloli na farilla guda biyar. Da kuma wasu zikirorin na dabam wanda suka zo a sunnah. Yana da kyau mutum ya lazimcesu a kowani lokaci, a kowani hali, domin wannan ayyuka ne wanda zaisa mai shi ya samu kusanci zuwa ga Allah, kuma zai wuce waninsa dasu, kuma wannan aiki ne wanda babu wahala acikinsa, kuma yana sa son Allah da kuma saninsa, kuma yana taimakawa kan alheri, da kuma kame baki ga barin furta abinda bashi da kyau.
Yana da kyau musulmi ya lazamci zikiri, safiya da maraice, da kuma bayan salloli, da sauran zikirorin da aka Rawaito Annabi yana yinsu a lokuta da kuma wurare, domin hakan kariya ne ga mumini, sannan kuma ga samun lada.
Yana daga cikin zikiri mai falala lazimtar Subhanahi wabihamdihi subhanahil azeem.
Manzon Allah yace:
كلمتان خفيفتان على اللسان، ثقيلتان في الميزان، حبيبتان إلى الرحمن: سبحان الله وبحمده، سبحان الله العظيم
kalimomi guda biyu, masu sauƙi akan harce, masu nauyi akan sikeli, masu soyuwa zuwa ga Allah. “Subhanahi wabi hamdihi, subhanahil Azeem”.
-Bukhari 6682
Sai muyi ƙoƙari muyi amfani da lokutanmu wurin yin zikirin Allah kafin lokaci ya ƙure mana, Allah yasa mudace.
Leave a Reply