A wannan yanayi na zaman gida ya dace a tunatar da mutane yadda ake Sallar Jam’i a gida tare da iyali wanda gashi kamar haka:
Mata da Miji: Miji zaiyi limanci, zai tsaya a gaba ita kuma ta tsaya a baya kamar yadda hoto na farko daga dama ya nuna
Ɗa da Uba: Zasu tsaya a sahu ɗaya, Limami daga cikinsu zai tsaya a gefen hagu, shi kuma mamu zai tsaya a gefen daman Liman kamar yadda hoto na biyu daga sama ya nuna
Ɗa da Uwa da Uba: ɗa da uba zasu tsaya tare uwa kuma zata kasance a bayansu kamar yadda hoto na tsaƙiya daga hanun dama ya nuna
Uba da Uwa da ƴaƴa mata da maza: Uba inya zamto shine liman zai tsaya a gaba, sai ƴaƴa maza su tsaya a bayansa, sai ƴaƴa mata da uwa su tsaya a bayansu, kamar yadda hoto na tsaƙiya daga hanun hagu ya nuna.
Uba da ƴaƴansa Maza: Limami daga cikinsu zai tsaya a gaba sai sauran su tsaya a baya kamar yadda hoto na ƙasa daga hanun dama.
Uba da Uwa da ƴaƴansu maza: Uba in shine Liman zai tsaya a gaba sai ƴaƴa maza su tsaya a bayanshi, sai Uwa ta tsaya a bayansu.
Leave a Reply