​MUSULUNCI BAI WAJABTA WA KOWA RIKON WATA AYYANANNAR MAZHABA BA

Danna nan domin shiga karatu Online

Mai Rubutu: Dr. Ibrahim Jalo
1. Babu inda Allah da manzonSa suka wajabta wa kowa yin riko da wata ayyanannar mazhaba cikin Mazhabobin da ake da su; sawaa’un Mazhabobin nan hudu ne ko kuwa wasunsu.
2. Wajibi ne a kan Musulumi ya gina addininsa a kan sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda duk wanda ya bar yin aiki da ingantaccen hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah cikin wata mas’ala cikin mas’aloli, kuma cikin zabinsa da jin dadinsa a bisa hujjar cewa: mazhabarsa ta saba wa hadithin, ko wata darika tasa ta Sufaye ta saba wa hadithin, ko wani tsari na kungiyarsa ya saba wa hadithin, ko wani tsari na duniyarsa ya saba wa hadithin to lalle wannan ya bace ya bar hanyar Muminai. Wannan kuwa shi ne abin da nassoshin Alkur’ani mai girma da Sunnah mai daraja ke tabbatarwa. Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu’ul Fataawaa 24/202:-

‎((وأما من تبينت له السنة فظن ان غيرها خير منها فهو ضال مبتدع بل كافر)).
Ma’ana: ((Amma wannan da Sunnah ta bayyana gare shi, sannan ya yi zaton cewa waninta ya fi ta alheri, to shi dan’bidi’ah ne, kai kafiri ne ma)).
Ya kuma ce cikin littafin 27/125:-
‎((ومن ترك النقل المصدق عن القائل المعصوم واتبع نقلا غير مصدق عن قائل غير معصوم فقد ضل ضلالا بعيدا)).
Ma’ana: ((Wanda ya bar nakalin da aka gaskata daga mai fada wanda yake ma’asuu’mi, sannan ya bi nakalin da ba a gaskata ba daga mai fadan da ba ma’asuu’mi ba, hakika ya bace bata mai nisa)).
Sannan Shehu Uthmanu Dan Fodiyo ya ce cikin littafinsa Hidaayatul Taalib shafi 28 ((واعلم ان الله تعالى لم يوجب في كتابه ولا رسوله في حديث صحيح ولا ضعيف كما قال ابن عبد البر رحمه الله التزام مذهب من مذاهب المجتهدين بخصوصه)) 
ma’ana: ((Ka sani lalle Allah da manzonSa ba su lazimatar wa kowa cikin Hadithi sahihi ko Dha’ifi kamar yadda Ibnu Abdul Barr ya ce bin wata mazhaba kebantacciya ba cikin Mazhabobin Mujtahidai)).
3. Yana da kyau kowa ya san cewa: Ba mazhaba ba ce laifi, a’a abin da yake laifi shi ne mazhabanci; watau nassi ya inganta daga manzon Allah cikin wata mas’ala daga cikin mas’aloli amma a ki yin aiki da nassin a bisa hujjar cewa ya saba wa abin da ke rubuce cikin wata mazhabar. Haka nan ba kungiya ba ce laifi, a’a kungiyanci shi ne laifi; watau nassi ya inganta daga manzon Allah cikin wata mas’ala daga cikin mas’aloli amma a ki yin aiki da nassin a bisa hujjar cewa ya saba wa wani tsari na wata kungiya.
4. Duk wani mutumin kirki daga cikin Malamai da aka ji ya nasabta kansa ko wasu sun nasabta shi zuwa wata mazhaba to lalle a kan wannan ka’ida yake ta cewa da zarar nassin Annabi ya saba wa mazhabar to zai bi nassin Annabi ya bar abin da mazhabar ta ce.
Allah muke roko da Ya tausaya wa al’ummarmu ya cusa musu ganin girman Annabi mai tsira da amincin Allah cikin zukatansu, da kuma kaunar gabatar da maganarsa a kan maganar waninsa cikin halittu. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “​MUSULUNCI BAI WAJABTA WA KOWA RIKON WATA AYYANANNAR MAZHABA BA”
  1. […] Source: ​MUSULUNCI BAI WAJABTA WA KOWA RIKON WATA AYYANANNAR MAZHABA BA […]

  2. Allah ya saka da alkhairi

Leave a Reply

Categories
Latest updates