Abubuwa uku suna tunkuɗe Bala’i

Danna nan domin shiga karatu Online

Karatu, maqala

Abu na farko: yawaita Addu’a; Addu’a ta ibada(Du’au ibadah) da kuma Addu’a ta roƙo(Dua’u mas’ala). Ya zamto kullum bawa na cikin roƙon Allah alherin duniya da lahira, da kuma yawaitar Zikirin Allah, domin da wannan ne zai sami kulawar Allah. Allah yace

Kace: Ubangiji na baya kula daku inba domin Addu’a da kukeyi ba.

Surat Al-furqan: 77

Wannan ya nuna cewa mai yawar Addu’a zai sami kulawar Allah, wanda kuma bayayi bazai samu ba.

Abu na biyu: Godewa Allah akan Ni’imomi; Domin in Allah yayi wa mutum Ni’imah kuma mutum yayi godiya akan wannan Ni’imah toh Allah zai ƙara masa wannan ni’imar da waninsa, kuma ya dawwamar masa da ita. Allah yace:

Lalle idan kuka gode toh lalle zan ƙara muku( Ma’ana in kuka gode wa Ni’ima ta)

Surat Ibrahim: Ayah No 7

Abu na uku: Taimakawa masu rauni; Taimakon masu rauni yana janyo ƙarin arziki da kuma samun nasara. Kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

Shin kuna ga Ana taimaka muku ne da kuma azurta ku inda ba domin masu rauni daga cikinku ba?

Sahihul Bukhari: 2896

Ma’ana Addu’a da Masu rauni daga cikin Al’umma da ikhlasinsu yana daga cikin sabuban da kesa Allah ya azurta mu ya kuma basu nasara, shiyasa bashi halatta a walaƙantasu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates