BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MU KARANTA TARIHI TARIHIN RIKICIN TATTAR (MAJLISI NA 1)(Dr Mansur Sakkwato)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
MU KARANTA TARIHI
TARIHIN RIKICIN TATTAR
(MAJLISI NA 1)
Gabatarwa
Allah Tabaraka Wa Ta’ala yana da
sunnoni da ya shimfida rayuwar
duniya a kan su. Tsari ne da yake
tafiya sambai babu karkata babu
kwana kuma ba ya canza hanya.
Abinda ka ga ya faru gare ka yau
ya faru ga wani jiya kuma gobe zai
sake faruwa ga wani.. haka har
zuwa ranar tashin kiyama.
Game da sha’anin munafukai,
Allah cewa ya yi: Sunnar Allah ce
da ta shude tun gabanin haka,
kuma ba zaka samun musaya ba
ga sunnar Allah. Suratul Ahzab:
62.
A duba Suratul Fathi: 22-23 da
Suratu Hijr: 4-15.
Wannan shi zai bayyana mana
muhimmancin sanin tarihi. Duk
abinda ka ga ya faru to an taba yin
irin sa. Ba wani sabon abu a
duniya. Idan muka bi tarihi sai mu
amfana da rayuwar wadanda suka
gabace mu. A gobe kuma
rayuwarmu ita ce tarihin. Ba ana
karanta tarihi ne kawai don aji
dadin karatu ba, ko don a sha
dariya ko don a ga abin al’ajabi.
Manufar karanta tarihi ita ce samun
abin lura wanda sanin sa zai sa mu
amfana; mu gyara tamu rayuwa,
mu kauce ma kurakuran na gaba,
mu bi sawunsu inda suka yi daidai.
Abinda duk suka cimma kuwa idan
mun bi tafarkinsu shi zamu cimma.
Alkur’ani sulusinsa labari ne.
Labarin annabawa, labarin
mummunai da na kafirai iri-iri.
Labarin nasarori da na matsaloli da
suka cimma mutane bisa ga
ayyukansu. Akwai kuma sura ta
musamman a cikin sa mai suna
Suratul Qasas, Surar Labarai, mai
ayoyi 88.
Don haka Allah Ta’ala ya ce: “Ka
labarta masu labaran ko da zasu yi
tunani”. Suratul A’raf: 175. Kuma
ya ce: “Hakika akwai abin lura a
cikin labaransu ga masu hankula”.
Suratu Yusuf: 111.
Darasinmu na yau zai yi bitar wani
labari ne daga cikin muhimman
abinda tarihin musulunci, kai ma
tarihin duniya gaba daya ya kunsa.
Abu ne da ya faru a cikin karni na
bakwai. Wucewarsa yau kuma ya
wuce shekaru dari bakwai, amma
cike yake da darussa masu hikima
da amfani ga al’ummarmu ta yau
da al’ummomi na kowane lokaci.
A yau zamu bada labarin Tattar,
wata al’umma wadda ta bayyana
kwatsam a cikin tarihin duniya.
Wadanda suka shedi bayyanar ta
da abubuwan da suka faru a
lokacinta sun ce suna jin tsoron
nan gaba in an fadi labarin Tattar a
karyata shi saboda al’amurransu
gaba daya sun tsallake hankali.
Kome na Tattar mai ban tsoro ne.
Yawan jama’arsu, kwarin shirinsu,
karfin jikinsu, taurin zukatansu da
rashin imaninsu. Haka kuma
yawan zubar da jinainan da suka
yi, da yawan biranen da suka rusa.
Yadda suka tozarta al’ummar
musulmi, suka wargaza daulolin
duniya cikin kankanen lokaci.
Yadda suka game duniya nan take
a lokacin da babu hanyoyin sufuri
babu na sadarwa. Tarihinsu ta
kowace fuska abin tsoro ne, abin
mamaki ne. Abinda ya fi haka ban
mamaki shi ne a yau wani karfi na
kafirci ya bayyana mai kama da
nasu, kuma a wadancan birane da
wancan abin ya faru, da mutane
irin wadancan da suka taka rawa a
wancan lokaci, suna kisan kiyashi
ga al’ummar musulmi suna yi masu
wulakanci kamar yadda a can
farkon ma musulmi ne aka
wulakanta.
Musulmin da suka shedi bala’in
Tattar sun yi tsammanin an kai
karshen duniya kenan, ko kuma
alal-akalla an gama da musulunci
da musulmi; ba za a sake jin
labarinsu ba. Wasu marubuta irin
su Ibnul Athir sun yi shekaru da
dama suna juyayi kafin su fara
rubuta abin da suka gane ma
idonsu. Akwai wadanda da-na-sani
da jin haushi ya kai su ga cewa,
ina ma gaba daya uwayensu basu
haife su ba! Don tsananin musibar
da suka auka tare da al’ummar
musulmi a cikin ta. Ibnul Athir ma
cewa yayyi, gara fitinar Dujjal da
waccan fitina ta Tattar. Ya ce
kuma: « Na rantse da Allah a nan
gaba in an fadi wannan labari na
baya sai sun karyata shi, kuma
suna da gaskiya don ya wuce
hankali ». Mai wannan maganar fa
– Ibnul Athir – ya rasu a shekara ta
637H tun fitinarsu ba ta kai karshe
ba, tun kafin su yi ta’adin da ba a
taba jin irin sa ba na kashe halifan
musulunci da zubar da jinin
musulmi miliyan biyu a cikin
kwanaki 40 kamar yadda zamu
gani a nan gaba. Da ace Ibnul Athir
ya ga shekara ta 699H sadda
Tattar suka tsallaka tekun “Furat”
suka shiga kasar Sham suka aukar
da bala’i wanda ba shi wasaftuwa
to da ba a san abinda zai ce ba.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah na
daga cikin wadanda suka gane ma
idonsa duk wadannan fitinu. Shi ya
sa ya ce, wannan fitinar tayi kama
da tsayin alkiyama in da uwa ke
gudun danta, miji ya guji matarsa,
masoyi na gudun masoyinsa; kowa
ta kansa yake yi, neman mafaka da
wurin tsira yake. A game da tarihin
Iran kawai Wikipedia Encyclopedia
ta kiyasta cewa Tattar sun kashe
tsakanin mutane miliyan 10 zuwa
15. A lokacin da Ibnul Athir yake
cewa, Tattar sun kashe musulmi
700,000 a Rayy (Tehran) a cikin
wuni guda.
Ku dakaci majlisi na 2 don jin
farkon tarihinsu in Allah ya so.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MU KARANTA TARIHI TARIHIN RIKICIN TATTAR (MAJLISI NA 1)(Dr Mansur Sakkwato)”
  1. ummulkhair Avatar
    ummulkhair

    jazakallahu khaira

Leave a Reply to ummulkhairCancel reply

Latest updates
Categories