BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
MU KARANTA TARIHI
TARIHIN RIKICIN TATTAR
(MAJLISI NA 3)
Shigowar Tattar a Biranen
Musulunci:
Wuri na farko da Tattar suka fara
kai hari shi ne Bukhara, inda suka
yi angaya a bayan wannan babban
birni. Suka kwana uku suna
gwabzawa da mayakan musulmi.
Daga karshe dai da yawan sojojin
musulmi suka gudu saboda bala’in
da suka gani wanda basu iyawa da
shi, suka tasar ma Khurasana.
Mutanen gari basu samu wata
mafita ba sai dai su yi saranda su
nemi a basu lamuni a kan
rayukansu. Alkali Badruddini ne ya
jagoranci masu neman wannan
sulhun. A ranar 4 ga watan Zhul
Hajji 616H aka buda ma Tattar
kofofin gari, suka shiga da makirci
suna masu nuna tausayawa da
kyautatawa ga mutane. Jinkizkhan
ya nemi mutanen Bukhara su
kama masu don su yaki sojoji
4000 da suka shiga Qal’ah
wadanda basu samu tserewa ba,
ya ce kuma duk wanda bai je ba za
a kashe shi. Ya kuma bada umurni
a cike babban ramin da sojojin
suka yi garkuwa da shi har ya sa
aka rinka dauko Alkur’anai daga
masallaci ana zubawa cikin ramin
don a cike shi. Aka kuma dauko
mimbarin masallaci aka kakkarya
katakonsa don a zuba cikin ramin a
cike shi. Da haka suka isa wannan
wuri suka gama da duk sauran
sojojin da suka rage ma musulmi.
Bayan haka ne sarkin Tattar ya ce
a rubuta masa sunayen muhimman
mutanen gari, ya sa aka rinka kiran
su guda guda, aka kwace duk wani
makami ko wata dukiya da ke
hannunsu, sannan aka yi masu
yankan rago baki daya. Sannan
aka kewaye sauran musulmi aka
rinka kisan su, aka farauci matansu
da ‘ya’yansu aka rinka aikata
alfasha da su gaban mazajensu.
Wadanda suka samu iya tserewa
suka gudu, wasu kuma suka auka
cikin makiya da makamai suka
samu shahada, cikin su har da
babban malamin fikihun nan
Ruknuddin Zadah da alkali
Sadruddin Khan. Wasu kuma aka
kama su ga hannu. Kai, a takaice
dai Tattar ba su bar birnin Bukhara
ba sai da suka kunna masa wuta,
suka kone masallatai da
makarantu da gidaje babu iyaka,
suka azabta fursunonin da suka
kama matsananciyar azaba. Inna
lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.
Daga nan suka tasar ma
Samarkanda, suka gargado
fursunonin musulmi kamar awaki a
gabansu, wanda duk ya kasa tafiya
sai su kashe shi su wuce. Suka
mika ma ko wane musulmi tuta ya
daga don a tsorata jama’ar
musulmin Samarkanda. Da isowar
su basu bata lokaci ba suka
gwabza da rundunar musulmi suka
kashe soja 50,000 sannan suka far
ma farar hula. Daga baya sai suka
rinka ja da baya suka zame jiki
musulmi na bin su, ashe wata
makida ce suka shirya sai da aka
fita garin gaba daya sai suka yanke
wata gada da suka haka suka yi
wa musulmi kimanin 70,000 zobe
suka kuma yi musu kisan kiyashi.
Su ma dai sauran mutanen da aka
baro a cikin birni sai da wancan
bala’in da ya cimma mutanen
Bukhara ya cimma su. Suka nemi
sulhu, Tattar suka ba su, kuma
suka yaudare su. Aka nemi su
bude kofofin gari, sannan su fito da
dukiyoyin da duk suka mallaka,
sannan su yo waje da dabbobinsu
da matansu da ‘ya’yansu. Aka ce
masu zamu kai ku wani wuri inda
zaku rayu.. daga karshe aka
gargada su zuwa titin alkiyama
baki daya. Sannan aka kona
babban masallacin gari, aka ci
mutuncin budare musulmi da rana
tsaka, aka aikata fasadi wanda ba
shi faduwa. Duka wannan ya faru a
cikin watan Muharram na shekarar
617H.
Zamu ci gaba in Allah ya so.
Leave a Reply