Babu wani Annabin Allah da ya zo
yana da’awar tauhidi face sai ya
koyar da mutane cewar su
bautawa Allah shi kadai kuma su
nisanci dagutu.
Amsar mushirikai da kafirai da
masu addinin gargajiya suke ba
dukkan wani Annabi ciki har da
Annabi Muhammad (SAW) shi ne
ya na zagin Iyayensu da
aibantashi.
Babu wani mutum da zai yi
da’awar kiyaye tauhidi ta wurin
kadaita Allah shi kadai face sai an
zage shi, kalaman da ake fadawa
wadancan Annabawa shi ma irin
shi a ke fada musu, domin daman
kafirci hanya daya ce.
Duk mutumin da zai ce a kadaita
Allah shi kadai, farkon abin da
zaka ji an ce shi ne ya raina su
wane, ya zagi iyayenmu, ya kafirta
malamanmu.
Babu wanda zai kira sunan wani
musulmi ya ce shi kafiri ne.
Manzon Allah ya hana haka, ya ce
ma duk wanda ya jifi wani da
kafirci to dole zata fada kan daya.
Amma kuma shi manzon Allah
SAW shi da kansa ya fada mana
cewar musulmi zai iya yin aiki da
zai fitar da shi daga musulunci. To
irin wadancan ayyukan su ake
cewar mai yin su yana aikin kafirci.
To yana da kyau ka tambayi kanka
ko da kana da’awar Sunnah, shin
ayyukan da nake yi akwai wanda
manzon Allah ya ce mai yinsu kafiri
ne, ko kuma ya kafirta? Idan babu
sai ka godewa Allah idan kuma
akwai kada ka ce kana jiran wani
ko shawarar wani ka yi maza ka
tuba tun rana bata fito daga
yamma ba. (An rufe kofar tubaba
ko kuma ka jika a cikin kabari)
Mu yi addinin Musulunci da akida
da Ilimi da Hujja da koyarwar
magabata na farko. Ba ra’ayi ba,
ba don kaga wani aboki ko uba ko
dan’uwa yana yi ba, ko kuma don a
garinku aka fito da wannan akidar
ba, ko dan garinku shine shugaba
a wannan tafiya, ko kuma kana
yinta ne domin ka baiwa wane
haushi, ko domin ka sami kudi, ko
dan kin ga mijinki yana yi, dukkan
wata akida da za mu yi mu dauki
littafai mu karanta bango zuwa
bango, mu ji ya wannan akida
take, me take kokarin koyar da mu,
tana koyar da mu girmana
wadansu mutane ne ko kuma tana
kokari karantar da mu yadda zamu
bautawa Allah shi kadai ne.
Ka da ka shagalu da yawan
alkawarin aljanna ko karama da
wasu su ke yiwa mabiyansu, domin
karshen karama shi Manzon Allah,
amma kuma kullum Sahabbai na
tare da shi a Masallaci wurin
Sallah, ba su dai na dukkan wata
ibada da ya koyar da su ba har sai
da suka koma gurin mahaliccinsu.
Hasalima ba su karbi wani zikiri ba
da da idan suna yin shi ba sai sun
yi sallah ba, ba su kuma karbi wani
zikiri ba da idan suka yi shi zai rika
cin ladaddakinsu
Kada wani ya rude ka cewar akwai
wani abu da idan ka yi shi zai baka
darajar Annabawa da Sahabban
Manzon Allah, da hakan gaskiya
ne, da Sahabbai da Tabi’ai sun
shagalu da wannan ibada.
Idan kai Musulmin gaskiya ne
babban abin da zaka fi damuwa da
shi shine
1) YA MANZON ALLAH YAYI KA
ZA,
2) YA SAHABBANSA SUKA YI
WANNAN IBADA,
3) YA MUTANEN NAN WADANDA
YACE AYI KOYI DA SU SUKA
4) YI YA KUMA WADANDA SHI
MANZON YA CE LOKACINSU YA
FI KOWANE LOKACI ALBARKA
SUNA YI.
Ina muku rantsuwa da Allah wanda
babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah babu wanda zai yi ibada da
wannan matakai guda hudu face
ya tsira ya samu babban rabo.
Allah ka tsarkake mana niyyar m
Leave a Reply