DUK WANDA YA GODE ALLAH ZAI KARA MASA(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

Allah mai yawan kyauta ga bayinSa. Mu sani hakika samu da rashi duk na karkashin abinda Allah ya qaddara ga bawanSa. Kowa in ya dubi halin da yake ciki a rayuwa to tabbas zai ga ya fi wani samun ni’ima da baiwa cikin rabon da Allah ya ba shi na yadda yake gudanar da rayuwar sa. Haka nan shi ma wani ya fi shi sannan yana daidai da wani.
Ma gane cewa fahimtar cewa ka fi wani, kuma kai ma wani ya fi ka sai mai natsuwa da hankali, don hakan yana da wuya ga kowa don jinya ta kwadayi da buri da dan adam ke da shi. Kuma ba abinda ke jawo gasa da juna cikin tara abin duniya da son mamaye komi sai rashin godewa Allah. Duk fa wanda ke godewa rabon da Allah ya ba shi to ya dace wajen kama hanyar zama mumini mai yawan godiya.
Pls kowa ya yi nazari sosai, ya kalli tsarin gudanar da rayuwa gaba daya, za ka samu rabon dukiya, ilimi, mulki, da samun duk abinda rai ke so daga Allah ne shi kadai. Kuma daidai gwargwado an bawa kowa rabon sa. Amma ita zuciya na cike da hankoron neman kari, ga jiki da son hutu, rai dangin goro…. Hutawar zuciya da hanyar samun sauki da rayuwa mai dadi ita ce kowa ya godewa Allah bisa rabon da aka bashi.
Halin mutum sai Allah.. Mu kalli dabi’ar rashin godewa Allah bisa rabon da aka bamu tabbas shi ke jawo mana tunani iri iri, da rashin hutawar zuciya, shi ne sanadin hassada, kuma yana jawo mana mugun nufi, wassu ya kaisu ga sabawa Allah ta hanyoyin sata, cin rashawa, kudin riba, algus, kisan kai, da sauran irin su. Haka nan rashin godewa Allah na bata tsakanin iyaye da ‘ya ‘yan su, yana wargaza zaman aure, munana zato ga makusanta, haddasa fitina cikin al’umma, da sauran irin su. Hakanan rashin godiya na kashe zuciya, da fadawa tarkon shaidan na yawan son kayan wani.
‘Yan uwa na maza da mata, Allah mai rahma ne da kyauta mai yawa ga bayinSa a duniya da lahira. Kuma kowa ba ya wuce rabon sa. Sannan a sama ko kasa ba mai iya tareka daga samun abinda Allah ya hukunta za ka samu. Kuma duk mai yawan godewa Allah to tabbas Allah zai kara masa. Duk gabar rayuwa da ka samu kanka da zangon da ka kai rabon ka ne daga Allah ana fatan ka gode sai a kara maka.
Tir da wanda ya samu ya yi alfahari, da wanda ya bar Allah ya koma ga masihirta da bokaye, ko mai dauka zurfin tunaninsa, da tulin hikima da wayonsa ne jagorar samun wani abu a gareshi. Da mai buga kirji yana kirari da yawan ilimi ko dukiyar sa. Ko mai yawan gori da raina mutane. Muna rokon Allah ya shirye mu.
Madallah da rayuwar bayin Allah masu tsentseni, da masu natsuwa da saukin kai cikin dukkan mu’amala. Masu godewa ni’imar da Allah ya basu. Da ma su murna da yabawa dan rabon da Allah ya ba su.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “DUK WANDA YA GODE ALLAH ZAI KARA MASA(Sheikh Aliyu Said Gamawa)”
  1. Misbah Avatar

    Allahu Akbar.

Leave a Reply

Categories
Latest updates