An rawaito Hadisi daga Abi Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace: Annabi Tsira Da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
Idan bawa Musulmi yayi Alwala ya wanke fuskarsa, duk wani laifi da ya kalla da idonsa zata fita da ruwan. Idan ya wanke hannunsa duk wani zunubi da ya damƙa da hanun sa zai fice da ruwan. Idan ya wanke ƙafafuwan sa dukkan zunuban da ya taka da ƙafansa zasu fita tare da ruwan har ya fito tsaftattacce daga zunubansa.
Sharhi: Wannan hadisi yana nuna mana falalar alwala. Duk wanda yayi alwala ya wanke fuskarsa duk abinda ya kalla na Haramun da wannan fuska Wannan ruwan alwala zai wanke shi. Haka nan duk wani abinda ya aikata na Haramun da hanunshi idan ya wanke hanun Ruwan zai wanke wannan zunubi. Haka nan ƙafafuwan sa idan ya wanke su yayin alwala za’a wanke masa zunuban da ya aikata da ƙafar.
Sai dai mu sani cewa zunuban da alwala yake kankare wa shine ƙananun zunubai. Kamar yadda nassoshi suka nuna cewa Babban laifi yana buƙatar Tuba.
Wannan Hadisi Muslim ya rawaito shi hadisi na 244.
Leave a Reply