Shimfida: Nasihar Sayyidna ‘Ali (Allah ya yarda da shi) “Ku zama ‘Ya’yan Lahira Ba ‘Ya’yan Duniya ba”
Tambayoyi dake ciki:
- Wanda ya manta bai zauna a raka’ar sa ta biyu a sallar shaf’i, bai tuna ba sai da ya miqe zuwa raka’a ta uku – yaya zai yi. (Cikin minti 17)
- Wanda ya riski raka’a ɗaya a sallar magriba in zai rama zai yi karatu a boye ne ko zai bayyana?(Daga minti 17 zuwa minti 19).
- Wai gaskiya ne Ibn. Taimiyya bayi da Malamai? (Daga minti 19 zuwa minti 20)
- Idan mamu ya sami tahiya a jam’i alhali limamin ya yi rafkanuwa. shin mamum zai yi sujjar rafkanuwa tare da sauran massalata? (Cikin minti 21)
- Hukuncin ruwa da ya jirkita da warin hayaqi? (Daga minti 23 zuwa minti 24)
- Idan matafiye ya samu raka’oin qarshe a sallar mazaunin gıda, shin zai cika sallar ko zai bar ta a matsayin qasaru? (Daga minti 24 zuwa minti 25)
- Fadar Allahumma salli ala Muhammadin … yayi ko sai an karanta Salatin Ibrahimiya (Daga minti 25 zuwa minti 26)
- Mace da mijinta yake dukanta kuma baya biya mata buqatanta tsawon wata 8 zata iya neman ya sawwaqe mata (Daga minti 26 zuwa minti 27)
- Shin manomi zai fara cire zakkar amfanin gona ne, ko kudin girbi da farko? (Minti 27 zuwa 28).
- Mutum zai iya sallar istikhara sau biyu a rana (minti 28 zuwa minti 29)
- Ya halatta amfani da laya don maganin ciwon kai (minti 29 zuwa minti 33)
- Falalar Azumin Litinin da Al-khamis (Minti 33-34)
- Wanda ya yi sallah bayan awa 4 sai ya tuna ba yi da tsarki, yaya zai yi (minti 34-35)
- Mai janaban dake jin tsoron mura ko rashin lafiya- zai iya taimama? (minti 35-37)
- Shin takalmanan da ake nunawa na Manzon Allah ne?(minti 37 zuwa qarshe)
Download
Leave a Reply