Shimfida: Nasiha akan abubuwa guda hudu in mutum yana da su to mutum bai rasa komai na duniya ba!
Tambayoyin dake ciki:
- Hukuncin azumin mutumin da yake saduwa da matarshi, aka kira sallar alfijir, bai dakata ba, yana qiyasin halin shi da mai cin abincin lokacin da aka kira sallar alfijir.
- Matsayin kabbarar da mutane keyi yayin raka gawa makabarta.
- Shin ya inganta tawassali da hatimin Annabi (saw)?
- Shin da gaske ne “hajarul aswad” zunubai ne ya baqanta shi? Kuma yaya tarihin zuwan shi duniya daga aljanna?
- Mainene ma’anar mutuwar shahada? Shiga aljanna ko kubuta daga azabar qabari?
- Shin Mala’iku ma za su mutum kamar yadda sauran hallitu suke mutuwa?
- Shin ana ganin Allah a mafarki?
- Bayanin aya ta 105 na Sura al-Ma’ida
يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنوا عَلَيكُم أَنفُسَكُم لا يَضُرُّكُم مَن ضَلَّ إِذَا اهتَدَيتُم إِلَى اللَّهِ مَرجِعُكُم جَميعًا فَيُنَبِّئُكُم بِما كُنتُم تَعمَلون
- Bada kyautar koda ma Malami da ke fama da rashin lafiya zai iya sadaqatul jariya?
- Hallacin cin naman maisa!
- Shin ana rama sallar shaf’i da witri?
- Wai in mutum ya fara azumin litinin da al-khamis ba a daina wa?
- Shin ana bayyana karatun raka’taiyil fajr da tahiyyatul Masjid?
- Nasiha ga mahaifi mai yawan fushi da fada ma wani dan shi, alhali ba ya mu’amalanta sauran yaran sa a bisa haka!
- Shin daidai ne mutum ya shiga ban daki da AirPod a kunneshi yana sauraron wa’azi ko karatun al-qur’ani?
- Shin yaya ingancin cewa wanda yayi sallah shi kadai a sahu, sai ya sake?
- Akwai falala a daura aure a watan Shawwal?
- Akwai adduo’i saboda yawan musiba?
- Bayanin nafilolin da ake bayyana karatu da kuma wadanda ake boye karatu!
- Iyaye suna da laifin in suka qi taimaka ma yaron su yayi aure har sai ya kammala karatu.
- Shin mutum zai iya sadaqa domin isar da ladan ga mahaifansa da ‘yanuwan sa!
- Shin matafiye zai iya hada sallolin qasaru (kamar azahar da la’asar) ko da yana masaukin sa, ba kan hanya ba?
- Shin ana iya duba kalanda ko agogo domin sanin lokacin sallah?
Download
Leave a Reply