Fina – Finan Hausa Tsakanin Gaskiya Da Karya(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Na dade ina karantawa
kuma ina jin
maganganun masu goyon bayan fina – finan
hausa a wannan lokaci,
musamman ma bayan
sun sa kafar wando daya
da malam Rabo, sai dai
abin takaici mafi yawan wadannan maganganu
fadarsu kawai ake,
amma ba haka suke ba,
don haka na ga ya dace
ni ma in ba da
gudummawata ta hanyar tunatar da masu
wadancan maganganu
gaskiyar hakikanin
wadannan fina – finan
hausar, don su sake
nazari akan abin da suke fada.
Fadakarwa Da Tarbiyya
A Cikin Fina – finan
Hausa.
Da farko sukan ce ai fina
– finan hausa fadakarwa ne da tunatarwa, suna
taimakawa wajen
tarbiyar mutane, da
sauran wadannan
maganganu. Haka suke
fada. Amma Alal hakika wannan magana ce
kawai, domin duk mai
hankali ya san barnar da
wadannan fina – finan
hausar suka kawo cikin
al’ummarmu ta ninka abubuwan da suka
koyar na alheri – in ma
sun koyar din, mu dauki
harkar raye – raye mu
gani, kafin zuwan
wadannan fina – finan duk wakar da zaka ji
yara na yi, waka ce mai
kyau, mai manufa, tana
koyar da halaye da
dabi’u nagari, sabanin
yanzu babu wata waka da zaka ji a bakin yara
sai wakar soyayya da
take dauke da wasu
kalmomi wadanda babu
yadda a da zaka ji irin
wadannan kalmomi a bakin yara. A yanzu za
ka ga yarinya karama
‘yar shekara biyar tana
tafiya tana rawa, tana
murguda jiki, kamar
yadda ta ga ni ana yi a fim, har ma wani sa’in
zaka ga tana bin wani
yaron karami namiji don
su yi tare, saboda haka
ta ga ana yi a fim, ganin
mutane suna ganin ta ba zai sa ta daina ba,
saboda a fim ma maza
da mata ake nuno wa
suna rawa tare. Ina
koyar da tarbiyya a nan!.
Waka A Cikin Fim Kafa hujja da cewa ai
tun kafin fina – finan
hausa bahaushe yana
waka a tatsuniya,
wannan ba hujja ba ce,
saboda wakar tatsuniya waka ce mai tsari, da
take dauke da ma’anoni
masu kyau, sannan babu
inda bahaushe a
tatsuniya yake cewa “sai
suka shiga lambu suna waka suna rawa, yana
cewa ina sonki tana
cewa ina sonka, matso
kusa da ni…”. Waka ce
kawai akan ambata
wane ya yi waka, ko wance ta yi waka ta ce
kaza.
Tarbiyya A Fina – finan
Hausa
Sannan yaya za a yi
wadda ta ki zaman aure, ta fito bayan ta kashe
aurenta za ta koya wata
tarbiyya? Inda tana da
tarbiyyar ai babu abin da
yafi ga ‘ya mace irin
gidan mijinta, kamar yadda bahaushe yake
fada, wadannan ‘yan
mata na fim, tarihinsu a
bayyane yake, saboda
yadda ake terere da su a
mujallu da jaridu da kafafen yada labarai. To
ta yaya wanda bai da
abu zai ba da shi, ashe
ba a Kanon nan ba ne
aka wayi gari ‘yar fim
tana tafiya a kan titi tana tangadi saboda
kayan maye da ta sha?!,
har ma aka kawo
rahoton ta a gidan
radiyo, ashe ba mafi
yawan ‘yan matan fim ba ne bincike ya nuna
suna yawace – yawacen
banza ba!? har ma a
wannan jarida tamu mai
farin jini malam gizago
ya yi sharshi mai kyau a kan gwagwaren
industry, in da ya fadi
abin da ya hana auren
wance (‘yar fim) da
wane (dan fim) da
wance (‘yar fim) da wane (dan fim),
wadannan su ne za su
bada tarbiyya!. Ashe ba a
daya daga cikin mujallan
da suke buga abin da ya
shafi ‘yan wasan hausa ba aka buga hoton wata
‘yar fim duk sassan
jikinta a waje, har wani
yake mata nasiha a cikin
wannan jarida tamu da
ta ji tsoron Allah. Yan uwa misalan suna da
yawa, kuma duk mai
bibiyar lamarin ya san
su, to ta ina za a samu
tarbiyya. Hausawa dai
tun tuni sun ce, “kowanne tsuntsu kukan
gidan su yake yi”.
KALU – Balen Masu Cewa
Fim Tarbiyya yake
koyarwa
Sannan ina tambayar masu cewa ai tarbiyya
da fadakarwa suke, ina
tarbiyya a cikin fim din
gidauniya, guda,
budurwa, tururuwa,
jarin Ibro, Ibro aloko, gishiri, da sauransu, na
kalubalanci masu cewa
fina – finan hausa
tarbiyya suke koyarwa,
su fada min fim din
hausa daya tak da abin da ya kunsa na tarbiyya
ya fi abin da ya kunsa na
rugaza tarbiyya, domin
duk fim din da aka yi irin
wadannan wake – wake
da raye – raye tsakanin maza da mata to ya
ruguza duk wani sako da
yake so ya aika, saboda
masu kallon wannan fim
din, wadanda ake cewa
su ake yi wa tarbiyyar babu abin da yake
danfarewa a cikin
kwakwalwarsu a yayin
da suka kalli fim sai
wadannan abubuwan na
wake –wake da raye – raye.

5 responses to “Fina – Finan Hausa Tsakanin Gaskiya Da Karya(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)”
  1. Which leads me to another thing – installing plug-ins and extensions.
    However, if you are planning to use Word – Press as CMS
    of your organization then it is desirable to have an idea about essentials of custom theme development.
    Some designs need additional extensions to become utilized.

  2. […] Fina – Finan Hausa Tsakanin Gaskiya Da Karya(Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo). […]

  3. SANI ISMAIL Avatar
    SANI ISMAIL

    May Allah bless ur efforts
    Ameeen

  4. moustapha yaro Avatar

    allah yabamu ikon tuba da gagawa kapin mutuwa kuma ya ciyar damu tsoronsa

  5. BIGARI Avatar
    BIGARI

    Allah ya kyauta

Leave a Reply to moustapha yaroCancel reply

Latest updates
Categories