Alhamdu lillahi rabbil A’lamin,
Wa sallallahu wa sallama ala
Nabiyyina Muhammad wa ala alihi wa
sahbihi ajma’in.
Amma ba’ad;
Lallai wanda yake son Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama zai fifita
shi akan duk abin da yake da girma
ko daraja ko tsada a gunsa. Domin
son Allah da manzonsa sune imani,
kuma imanin bawa bazai cika ba sai
da su. Allah subhanahu wa ta’ala
yace:
“ kace idan har iyayenku da
‘ya’yanku da ‘yan uwanku da
matanku da danginku da dukiyar da
kuka tsuwurwurta da kasuwancin da
kuke jin tsoron tasgaronsa da gidaje
da kuke yarda dasu sune suka fi
soyuwa a gareku daga Allah da
Manzonsa da jihadi saboda Allah ;to
ku zauna har Allah ya zo da
al’amarinsa, allah baya shiryar da
fasikai” {Tauba :24}
Wannan ayar nassi ce karara a bisa
wajibcin kaunar Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama,da
wajibcin gabatar da wannan kaunar
akan duk wani abin kauna.
Alkali Iyadh yace: “wannan ayar ta
isa wajen zaburarwa da fadakarwa da
shiryarwa da zama hujja ta gaske a
bisa wajibcin kaunar Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama da
cancantarsa da wannan soyayyar,
domin Allah ya kwankwashi wadanda
dukiyarsu da iyalansu da ‘ya ‘yansu
suka fi soyuwa a garesu fiye da Allah
da manzonsa,kuma yayi musu narko
cewa su jira har Allah ya zo da
al’amarinsa,sannan ya fasikantar da
su, ya kuma sanar da su cewa sun
bacewa hanya madaidaiciya, Allah ba
zai shiryar da su ba.
Hakanan kuma wanda ya yi la’akari
da wannan ayar zai ga cewa umarnin
bai tsaya ga samuwar soyayya ga
Allah da Manzonsa kadai ba, barima
dai dole ne sai wannan son ya zama
sama da son duk wani abu wanda ba
su ba.
Wa sallallahu wa sallama ala
Nabiyyina Muhammad wa ala alihi wa
sahbihi ajma’in.
Leave a Reply