Hanyoyin samun kariya daga sihiri da Aljani

Danna nan domin shiga karatu Online

Maqala

Kamar yadda yake Aqeeda ta Ahlussunah shine cewa Sihiri gaskiya ne, amma baya tasiri da kansa sai da yardar Allah, kamar yadda Allah ya bada labari acikin Suratul baqara ayah ta 102

Kuma bazasu iya cutar da kowa dashi ba sai da izinin Allah

Ma’ana masu sihiri basu iya cutar da mutum sai Allah yaso, sabida haka Musulmi mai cikakken Imani baya tsoron masu sihiri duk da cewa yasan sihiri gaskiya ne.

Yasan cewa duk abinda ya sameshi daga Allah ne.

Toh inhar ya zamto cewa shi sihiri baya shafar mutum sai da izinin Allah toh ai bai dace Musulmi ya ɗaga hankalin sa ba, har ya kaiga jefa kansa ga halaka wurin yin abubuwa wanda basu dace ba domin neman kariya daga sihiri, abinda kawai ya dace yayi shine yabi abinda Allah da Manzonsa sukace ayi domin samun kariya. Wanda wannan shine zamuyi bayaninsa a taƙaice.

Mu sani cewa baya halatta mutum yaje wurin boka domin neman ya bashi wasu abubuwa wa’inda zasu kareshi daga sihiri, irin Laya ko guru da makamantansu. Wannan yana daga cikin shirka.

anan ƙasa zamu kawo muku hanyoyin kariya a taƙaice ba tare da kawo nassoshi ba. Maison neman faɗaɗawa zai iya duba Littafin “Assarimul Battar” na Sheikh Abdussalam Wahid Bali daga shafi na 102.

Hanyoyin kariya daga Sihiri:

  1. Mutum yaci dabinai guda bakwai, irin baƙaƙen dabinannan ƴar Madina da ake kiranta Ajwah.
  2. Lazimtar Zikirin safe da yamma
  3. Yin alwala: mutum ya kasance yana yawaita zama cikin tsarƙi domin hakan na bada kariya.
  4. Kiyaye Sallah cikin Jam’i
  5. Tsayuwar dare
  6. Neman tsari yayin shiga bayan gida
  7. Neman tsari yayin shiga Sallah
  8. Alwala kafin bacci
  9. Faɗin La’ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu wahuwa Ala kulli shai’in kadir” sau ɗari safe da yamma
  10. Faɗin Bismillahillazi la ya durru Ma’asmihi shai’un fil ardi wala fissama wahuwa ssami’ul alim” sau uku safe da yamma
  11. Faɗin “A’uzi bikalimatillahit-tammat min sharri ma khalaka” sau uku safe da yamma.

Wannan kaɗan daga cikin hanyoyi kenan na neman kariya daga sihiri da shaiɗanu, ba dole sai mutum yayi su duka ba, mutum zai iya yi gwargwadon ikonsa.

Amma abu mai matuƙar mahimmanci da ya kamata Mu sani shine, Zikirin safe da yamma yana da matuƙar mahimmanci sosai, wanda inda Musulmi yasan mahimmancin sa da kuma kariya da yake bashi da bai barshi ba koda na kwana ɗaya ne.

Idan mutum ya kiyaye wannan zikirorin ya kuma ƙaurace wa saɓon Allah toh haƙiƙa Allah zai ƙareshi daga kowani irin sharri, kuma zaiyi rayuwa rayuwa mai ɗaɗi domin da Ambaton Allah ne da yimasa biyayya ake samun natsuwa. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates