HUJJAR AHLUS SUNNAH A KAN RASHIN YIN KUNUTIN DIN-DIN- DIN NA SALLAR ASUBA(Dr.Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga karatu Online

‘Yan’uwa Musulmi masu daraja! Lalle
Ahlus Sunnan da ba sa karanta
Kunutin din-din-din na Sallar Asuba
suna yin hakan ne saboda riko da
Sahihiyar Sunnah ba wai saboda son
zuciya ko neman kare girman wani
jagoran wata bidi’ah ba. A wannan
dan takaitaccen bayani zan ambaci
Hadithai biyu ne kacal masu ingancin
isnadi, muna kuma fata Al’umma za
su gamsu:-
1- Imam Ibnu Khuzaimah ya ruwaito
hadithi na 619, cikin Sahihinsa, da
kuma Imamut Tabarii hadithi na 2598
cikin Tahziibul A’athar, daga Sahabi
Abu Hurairah Allah Ya kara masa
yarda ya ce:-
((ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻻ ﻳﻘﻨﺖ ﺍﻻ
ﺍﻥ ﻳﺪﻋﻮ ﻻﺣﺪ ﺍﻭ ﻳﺪﻋﻮ ﻋﻠﻰ ﺍﺣﺪ)).
Ma’ana: ((Lalle Annabi mai tsira da
amincin Allah ya kasance ba ya yin
Kunuti sai dai in zai yi wa wani
addu’ar alheri, ko kuwa zai yi wa wani
mugunyar aduu’a)). Wannan Hadithi
Shaikul Al’azumii ya inganta shi.
2- Imamut Tirmizii ya ruwaito hadithi
na 402 cikin Sunan, daga Abu Maalik
Al’ashja’ii ya ce:-
(( ﻗﻠﺖ ﻻﺑﻲ ﻳﺎ ﺍﺑﺔ! ﺍﻧﻚ ﻗﺪ ﺻﻠﻴﺖ ﺧﻠﻒ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺍﺑﻲ ﺑﻜﺮ ﻭﻋﻤﺮ
ﻭﻋﺜﻤﺎﻥ ﻭﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﻫﻬﻨﺎ ﺑﺎﻟﻜﻮﻓﺔ ﻧﺤﻮﺍ
ﻣﻦ ﺧﻤﺴﻴﻦ ﺳﻨﺔ، ﺍﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻘﻨﺘﻮﻥ؟ ﻗﺎﻝ: ﺍﻱ ﺑﻨﻲ !
ﻣﺤﺪﺙ)).
Ma’ana: ((Na ce wa babana: Ya Baba!
Lalle kai ka yi salla bayan Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah, da
Abu Bakar, da Umar, da Uthman, da
Aliyyu Dan Abii Taalib a nan Kufah
kusan shekara hamsin, ko sun kasance
suna yin Kunuti? Sai ya ce: Ya kai
Dana, ai bidi’ah ce)). Wannan Hadithi
Albaanii ya inganta shi.
*************************
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah
ya ce cikin littafinsa Majmuu’ul
Fataawa 22/372:-
(( ﻭﺍﻟﺬﻱ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻤﻌﺮﻓﺔ ﺑﺎﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻧﻪ ﻗﻨﺖ
ﻟﺴﺒﺐ ﻭﺗﺮﻛﻪ ﻟﺰﻭﺍﻝ ﺍﻟﺴﺒﺐ)).
Ma’ana: ((Abin da dai Masana ilmin
Hadithi ke kansa shi ne: (Shi dai
Annabi) ya yi Kunuti ne saboda wani
dalili, kuma ya bar yin Kunutin
saboda gushewar dalilin)).
*******************
To amma idan wani ya ce: Ai Imam
Ahmad ya ruwaito hadithi na 12679
cikin Musnad daga Sahabi Anas Dan
Maalik cewa:-
(( ﻣﺎ ﺯﺍﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻨﺖ
ﻓﻲ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺣﺘﻰ ﻓﺎﺭﻕ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ)).
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah bai gushe ba yana yin
Kunuti cikin Sallar Asuba har ya bar
Duniya)).
Sai mu ce da shi: wannan Hadithi ba
zai cancanci a kafa hujja da shi ba,
saboda hidithi ne mai rauni. Imamul
Albaanii ya ce cikin Silsilah Sahihah a
karkashin lambar Hadithi na 5574:
Hadithi ne munkari ba ya inganta.
Haka nan shi ma Sheik Shu’aibul
Arnaa’ut ya ce hadithi ne dha’iifi.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “HUJJAR AHLUS SUNNAH A KAN RASHIN YIN KUNUTIN DIN-DIN- DIN NA SALLAR ASUBA(Dr.Ibrahim Jalo Jalingo)”
  1. […] HUJJAR AHLUS SUNNAH A KANRASHIN YIN KUNUTIN DIN-DIN-DIN NA SALLAR ASUBA(Dr.Ibrahim Jalo Jalingo). […]

Leave a Reply

Categories
Latest updates