Tambaya: Menene Hukuncin tafiya da takalmi a cikin maƙabar ta?
Amsa: Sunnah ga wanda ya shiga maƙabarta shine ya cire takalmin sa, Amma idan acikin Maƙabartar akwai ƙaya wanda zai cutar dashi to babu laifi ya sanya takalmin sa, saboda lalura
An Tambayi Maluma na Fatawa ta Lajnatud-da’ima shin cire takalmi idan aka shiga maƙabar ta Sunnah ce ko bid’ah sai suka ce:
An shar’anta wa wanda ya shiga maƙabarta ya cire takalman sa, saboda Hadisi da Aka rawaito Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam yaga wani mutum ya shiga maƙabarta da Takalmin sa, sai ya umar ce shi ya cire.
Fatawa Lajnatud-daimah: 9/123-124
Sheikh Ibnu Uthaymeen Allah ya masa Rahama yace:
Tafiya da takalmi tsaƙanin Ƙaburbura tsaɓanin Sunnah ne, abinda yafi wa Mutum shine ya cire takalman sa idan yana tafiya tsaƙanin ƙaburbura, sai dai idan akwai wata buƙata ta sanya takalmin, kaman akwai ƙayoyi acikin maƙabartar ko tsananin zafin rana, ko ƙananun duwatsu da zasu cutar da mutum, to anan babu laifi ya sanya takalmin sa yayi tafiya acikin ƙabari.
Majmu’u Fatawa Ibnu Uthaymeen: 17/202
Leave a Reply