(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَإٍ فَتَبَيَّنُوا أَنْ تُصِيبُوا قَوْمًا بِجَهَالَةٍ فَتُصْبِحُوا عَلَىٰ مَا فَعَلْتُمْ نَادِمِينَ).
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma.
[Surat Al-Hujraat 6]
Bismillahirrahmanirraheem.
Abin yana matukar damuna kuma Yana Daga min hankali ta yadda a kullum nake ganin musulmai zuciyarsu ta ta’allaka da gidajen labaru na wannan zamani tamu wanda yawancinsu makaryata ne kuma duk wani abinda ya shafi addinin musulunci so suke su Canza masa kamanni su Laqaba mishi Mummunan Suna da mummunan sura. Kuma duk wata mummunan aiki da akayi da sunan musulunci an rinka
yayatashi kenan amma haryanzu musulmai sun kasa gane me sukeyi duk abinda aka fada musu yarda sukeyi ba tare dayin bincike ba wanda wannan ta tsabawa koyarwar addinin musulunci, ko musulmi ne ya kawo maka labari addinin musulunci ya koyar damu damu bincika gaskiyarta tukunna, toh ina ga kuma wanda ba musulmi ba? Ya dace musulmi ya zama wayayye kada ya zama kidahumi komai aka fada masa yabi. Kirata ga dukkan ‘yan’uwa shine mu kiyaye bakunanmu da fadin komai da muke ji ko muke karantawa har sai munsamu yaqini cewa gaskiya ne. Yawancin mutane da kakeji yau ake ce musu ‘yan ta’adda agidajen labarai inda zqkaje ka bibiye yadda suke sai ka sami akasin haka, sannan meyasa sai abu ya shafi addinin musulunci tukunna za’a dinga danganashi da ta’addanci? Yanzu irin zalunci da akeyi wa musulmin burma kana jinsa a labarai? Kana jin America da kawayenta da majalisan dinkin duniya suna magana akai? Mutanen da aka hanasu shaidan zama ‘yan kasa, kullum kuma ‘yan addinin budha kashesu sukeyi, amma bazaka taba jin labaran wa’innan ‘yan addinin budha ana cemusu ‘yan ta’adda ba. Haka nan kasar isra’ila kullum tana kame palastinawa ta kashe na kashewa ta kuma rusa gidajensu amma bazaka taba jin irin wa’innan labari ba, kuma baza’a kirashi da ta’addanci ba. Amma inda musulmi zai kashe mutum daya da sunan musulunci koda ko ba Wakiltar al’ummar musulmai yakeyi a wannan kisa da yayi ba, ka rinka jin ana yayata wannan labari kenan ba kakkautawa. Ya dace mu natsu musan me mukeyi. Abinda bamu da Hakikaninsa mudaina Yarda dashi har sai mun sami dalili, hakanne zai tserar damu gaban Allah. Domin duk abinda muke fada yana nan ajiye yana jiranmu muzo muyi bayaninsa.
Wassalamu alaikum.
Leave a Reply