A wannan zamani namu da yawa daga cikin mutane zaka samesu suna mance wa da Allah a lokacin da suke buƙatan wani abu, sai dai su fara lissafi wa nake dashi? Nasan wane! Toh wannan yana daga cikin raunin imani, domin shi mumini a kullum ya kamata ya sanya imaninsa da ƙarfin gwiwansa baki ɗaya ya zamto a wurin Allah yake ba a wurin wani mahaluƙi ba, domin duk abinda kaga ka samu Allah ne ya baka, babu wani wanda yake da dama ya hana ka, ko kuma ya baka sai indai Allah ne yasa ya baka, ko ya hanaka, toh in ya zamto ainahin tsotson arziki da komai a wurin Allah yake toh bai dace ka karkata zuwa ga wani ba Allah ba. Yana daga cikin haƙiƙanin imani a samu mutum yana da cikakken tawakkuli ga Allah maɗaukakin sarki domin shine rayayye wanda baya mutuwa, amma duk wanda zaka kama kayi aikin banza, domin zai iya mutuwa, ko kuma yana raye ma ya kasa biya maka buƙatunka. Allah yace
وتوكل على الحي الذي لا يموت.
Ka dogara da wanda yake rayayye wanda baya mutuwa.
Allah shi kaɗaine wanda inka dogara dashi bazai taɓa baka kunya ba, koda ko bai baka abinda kakeso ba a lokacin da kakeso, inkayi haƙuri zaka fahimci hana ka da yayi sabida wata hikima ce tasa.
Kada ka kalli mutane da abin da Allah ya basu, ka dogara da Allah, kayi iya ƙoƙarinka wurin sama wa kanka mafita cikin lamuranka.
Allah maɗaukakin sarki yana cewa:
فابتغوا عند الله الرزق واعبدوه واشكروا له إليه ترجعو
Ku nemi Arziƙi awurin Allah, ku bauta masa, sannan ku gode masa, zuwa gareshi zaku koma.
Duk wanda Allah ya datar dashi da barin roƙon mutane, da kuma kwaɗayin abinda ke hanunsu toh Haƙiƙa ya samu gagarumin nasara a rayuwarsa, domin zai samu kwanciyar hankali da kuma kare mutuncinsa.
Sabida girman wannan lamari Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana karɓan mubaya’ar sahabbansa kan cewa kada su roƙi kowa komi. Har ya kasance ɗaya daga cikinsu sandansa zata faɗi daga kan abin hawansa baya tambayar wani ya ɗauka masa, sai dai ya sauƙo ya ɗauka. Sabida kada ya dogara da wani.
Haka akeso mumini ya kasance. Mai ɗauƙaƙa, ba ƙasƙantacce ba. Yana ƙoƙari kullum wurin warware matsalolin sa ba tare da wani ya sani ba. Sannan in ya shiga damuwa baya yaɗa ta kowa ya sani. Yana roƙon Allah ya yaye masa, kuma baya kai kukansa zuwa wurin wani ba Allah ba.
Leave a Reply