Hakika wanda yakeson cigaba a rayuwarshi, kuma yakeso ya cimma burinsa dole ne ya kauce wa ɗebe tsammani, ya kuma lazimci sa ran cin nasara da kuma kyautata zato ga Allah, sannan yayi iya ƙoƙarin sa kada ya gaza, sannan ya samu jajircewa. Da haka ne mutum zai samu cimma burinsa.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
المؤمن القوي خيرٌ وأحبُّ إلى الله من المؤمن الضعيف، وفي كلٍّ خير، احرص على ما ينفعك، واستعن بالله ولا تعجز، وإن أصابك شيء فلا تقل لو أنِّي فعلت كان كذا وكذا، ولكن قل قدَّر الله وما شاء فعل، فإنَّ لو تفتح عمل الشيطان
Mumini wanda imaninsa ke da ƙarfi yafi alheri kuma yafi soyuwa zuwa ga Allah fiye da Mumini wanda imaninsa ke da rauni, amma dukansu akwai alheri acikinsu. Ka kwaɗaitu zuwa ga abinda zai amfaneka, ka nemi taimakon Allah kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada kace da ace nayi kazaa da kazaa ya faru. Kai dai kace: Allah ne ya ƙaddara, kuma abinda yaso yake aikata wa. Domin Lau(da ace) tana buɗe ƙofar shaiɗan.
Muslim: 2664
A wannan hadisin Annabi ya nuna mana cewa a kullum Musulmi ya rinƙa duba abinda zai amfane shi, ya kuma kauce wa duk wani abu da bashi da amfani. Yayi iya ƙoƙarin sa wurin cimma burinsa na alheri, in Allah ya taimake shi ya cimma toh sai yayi godiya. Inkuma aka samu akasi ya guji yin tunani da nadama da bashi da amfani kan abinda bashi da daman canza wa. Ya nemi Allah ya canza masa da wanda yafi alheri sannan ya miƙa wuya zuwa ga hukuncin Allah.
Leave a Reply