Yana daga cikin laddubar ranar idi:
- Anaso Mutum yayi wanka ya sanya tufafinsa mai kyau yayi ƙwalliya a lokacin da zai fita zuwa sallan idi
- Anaso aci dabino ko wani abin ci kafin a fita zuwa sallar idin azumi, sannan kuma ana so a kame baki a Sallar idin lahiya har sai an dawo daga sallah.
- Yin kabbarori: Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar, La’ilaha illallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar Allahu Akbar Walillahil Hamd. Ana fara yin wannan kabbarorinne a Sallar azumi da zarar Rana ya faɗi na ƙarshen ranar azumi, har zuwa a kammala sallar idi ko kuma zuwa fitowar liman. a Sallar idin Lahiya kuma ana fara wa ne da zarar anshiga watan dhul hijja har zuwa ranar goma sha uku.
- Gaisuwa da kuma fatan alheri: anaso ayi gaisuwa tsaƙanin Musulmai da kuma fatan alheri, kamar ace Allah ya amsa mana da dai makamantansu.
- Kai ziyara: anaso a kai ziyara wa juna a ranar Idi, da kuma gaishe da juna
- Canza hanya lokacin tafiya da dawowa daga Sallar idi: anaso a canza hanya, a lokacin tafiya da kuma dawowa daga Sallar idi, hanyar da mutum ya tafi kada ya dawo ta wannan hanyar.
Allah ya amsa mana, ya kuma sa muyi bikin Sallah lafiya.
Leave a Reply