MA'ANAR SALAFIYYAH

Danna nan domin shiga karatu Online

By: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo



Ma’anar Salafiyyah shi ne: bin hanyar magabata; watau Sahabbai, da Taabi’ai, da Taabi’ut Taabi’iina, da Taabi’ut Taabi’it Taabi’iina wajen girmama Annabi mai tsira da amincin Allah, da barin maganar kowa a duk lokacin da ta yi karo da maganarsa, da nuna fashi da damuwa a duk lokacin da aka ga wani ya yi watsi da maganar; Saboda wannan matsayi lalle shi ne matsayin Sahabbai, da Taabi’ai, da Taabi’ut Taabi’iina, da Taabi’ut Taabi’it Taabi’iina. Ga misalai kadan na irin yadda Sahabbai suke girmama maganar Annabi, suke bin maganarsa sau-da-kafa, suke kuma nuna fushinsu a kan duk wani da ya ki bin maganarsa ya koma yana bin maganar waninsa:- 1. Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3093, da Muslim Hadithi na 1759 cewa babban Sahabi Sayyidina Abubakar As-Siddiq ya ce:-
((لست تاركا شيئا كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يعمل به الا عملت به فاني اخشى ان تركت شيئا من أمره ان أزيغ)).

Ma’ana: ((Ni ba zan bar yin wani abu da manzon Allah ya kasance yana yi ba face sai na yi shi, lalle ni ina jin tsoron cewa in na bar wani abu na umurninsa in karkata)). 2. Daaramiy ya ruwaito cikin Sunan Hadithi na 451 cewa babban Sahabi Ubaadatu Bin Saamit ya ambaci cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya hana a canja Dirhami biyu da Dirhami daya. Sai wani mutum ya ce: Ni ba na ganin laifin yin hakan matukar dai in aka yi shi hanu da hanu! Sai Ubaadatu ya ce:-
((أقول قال النبي صلى الله عليه وسلم وتقول: لا ارى به باسا؟ والله لا يظللني وإياك سقف أبدا)).
Ma’ana: ((Ina cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce Sannan kai kuma kana cewa: Ni ba na ganin laifi cikin yin hakan? Wallahi Inuwar wani rufin daki har abada ba zai hada ni da kai ba)). 3. Muslim ya ruwaito Hadithi na 1954 cewa akwai wani dan’uwa ga Sahabi Abdullahi Bin Mugaffal da ya jifa da tsakuwa ta hanyar kan farcen yatsar hannunsa, sai ya hana shi ya kuma ce da shi: Annabi mai tsira da amincin Allah ya hana yin jifa ta hanyar kan farce; ya ce: ba ya iya farautar dabbar daji, ba ya iya jiwa wani abokin gaba, amma kuma ya kan karya hakori ya kan kuma huda ido”. Sai mutumin ya sake yin jifar. Sai ya ce da shi:-
((أحدثك ان رسول الله صلى الله عليه وسلم نهى عنه ثم تخذف؟ لا أكلمك أبدا)).
Ma’ana: ((Ina gaya maka cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya hana yin jifa ta hanyar farcen yatsa sannan kuma ka koma yin jifar? Har abada ba zan yi magana da kai ba)). Ga kadan daga cikin misalan irin yadda Taabi’ai suke girmama maganar Annabi suke gabatar da ita a kan maganar kowa, suke kuma nuna fushinsu a kan duk wani wanda ya ki bin maganar ya koma ya bi wata maganar koma bayanta:- 1. Al-Mirwaziy ya ruwaito cikin littafin Sunnah athari na 94 cewa Taabi’i Umar Bin Abdil Aziz ya rubuta wa mutane ya ce
:- ((انه لا رأي لأحد مع سنة سنها رسول الله صلى الله عليه وسلم)).
Ma’ana: ((yadda lamarin yake shi ne: babu mutum daya da za a yi aiki da ra’ayinsa indai akwai sunnar da manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya sunnanta)). 2. Imamuz Zahbiy ya ce cikin littafin Taariikhul Islam 7/298, da littafin Siyaru a’alaamin Nubalaa 4/472 cewa Taabi’i Abu Qilaabah Abdullahi Bin Zaid ya ce
:- ((اذا حدثت الرجل بالسنة فقال: دعنا من هذا وهات كتاب الله فاعلم انه ضال)).
Ma’ana: ((Idan ka gaya wa Mutum Sunnah sannan sai ya ce: Raba mu da wannan ka kawo littafin Allah ka sani lalle shi batacce ne)). 3. Daaramiy ya ruwaito cikin Sunan Hadithi na 441 cewa Taabi’i Muhammad Bin Seerin ya karanta wa wani mutum hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah, sai mutumin ya ce: Wane ma ya ce kaza da kaza! Sai Ibnu Seerin ya ce
:- ((أحدثك عن النبي صلى الله عليه وسلم وتقول: قال فلان كذا وكذا؟ لا أكلمك أبدا)).
Ma’ana: ((Ina karanta maka Hadithi daga Annabi mai tsira da amincin Allah Sannan kai kuma kana cewa: wane ma ya ce kaza da kaza? Har abada ba zan maka magana ba)). Ga kadan daga cikin misalan irin yadda Taabi’ut Taabi’iina suke girmama maganar Annabi mai tsira da amincin Allah, suke gabatar da ita a kan maganar kowa, suna kuma sanar da kowa cewa: idan sun ga wata magana tasu ta saba wa maganar Annabi mai tsira da amincin Allah to su yi aiki da maganar Annabi su bar maganar tasu:- 1. Imam Abu Hanifah ya ce: ((Idan Hadithi ya inganta to shi ne mazhabata)). 2. Imam Malik ya ce: ((Ni ba kowa ba ne face mutum; ina yin kure ina kuma yin daidai, ku yi nazari game da ra’ayina dukkan abin da ya dace da AAlkur’ani da Sunnah ku rike shi, dukkan abin da bai dace da Alkur’ani da Sunnah ba ku bar shi)). 3. Imamush Shaafi’iy ya ce: ((Musulmai sun yi ijmaa’i a kan cewa duk wanda Sunnah daga manzon Allah mai tsira da amincin Allah ta bayyana a gare shi to ba ya halatta a gare shi ya bar ta saboda maganar wani mutum)). Ga kadan daga cikin misalan irin yadda Taabi’ut Taabi’it Taabi’iina suke girmama maganar Annabi mai tsira da amincin Allah, suke gabatar da ita a kan maganar kowa, suke kuma ganin cewa duk mai barin yin aiki da hadithin Annabi ya koma ya yi aiki da maganar wani to lalle wannan dan bidi’ah ne:- 1. Imam Abu Muhammad Al-Hasanul Barbahaariy ya ce cikin littafin Sharhus Sunnah athari na 105 shafi na 51
:- ((اذا سمعت الرجل يطعن على الاثار أو يرد الاثار فاتهمه على الاسلام ولا تشك انه صاحب هوى مبتدع)).
Ma’ana: ((Idan ka ji wani mutum yana sukan hadithai, ko yana watsi da yin aiki da hadithai to ka tuhume shi game da Musulunci kuma kada ka yi shakkar cewa shi ma’abucin son zuciya ne dan bidi’ah)). 2. Imam Ahmad Bin Hanbal yana cewa: ((Duk wanda ya ki yin aiki da hadithin manzon Allah mai tsira da amincin Allah to lalle yana kan gabar halaka)). Wannan shi ne ma’anar Salafiyyah, shi ne kuma manufa da aqidar dukkan wani musulmin kirki, amma mutumin da zai bar yin aiki da Hadithi a bisa hujjar cewa: maganar Sahabi wane, ko maganar Taabi’i wane, ko maganar Taabi’ut Taabi’iina wane, ko maganar Taabi’ut Taabi’it Taabi’iina wane ya saba wa maganar shi Annabin to lalle wannan battacden dan bidi’ah ne. Allah Ya taimake mu. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates