Mas'alolin Aure Fitowa ta 18(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

Bayani ya gabata akan nau’ikan
aure da dama wadanda shari’a ta
hana. TAMBAYA:
TAMBAYA:
Mene ne hukuncin auren dole a
Musulunci?
AMSA:
Babu auren dole a Musulunci bisa
dalilai mafiya inganci na maganar
malamai. Sai dai wadansu
malamai kamar Imam Malik da
Imamus Shafi’i da Ishak Ibn
Rahawaihi da daya daga cikin
fadin Imamu Ahmad sun tafi a kan
cewa uba zai iya aurar da `yarsa
ko da kuwa ba ta so, sun karfafi
maganarsu da hujjoji kamar haka;
1- An rawaito hadisi daga Urwatu
Ibn Zubair daga babansa daga
Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ce:
ﺗﺰﻭﺟﻨﻲ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻟﺴﺖ
ﺳﻨﻴﻦ ﻭﺑﻨﻰ ﺑﻰ ﻭﺍﻧﺎ ﺍﺑﻨﺔ ﺗﺴﻊ ﺳﻨﻴﻦ
Ma’ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya aure ni ina da shekara
shida, kuma ya tare da ni ina `yar
shekara tara.
Imamus Shafi’i (Allah ya ji kansa)
ya ce:
ﻭﻗﺪ ﺯﻭﺝ ﻋﻠﻰ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﺍﻡ ﻛﻠﺜﻮﻡ
ﺑﻐﻴﺮ ﺍﻣﺮﻫﺎ
Ma’ana:
Hakika Sayyadina Aliyu
radhiyallahu anhu ya aurawa
Sayyadina Umar radhiyallahu anhu
`yarsa Ummu Kulsum ba tare da
izininta ba.
Kamar yadda aka rawaito a cikin
hadisin Hasan Ibn Hasan daga
babansa cewa:
ﺍﻥ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ﺧﻄﺐ ﺇﻟﻰ ﻋﻠﻰ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻬﻤﺎ ﺍﻡ ﻛﻠﺜﻮﻡ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻧﻬﺎ
ﺗﺼﻐﺮ ﻋﻦ ﺫﻟﻚ ﻓﻘﺎﻝ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺳﻤﻌﺖ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻝ ﻛﻞ ﺳﺒﺐ
ﻭﻧﺴﺐ ﻣﻨﻘﻄﻊ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﺍﻻﺳﺒﺒﻰ ﻭﻧﺴﺒﻲ ﻓﺎﺣﺒﺒﺖ
ﺍﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻟﻰ ﻣﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺳﺒﺐ ﻭﻧﺴﺐ ﻓﻘﺎﻝ ﻋﻠﻰ ﻟﺤﺴﻦ ﻭﺣﺴﻴﻦ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻬﻤﺎ ﺯﻭﺟﺎ ﻋﻤﻜﻤﺎ ﻓﻘﺎﻻ ﻫﻲ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ
ﺗﺨﺘﺎﺭ ﻟﻨﻔﺴﻬﺎ ﻓﻘﺎﻡ ﻋﻠﻰ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻣﻐﻀﺒﺎ
ﻓﺄﻣﺴﻚ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺑﺜﻮﺑﻪ ﻭﻗﺎﻝ ﻻ ﺻﺒﺮ ﻋﻠﻰ ﻫﺠﺮﺍﻧﻚ
ﻳﺎ ﺍﺑﺘﺎﻩ ﻗﺎﻝ ﻓﺰﻭﺟﺎﻩ
Ma’ana:
Sayyadina Umar radhiyallahu anhu
ya nemi auren Ummu Kulsum a
wurin Sayyadina Ali radhiyallahu
anhu, sai Sayyadina Ali
radhiyallahu anhu ya ce masa: ai
ta yi kankanta, sai Sayyadina Umar
radhiyallahu anhu ya ce: na ji
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce: “Dukkan wani
sababi da nasaba abin yankewa
ne ranar Alkiyama, sai dai
sababina da nasabata”, don haka
nake son na hada nasabata da ta
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama , sai Sayyadina Ali
radhiyallahu anhu ya cewa
Sayyadina Hasan da Sayyadina
Husain ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ku aura wa
amminku (ita), sai suka ce: ai ita
mace ce daga cikin mataye tana
da zabin kanta, sai Sayyadina Ali
radhiyallahu anhu ya tashi cikin
fushi ya kama tufafin Sayyadina
Hasan radhiyallahu anhu, sai
Sayyadina Hasan radhiyallahu
anhu ya ce: ba zan iya jurewa da
fushinka ba ya babana (mun yarda
da abin da ka fada), daga nan sai
suka aura masa ita.
Imamus Shafi’i (Allah ya ji kansa)
ya ce:
ﻭﺯﻭﺝ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺍﺑﻨﺘﻪ ﺻﺒﻴﺔ. ﻭﺯﻭﺝ
ﻏﻴﺮ ﻭﺍﺣﺪ ﻣﻦ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺑﻨﺘﻪ ﺻﻐﻴﺮﺓ. ﻗﺎﻝ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﻜﺎﺡ ﻻ ﻳﺠﻮﺯ
ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺒﻜﺮ ﺍﻻ ﺑﺎﻣﺮﻫﺎ ﻟﻢ ﻳﺠﺰ ﺍﻥ ﻳﺰﻭﺝ ﺣﺘﻰ
ﻳﻜﻮﻥ ﻟﻬﺎ ﺍﻣﺮ ﻓﻲ ﻧﻔﺴﻬﺎ
Ma’ana:
Zubair Ibn Auwam radhiyallahu
anhu ya aurar da `yarsa alhali tana
`yar karama. Haka kuma mutane
da yawa daga cikin Sahabban
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama sun aurar da `ya`yansu
alhali suna kanana. Sannan ya ci
gaba da cewa: da aurar da
budurwa bai halatta ba sai da
izininta, da ba za a aurar da ita ba
sai da yardarta.
Haka kuma Imamus Shafi’i (Allah
ya ji kansa) ya fassara cewa:
ﻭﺍﻟﻤﻮﺍﻣﺮﺓ ﻗﺪ ﺗﻜﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﺳﺘﻄﺒﺔ ﺍﻟﻨﻔﺲ
Ma’ana:
Neman shawararta kan zama
dadada rai ne.
Sannan ya ci gaba da cewa: an
rawaito hadisi daga Abdullahi Ibn
Umar radhiyallahu anhu ya ce:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
ﻭﺍﻣﺮﻭﺍ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻲ ﺑﻨﺎﺗﻬﻦ
Ma’ana:
Ku nemi shawarar iyaye mata
dangane da `ya`yansu mata.
Kuma ya ce:
ﻭﻟﻢ ﻳﺨﺘﻠﻒ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻥ ﻟﻴﺲ ﻻﻣﻬﺎ ﻓﻴﻬﺎ ﺍﻣﺮ ﻭﻟﻜﻦ
ﻋﻠﻰ ﻣﻌﻨﻰ ﺍﺳﺘﻄﺎﺑﺔ ﺍﻟﻨﻔﺲ
Ma’ana:
Babu wanda yake da sabani a kan
cewa iyaye mata ba su da wani iko
sai dai ma’anarsa dadada rai ake
nufi.
Haka kuma an rawaito daga Imam
Ibrahimun Nakha’i ya ce:
ﺍﻟﺒﻜﺮ ﻳﺠﺒﺮﻫﺎ
Ma’ana:
Uba zai iya tilastawa `yarsa
budurwa.
Imamus Sha’abi ya ce:
ﻻ ﻳﺠﺒﺮ ﺍﻻ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪ
Ma’ana:
Babu wanda zai iya tilastawa
budurwa sai uba.
Haka kuma sun kara kafa hujja da
fadin Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama cewa:
ﻻ ﺗﻨﻜﺢ ﺍﻟﻴﺘﻴﻤﺔ ﺇﻻ ﺑﺈﺫﻧﻬﺎ
Ma’ana:
Ba a aurar da marainiya sai da
izininta.
Sai suka ce: wannan hadisin ya
nuna cewa, idan budurwa ce, za a
iya aurar da ita ba tare da izininta
ba.
Sai dai duk da wadannan dalilai da
suka kawo, Imamu Malik da
Imamus Shafi’i da Imam Ibn Abi
Laila sun ce:
Matukar akwai cutarwa
bayyananniya a cikin auren dole,
to, uba ba shi da ikon ya aurar da
`yarsa karama ko babba. Wannan
shine fadin Imamu Ahmad da
Imam Ishaq da ma’abota ilimi masu
yawa.
Magana ta biyu ita ce malaman da
suka ce auren dole bai halatta ba,
sun karfafi maganarsu da hujjoji
kamar haka;
Hadisi ya tabbata daga Abu
Huraira radhiyallahu anhu ya ce:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce:
« ﻻ ﺗﻨﻜﺢ ﺍﻷﻳﻢ ﺣﺘﻰ ﺗﺴﺘﺄﻣﺮ ﻭﻻ ﺗﻨﻜﺢ ﺍﻟﺒﻜﺮ ﺣﺘﻰ
ﺗﺴﺘﺄﺫﻥ .« ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻛﻴﻒ ﺇﺫﻧﻬﺎ ﻗﺎﻝ »
ﺃﻥ ﺗﺴﻜﺖ ».
Ma’ana:
Ba a aurar da bazawara sai an
nemi izininta da yardarta. Kuma ba
a aurar da budurwa sai da
yardarta. Sai Sahabbai suka ce: Ya
Rasulallahi sallallahu alaihi wa
sallama yaya yardarta za ta
kasance? Sai ya ce: Shirunta (shi
ne yardarta).
Babban malaminnan Ibn Athir ya
ce: fadin Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama game da
bazawara cewa: “A nemi izininta
da yardarta”. Hakan yana nufin
al`amarinta yana hannunta, sai ta
yarda kuma ta furta amincewarta.
Haka kuma neman yardar budurwa
ya zama dole, amma shirunta shi
ne izininta.
Haka kuma Imamut Tirmizi ya ce:
Maganar Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama cewa a nemi izini
da yarda daga bazawara yana
nuna cewa tana da hakki a
sha`anin auren ta fiye da
waliyyinta. Wannan kuma shi ne
ra`ayin mafi yawan malamai.
Saboda haka waliyyinta ba zai
aurar da ita ba, sai da yardarta tare
da amincewarta. Idan kuma ya
aurar da ita ba tare da izininta ba,
to, wannan auren batacce ne bai
inganta ba. Sannan ya kara da
cewa mafi yawan malamai a cikin
su akwai malaman Kufa da
sauransu sun ce:
Idan uba ya aurar da budurwa
bayan ta balaga ba tare da izininta
ba, kuma ba ta yarda da auren ba,
to, shi ma wannan auren batacce
ne bai inganta ba.
Haka ne ya sanya Imamul Bukhari
ya bude babi da fadin cewa: “Idan
mutum ya aurar da `yarsa alhali ba
ta so, to, auren abin mayarwa ne
(ma’ana auren bai dauru ba)”.
Sannan sai kuma ya kawo hadisin
Khansa’u Bint Khizam ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ
cewa:
ﺃﻥ ﺃﺑﺎﻫﺎ ﺯﻭﺟﻬﺎ ﻭﻫﻲ ﺛﻴﺐ ﻓﻜﺮﻫﺖ ﺫﻟﻚ ﻓﺄﺗﺖ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ ﻓﺮﺩ ﻧﻜﺎﺣﻪ
Ma’ana:
Hakika babanta ya aurar da ita
alhali tana bazawara, sai ba ta so
auren ba, sai ta je ta fadawa
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama , sai ya rushe auren.
Amma a ruwayar Imamus Sauri ya
nuna cewa: Khansa’u ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ,
budurwa ce ba bazawara ba ce.
Haka kuma Imam Abu Dawud ya
rawaito daga Abdullahi Ibn Abbas
radhiyallahu anhu cewa:
ﺃﻥ ﺟﺎﺭﻳﺔ ﺑﻜﺮﺍ ﺃﺗﺖ ﺍﻟﻨﺒﻰ -ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ –
ﻓﺬﻛﺮﺕ ﺃﻥ ﺃﺑﺎﻫﺎ ﺯﻭﺟﻬﺎ ﻭﻫﻰ ﻛﺎﺭﻫﺔ ﻓﺨﻴﺮﻫﺎ
ﺍﻟﻨﺒﻰ -ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ -.
Ma’ana:
Hakika wata yarinya budurwa ta zo
wurin Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama , sai ta ambata
masa cewa: babanta ya aurar da
ita alhali ba ta so, sai Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ba
ta zabi.
Wadannan ruwayoyin sun tabbatar
da cewa: idan aka aurar da
budurwa ba tare da yardarta ba, to,
auren bai dauru ba, rusasshe ne
har abada.
Dangane da aurar da karamar
yarinyar da ba ta balaga ba kuwa
sun ce: uba zai iya aurar da ita ba
tare da neman izininta ba, matukar
auren zai zamar mata maslaha nan
gaba, kuma ita kanta za ta yi lale
da wannan auren bayan ta yi
hankali, kamar yadda Imam Ibn
Munzir ya fada cewa:
Ma’abota ilimi sun hadu a kan
cewa, uba yana da ikon ya aurar
da `yarsa karama idan har wannan
mijin da za a aurawa, ya dace da
ita ta fuskar matsayi, wannan kuwa
ko da ba ta sonsa.
Sai dai Ibnu Hazmin ya ki
amincewa da wannan magana
inda ya ce:
Uba ba shi da ikon aurar da
yarinya karama, har sai ta balaga
kuma ya nemi yardarta.
Daga wadannan bayanai da suka
gabata za mu fahimci cewa, bai
halatta ba uba ya aurar da `yarsa
ko bazawara ko marainiya da ke
karkashinsa sai da yardarta. Amma
uba zai iya aurar da yarinya in har
ya samar mata miji mai matsayin
da ba kowa yake samu ba matukar
ba ta nuna cewa tana kin sa ba. A
nan uba zai iya aurar da ita don
moriyar da `yar za ta samu duniya
da lahira game da wannan mijin
kamar yadda Sayyadina Abubakar
radhiyallahu anhu ya aurar da
Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ga
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama alhalin tana karama. Kuma
ma wannan auren na Nana A’isha
ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ishara ce daga Allah
subhanahu wa ta’ala, domin an
nunawa Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ita a mafarki
cewa ga matarka, wanda kuma
mun sani cewa mafarkin
Annabawa wahayi ne.
Don haka ba dalilin da zai sa
mutum ya aurar da `yarsa karama
ga wanda ba ta so komai
dukiyarsa, domin ba a kiyasin
auren Nana Aisha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ da
sauran mata, domin ita Allah
subhanahu wa ta’ala ne ya zabe ta
kuma ya ba ta wannan matsayi.
Kuma mafi yawan auren dole, shi
yake kawo mutuwar auren mata
wanda yakan sa su fada ayyukan
fasadi da karuwanci da sauran
abubuwan da ba sa haifar da
alheri. Don haka muna nasiha ga
iyaye da su tabbata sun tarbiyantar
da `ya`yansu bisa tarbiyya ta gari,
a kuma zabar musu mazaje na
gari. Sannan a yi ta yi musu
addu`a wadda za ta amfane su
duniya da lahira, saboda
addininmu ya bayyana komai na
alherin duniya da lahira. Domin
rayuwar Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama da sahabbansa,
darasi ce a gare mu, wanda idan
mun rike su, za mu huta duniya da
lahira. Kuma yana da kyau mu sani
cewa, idan mun riki addininmu, sau
da kafa, da`awar da Turawan
yamma suke yi da sunan ci gaba
ko neman `yancin mata ko
wayewar kai ta banza, ba za ta
cutar da mu ba, domin mu ne a
gaba da su. Allah ya sa mu dace
amin.
TAMBAYA:
Shin baiko aure ne?
AMSA:
A`a! Baiko ba aure ba ne, sai dai
kawai al`ada ce ta wasu al’umma
da take nuna an tsayar wa mace
miji, tare da shelanta cewa za a
daura mata aure nan gaba. Kuma
wannan al`adar ta bambanta daga
kabila zuwa kabila. Sannan duk
wadanda suke yin baiko sun yarda
da cewa ba aure ba ne kuma ba su
taba cewa akwai gado a tsakanin
wadanda aka yi wa baikon ba idan
dayansu ya mutu kafin daurin aure,
kuma Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce:
ﺇﻧﻤﺎ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ ﺑﺎﻟﻨﻴﺔ
Ma’ana:
Dukkan ayyuka ba sa tabbata sai
da niyya…
Saboda haka ko da a yayin baiko
an sami sigar da take nuna
bayarwa da karba, tare da bayar
da ko ambaton sadaki da shaidu,
har yanzu bai zama daurin aure
ba, domin niyyar ta baiko ce ba ta
aure ba.
A nan muke nasiha ga `yan’uwa da
su guji tarawa da matan da aka yi
masu baiko da su da ikrarin cewa
matansu ne, domin ba su da wani
dalili a Littafin Allah ko sunnar
Manzonsa sallallahu alaihi wa
sallama ko abin da Shari’a ta yarda
da shi na hukuncin al`adarsu
wanda za su kafa hujja wurin
halatta abin da suke yi. Kuma babu
wani sabanin malamai a kan
wannan mas`ala. Saboda haka,
idan har suka kuskura suka yi
wannan danyen aiki, su tabbata
cewa ba komai suka yi ba face
zina. Ya kuma kamata su nemi
gafara wurin Ubangiji subhanahu
wa ta’ala.
TAMBAYA:
Menene hukuncin neman auren
mace bayan an tsayar mata da miji
ko an kusa ba shi ita?
AMSA:
Bai halatta mutum ya nemi aure a
cikin neman auren dan uwansa ba,
matukar yarinyar ta yarda da na
farko kuma waliyyanta sun amince
ya ci gaba da neman auren ta.
Domin hadisi ya tabbata daga Abu
Huraira radhiyallahu ya ce:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce:
… ﻭﻻ ﻳﺨﻄﺐ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻋﻠﻰ ﺧﻄﺒﺔ ﺃﺧﻴﻪ ﺣﺘﻰ ﻳﺘﺮﻙ
ﺍﻟﺨﺎﻃﺐ ﻗﺒﻠﻪ ﺃﻭ ﻳﺄﺫﻥ ﻟﻪ ﺍﻟﺨﺎﻃﺐ
Ma’ana:
… Bai halatta mutum ya yi neman
aure a cikin neman dan uwansa
ba, sai dai idan shi na farkon ya
janye ko kuma ya yi masa izini.
Haka kuma malamai sun hadu
akan cewa bai halatta mutum ya
nemi auren mace ba matukar
waliyyanta sun amince da wani.
Idan kuma mutum ya yi nema a
cikin neman dan uwansa har ya
auri yarinyar, a nan malamai sun yi
sabani a kan ingancin wannan
auren. Daya daga cikin kaulin
Imam Malik da Imam Ahmad da
Dawud Az-Zahiri da Ibn Taimiyya
sun ce wannan auren batacce ne,
bai inganta ba, dole ne a raba shi.
Dalilinsu kuwa sun ce: Duk abin da
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya hana haramun ne, duk
kuwa abin da ya zama haram, to,
ba shi da asali kuma aikata shi bai
inganta ba. Magana ta biyu kuma
ita ce maganar Jumhurun malamai
wanda suka hadar da Imam Abu
Hanifa da Imam Shafi’i da kuma
daya daga cikin kaulin Imam Malik
sun ce, auren ya inganta, sai dai
an sabawa Allah da Manzonsa
sallallahu alaihi wa sallama, sai a
tuba wurin Allah. Sun kawo
dalilansu kamar haka na farko shi
namijin shine Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya
hana nema a cikin neman wani,
kuma hanin ya tsaya a kan neman
auren ne kawai, ba wai ga daura
auren ba. Dalilinsu na biyu kuwa
sun ce: ai a asali, za a iya daura
aure ba tare da an yi nema ba,
matukar dai an sami amincewar
yarinyar da kuma angon, kuma
wannan ita ce magana mafi
rinjaye.
Allah datar da mu baki daya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “Mas'alolin Aure Fitowa ta 18(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)”
  1. Shuaibu Ahamed Yula Avatar
    Shuaibu Ahamed Yula

    Man city fc is real.

  2. kamalkima Avatar
    kamalkima

    Allah yasaka da alkhairi.

Leave a Reply

Categories
Latest updates