TAMBAYA
Wace addu`a ya kamata a yi wa
Ango da Amarya?
AMSA:
Addu`ar da ake yi musu ita ce:
ﺑﺎﺭﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻚ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻴﻚ ﻭﺟﻤﻊ ﺑﻴﻨﻜﻤﺎ ﻓﻲ ﺧﻴﺮ.
Ma`ana:
Allah ya sanya maka albarka,
kuma Allah ya sanya albarka a
cikin aurenka, kuma ya hada
tsakaninku da alheri.
Wannan addu`ar tana daga cikin
addu’o’in da suka tabbata daga
bakin Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ga al’ummarsa
idan sun yi aure.
TAMBAYA:
Yaya magabata na kwarai suke
gabatar da bikin aurensu?
AMSA:
Magabata na kwarai sun kasance
suna yin biki yadda shari’a ta yarda
da shi. Yana daga cikin tsarin
bikinsu, koyawa amarya yadda za
ta yi ado da sanya lalle da dukkan
kwalliyar da ta kamata. Domin
kamar yadda ya gabata, Ummu
Sulaim ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta yi wa Nana
Safiyyah ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ kwalliya ta
mika ta ga Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ranar tarewarta.
Sai dai a kiyayi yin ado da kaya
masu shara-shara, wadanda suke
bayyana al`aura ko dukkan
kwalliyar da ta sabawa shari`a,
kamar aske gashin gira, ko maza
su yiwa mata kwalliya, da dai
sauransu.
Haka kuma yayin da mata suke kai
amarya gidan mijinta, za su iyayin
wakokin da suka dace, wadanda
ba su sabawa shari`ar Musulunci
ba. Kuma ya halatta a yi kidan da
babu batsa a cikinsa, kamar kidan
shantu ko na kwarya da sauransu.
Domin hadisi ya tabbata cewa:
Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ da sauran
mata sun kai amaryar daya daga
cikin mutanen Madina. Sai Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya tambaye ta cewa:
… ﻳﺎ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﻌﻜﻢ ﻟﻬﻮ ؟ ﻓﺈﻥ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ
ﻳﻌﺠﺒﻬﻢ ﺍﻟﻠﻬﻮ.
Ma’ana:
Ya A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ wane irin
nishadi/wakoki kuke yi yayin kai
amaryar? Domin hakika mutanen
Madina sun kasance masu son
nishadi/wakoki ne.
Haka kuma a nisanci cakuduwa
tsakanin maza da mata yayin biki,
sannan a guji yin koyi da Kiristoci
wurin kai amarya, kamar sanyawa
amarya doguwar riga fara irin ta
Coci, da yi wa motar kai amarya
ado da fulawoyi ko balo-balo da
sanya wa amarya ko ango zobe da
yanka kek da tafiya bakin ruwa
(picnic) da yin rawa tsakanin maza
da mata wasu ma har suna lika
kudi da sauransu.
Kuma bai halatta ba a rika daukar
hotunan mata, musamman matan
aure a kyamara ko hoton bidiyo,
wanda yawanci suke caba ado tare
da bayyana tsiraici, wani lokaci ma
suna rawa a irin wannan hali marar
kyan gani, kuma wasu mutanen da
ba muharramansu ba suna kallon
wadannan hotunan. Wannan yana
nuna rashin kishin wasu mazaje.
Kuma a karshe yana sabbaba
bala`i na neman matan mutane da
dukkan nau`ika na alfasha. Dukkan
wadannan abubuwan da muka
lissafa sabawa Allah ne da
Manzonsa sallallahu alaihi wa
sallama. Don haka wajibi ne a
matsayinmu na Musulmi mu
nisanci dukkan nau’in maguzancin
Turawa da Kiristoci a wurin
bukukuwanmu.
Babban abin takaici shi ne irin
yadda ake yi ranar kai amarya,
amare da angwaye suke shagala
ga barin salla, musamman Sallar
Magariba da Isha`i da Asuba.
Wannan kuma babban laifi ne, don
bai kamata ba a ce ranar da
amarya za ta sanya kafa dakin
mijinta, ta kasance ta sabawa Allah
da Manzonsa sallallahu alaihi wa
sallama.
Haka kuma al`adar nan ta sayen
baki, ita ma ta sabawa koyarwar
Addinin Musulunci, saboda
cakuduwar da ake yi tsakanin
abokan ango da kawayen amarya
wadanda ba muharramansu ba, da
kuma abubuwan da suke yi
wadanda ba su halatta ba.
A karshe ya kamata a fahimci
cewa, dukkan al`adar da ta
sabawa Shari`ar Musulunci ba
abar yi ba ce. Don haka a nisance
ta, domin samun albarka da zuriya
ta gari da rabauta daga Allah
Madaukakin Sarki.
Bayan duk abubuwan da muka yi
bayani a baya, akwai wasu
bukukuwa da aka aro daga
Turawa, kamar bikin cika shekarar
aure (ana yanka kek), ko bikin
cikar shekarar haihuwa da
makamantansu. Duk wadannan
kwaikwayo da Yahudu da Nasara
ne, bayan kuma Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya
umarce mu da mu saba musu a
cikin ayyukanmu.
TAMBAYA:
Mene ne hukuncin saka hoton
ango da amarya a kalanda ko kati
tare da ayoyin Alqur`ani ko
hadisan Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama a rarrabawa
mutane?
AMSA:
Yin wadannan sabawa Shari`ar
Allah ne karara, da wulakanta
ayoyin Alkurani da hadisan
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama, da kuma jahiltar addinin
Musulunci tare da sabawa
kyawawan al`adunmu na gari da
muka gada.
Kuma wani babban abin bakin ciki
ma shi ne yadda za ka ga irin
wadannan hotunan masu dauke da
sunan Allah ko hadisan Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
an zubar da su a bola (juji) ko
kuma wurin kazanta bayan an
gama bikin . Wannan yana nuna
irin rashin kishin wasu mutanenmu,
ta yadda za ka ga an buga hoton
ango da amarya ta yi ado cikin
gwalagwalai da kaya masu
bayyana siffar jikinta. Tare da
haka, wasu ma har lambar
wayarsu suke sanyawa a jikin
hoton wanda wannan zai iya ba da
kofar wata fitina ta samu. Da fatan
Allah ya shirye mu baki daya.
Leave a Reply