Sheikh Muhammad Bn Saalih Al-Uthaymeen Allah ya jikansa da Rahama yana cewa:
Ni ina cewa, Mazhabin Ahlussunnah shine muyi shiru kan abinda ya auku tsaƙanin Sahabbai na fitintinu, kada mu tsoma bakinmu aciki, mu kautar da zuƙatanmu da kuma Harsunanmu kan abinda ya faru tsaƙanimsu na fitintinu muce: “Dukansu mujtahidai ne, wanda ya dace cikin ijtihadinsa yana da lada biyu, wanda kuma yayi kuskure yana da lada ɗaya” kuma su wasu Al’ummah ce wacce tariga ta gushe abinda suka aikata yana kansu, abinda mu kuma muka aikata yana kanmu. Kuma baza’a tanbayemu kan abinda suka aikata ba
Da mutum zai karanta tarihi kan wannan Lamari na fitintinu da suka auku tsaƙanin Sahabbai da yaga abin mamaki matuƙa, zai samu wanda yake goyon bayan Banu Umayyah yana kushe Aliyu bin Abi ɗalib da kuma Aalil-Bait, haka nan kuma zai sami maiyin guluwwi kan Aliyu bin abi ɗalib da kuma Aalil-Bait yana kushe banu umayya. domin shi tarihi yana bin siyasa.
Sharhin Riyadussaliheen na ibn Uthaymeen 2/281
A dalilin haka ya wajaba a kanmu kada muyi saurin yin hukunci, domin shi tarihi sau da dama ana samun karerayi acikinsa, sannan ana yawan samun son Zuciya da kuma canza Gaskiya, a yaɗa abinda ba haka yake ba, sannan kuma a share abinda yake shine gaskiya, duka domin bin siyasa, a kowani hali abinda ya wajaba akanmu shine mu kame ga barin yin suka kan ko wani ɓangare da wannan rikici ya shafa, kamar yadda yake shine Mazhabin Ahlussunnah, sabida kada a samu wani ƙulli da ƙiyayya acikin zuciyarmu kan wani daga cikinsu. Muna sonsu baki ɗayansu, kuma muna roƙon Allah ya kashemu muna masu sonsu, muna sonsu baki ɗayansu, kuma muna faɗi cewa “Allah ka gafarta mana tare da ƴan’uwanmu wa’inda suka gabace mu da imani, kada kuma ka sanya wani ƙulli ko gaba acikin zuƙatanmu kan wa’inda sukayi imani. Ubangijin mu kai mai Rahama ne mai jin ƙai”
Kaman yadda Sheikh Bin Uthaymeen ya faɗi acikin wannan littafi, wannan shine Aƙidan Ahlussunnah tun daa haryanzu, komai nasu tsaƙatsaƙiya yake, babu wuce gona da iri, sannan kuma babu sako sako. Kuma haka musulmi ya dace ya zama. Domin mutum yanzu yazo yana ruruta Wutan rikici tsakanin musulmi a wannan zamani domin abinda ya faru tsaƙanin Sahabbai a shekarun baya masu yawa, wannan ba hanya bace ta taimakon Addini ko kuma ta taimaka wa su wa’innan Sahabbai. Sannan kuma koda mutum mutuwa yayi Allah bazai tambaye shi kan meyafaru tsaƙanin Sahabbai ba, sabida Allah bai shar’anta mana sai mun sanshi ko kuma sai mun tsoma baki a ciki ba. Sabida haka meyasa zaka ɓata lokacin ka da tunanin ka wurin zagi da cin fuskan wani sahabi sabida kawai kana ga abinda yayi bai dace ba? Kuma zai yiwu shi abinda ka gina ƙiyayyarka akai bai tabbata ba? Allah yasa mudace.
Leave a Reply